https://www.wattpad.com/1112326619?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=b5uzlwrsmnjDJy16UxrP%2B6c%2F7MtDoc5iAfHC4HQyJIms0PfUCslcpjPlXla74C0IG9WLlc5Su6cieJVelxnZUaqj64NLFkeQVg24jiQwUO0LftfuKKKLW5VGghOyRdvm
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....BABI NA ARBA'IN DA TAKWAS.
"Toh ki shirya muje mana!" Kallonta Auta nayi a shagwaɓe,
"Auta ina jin tsoro ne, kar naje a sami matsala.""Ba gani ba" ta faɗa cikin tsokana,
"Kai Auta me zaki iya, keda ba karfi ne dake ba, balle ni"Harara ta tayi sannan tace min.
"Baki da mutunci kona miskala zarati, na yarda bani da karfi..dan haka maza ki shirya muje lokacin na tafi karfe biyar za ayi fa!"Buga kofar mu akayi, ita ta tafi a hankali ta bude kofar.
"Kina niman waye?"
"MG Mohan ya aiko ni nayiwa. Maimunari kwalliyar"
"Toh shigo mana" ta bude kofar ta shigo. Juyawa nayi na kalle ta.
"Laa! Aunty Uwani shigo mana"
"Ya haka karfe hudu saura amma baki shirya ba, gashi can ya addabi rayuwata da kira. Uwani ki tabbatar kin fitar min da ita, Uwani ki gyara min fuskarta."Murmushi nayi domin indai Mohan ne zai rina.
"Aunty bari na watsa ruwa."
"Ok! Amma tsaya ga wannan"
Ta mika min wata jaka.
"Ki duba zaki ga yadda ake anfani da shi.""Toh nagode"
Tunda na shiga ban daki na shafa wannan, na goga wannan. Kai har su gashin hammata duk dai da na fitar, sannan na yi wanka da wani sabulu na musamman, na fito, zan goge jikina sai ga auta da wasu mai.
"Malama zauna na shafe ki!"
"Wallahi baki isa ganin jikina ba."
"Toh ko nakira Hammah Mohan ne dan nasan shi zai iya gani har can birnin lintsin" ta fada tana min dariya.
Bayana na yarda ta shafa min, sauran na shafa da kaina, bayan na gama na saka doguwar riga naje na zauna. Aka fara kwalliyar. Tun karfe hudu aka fara bamu gama ba, sai biyar saura minti biyar, sannan na mike na saka doguwar gown din da ya bani ranar, sai yanzun nake yabawa da shi, dauko min wani set na bracelet diamond ja mai mugun kyau da tsada, dan kunnen shi da abin hannun shi, da wata zobe mai mugun kyau duk nashi. Sai yar siririn agogo duk nashi. Kallon shi nayi da kyau.Ina jin kwalla na cika a idanuna, jan hancina nayi sannan nace mata.
"Ban san iy adadin soyayyar da Mohan yake min ba, amma kyautar tayi min girma"
"Ke dai Allah ya tabbatar da alkhairi" inji Auta. Wani hula me kyau ta saka min bayan an shirya ni, sannan aka shiga daukar hoton, tare da tura mishi.Sannan ta gyara auta itama tayi kyau sosai, buga mana kofa aka yi. Auta ta bude,
"Barka da zuwa Khalil"
"Yawwa Auta, kun shirya?"
"Eh! Uwani ai ba dan Surukata karta ga nayi azarbabbi ba da na je na dauko Beenah amma babu kom.."
Daukar wayar yayi yana faɗin.
"Banza kawai idan kayi hakuri zan kawo ta, kafin a saka maka. Shege mayyen mata""Zan ci Ubanka!"
"Na yarda, ku tashi kafin Mohan ya tawo dan ba kunya ce ta ishe shi ba."Takalmin da aka ciro min na gani kamar zanyi kuka nace musu.
"WALLAHI tunda Uwata ta haife ni dau daya na saka irin wannan takalmin don Allah ku barshi, zan fad'i" jan kafana Aunty Uwani tayi sai da ta daka min ta daure min belt din, sannan ta mika min yar pose din, sannan ta shiga fesa min turare, sannan ta saka auta ta riko hannuna. Muka fito.Motar da ina da yakinin bai tab'a shigar ta ba, domin naga alamar sabuwa ce, bude min baya Khalil yayi sannan na shiga auta ta zauna kusa dani, muka fara ajiye Aunty Uwani a shagonta. Mika min wata jacket yayi tare da cewa.
"Mutumin ki yace ki saka."
Amsa nayi, tare da rikewa har muka shiga kofar farko na fadar shugaban kasa.
YOU ARE READING
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mystery / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....