https://www.wattpad.com/1114000208?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=9erIrydatIuPkJseZal69xUkMstLsWx8GyFdlSLeJfq8JZ7%2BWyAuXyBi3TFONZWvmJKNlkO3cngr4M2Sk%2BLQ9DhqVJ2mn36fvlalGIeTBV4qaMAzYIkNfoxokz2fxpjv
🐂🐂BOROROJI🫀🫀~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....BABI NA HAMSIN DA BAKWAI.
HMMM NIDAI YAR KALLO CE!
Zuɓewa yayi akan gwiwar shi, ya rasa meke mishi dad'i baki daya, wayar shi ya ciro. Ya shiga gurin kira, ya kira Abie.
"Abie ta tafi" ya faɗa kamar yaro karami. "Kuka zaka yi?" Ya tambaye shi yana murmushi,
"Karka damu, zata dawo Insha Allah ba zata tsallake boda ba, zata dawo.""Abie Mommy tace tana da juna biyu! Abie rayuwar su da abincin ki ta!"
"Karka damu zata dawo, baka yarda dani bane?"
"Na yarda da kai"
"Kwanta kayi barci zata dawo Insha Allah. Sai dai idan ta dawo ka rabu da ita kayi watsi da ita""Ba zan iya ba"
"Zaka iya, domin zata cutar da kai da abinda soyayyarta. Ka cigaba da hakuri Mahaifinka ma kayi ta bashi hakuri. Itama Mahaifiyarka ka bata hakuri.""Toh" ya faɗa, Abie ne ya kashe wayar ma.
*
Bayan sun gama wayar yayo alola tare da ɗaukar Alqur'ani, addu'o'in kawai ya shiga yi yana ambaton sunanta. Bai tashi ba zai da yaji a ranshi Allah zai amsa addu'o'in shi sannan ya mike tare da turawa Dr Zainab sako.
*_Ina kara baki hakuri don Allah ki taimaka mana da addu'a ke uwa ce Maimunari tana bukatar addu'o'in ki._*Sannan ya mike tare da fitowa falo yana labarta musu tafiyar Maimunari.
***
Tafiya muka yi bana kare ba, dab zamu fita bodin Nijar, mu shiga hanyar Libya, hukumar shige da ficce suka kamani, nayi juyin duniyar nan amma fir suka ki sake ni, karshe wayata suka amsa suka duba Number Hammah Mohan.Aka kira shi. Kamar a mafarki ya ji kiran dan haka bai b'ata lokaci ba, ya kira Dan Ba'are, aka yi magana da hukumar sojojin sama, aka bada jirgi. Har bakin bodar yazo daukata, sai da yayi kome sannan ya shiga inda aka ajiye ni, na kifa kaina da hannuna.
"Tashi muje" mik'ewa nayi a hankali, ya dauki jakar kayana ya fita dashi. A hankali naga yana tafiya. Da gudu na bishi tare da rungume shi ina kuka. Tsayawa yayi yana sauke ajiyar zuciya. Shi kanshi dan Ba'are goge kwallar da yake zuba mishi yayi.Muna shiga cikin jirgin yayi mishi magana da buzanci.
"Ka dauki matar ka ku bar kasr nan."
"Taya?"
"Zaka iya mana"
"Zan bar Abbu cikin kad'aici ne"
"Toh ai Ammyn tana kan bakanta sai ka auri yar masu kudi.""Toh nagode! Amma ka tattauna da Abbu duk yadda yace"
Haka suka yinta hira ina jikin shi a kwance, ina shaƙar kamshi turaren shi, har muka isa Niamey.A hankali ya dauke ni, muka wuce gidan Abie, Khalil na parking ya wuce dani dakin da ya tab'a kai ni, lokacin karfe biyu na rana, haka ya kwantar dani. A hankali ya janye rigar jikina yana kallon shafaffen cikina zuwa maran bai ga alamar kome ba, babu alamar cikin fa. Maida kanshi yayi kirjina da ya cika. Murmushi yayi yana shafa kirjin, su kam ya yarda dan sun dauke kome, har wani kumbura suka yi, addu'o'in yayi mata tare da shafe ta, sannan ya fito ya sami Abie.
Mika mishi fura da nono yayi, a hankali yake sha. Shigowar Khalil shima Abie ya mika mishi.
"Abie zama haka babu dad'i fa? Kayi aure mana"
"Hmm"
"Ko Mommyn mu zamu maka bikonta."
أنت تقرأ
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
غموض / إثارةlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....