BABI NA TALATIN DA TARA.

951 200 38
                                    

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
_Merci beaucoup, surtout mes compatriotes nigérs qui parlent français. Merci. Merci. Incha Allah. Nagode sosai ❤️😍💓😘👏_

BABI NA TALATIN DA TARA.

"Kinga ga inda zaki yi aiki, domin munyi magana da shi, dan haka ki nutsu kiyi abinda ya kawo ki,ban da shiga damuwar Kowa. Kinji" gyada mishi kai nayi, sannan ya juyar dani, ina kallon alkali, gaba na ne ya fadi.

Lokacin da nashi ya fadi ya kura min ido. Cike da mamaki.
"Moonah! Gashi nan kiyi aiki da gaskiya karki yarda a hada kai dake a cuci wani ko shi, sannan ki nutsu babu ruwanki da kowa, ki gabatar da kanki."

Kasa magana nayi ina kallon shi, haka shima yake kallona, gyada kai kawai nake ina kallon shi, kwarjinin shi da girman shi ya cika min idanuna, sunkuyar da kai nayi kasa, ina kallon kasa.
"Itace yarinyar ka?"
Cikin karamin murmushi ya gyada mishi kai,
"Sunan ta? Ya tambaya zuciyar shi na wani irin bugu.
"Maimoon I Umar" ya faɗa.
"Toh zaku iya zuwa babban Ofishin majastiri, kuyi cike ciken da ya dace sauran kudawo nan ita daya."

      "Toh" ya ja hannuna muka tafi, har na manta da Rukayyah Hussain Adam, haka muka gama kome, sannan muka koma ofishin sa, idan ban gaya muku ba. Hammah Mohan so yake ya lalace a jikina, domin baki daya wani ranar haka muka yi ta zirga-zirga, lokacin da na koma ofishin sa, na zauna yana masalaci. Ina cikin Office din ya dawo, ya shigo da sallama na amsa mishi. Ban san me yasa mutum yake min kwarjini da cika ido ba. Zama yayi tare da mai da hankali akan aikin shi. Mikewa nayi tare da cewa.
"Yallabai"
"Koma ki zauna" zama nayi cikin jin kunya.
"Baki da mafadi ne? Ko abinda iyayenki suka turoki kenan? Shi kwalliya ce a tare dashi, ke kuma abin kunya ce a gare ki, ban ji dadin yadda yake rungume a kan idanuna ba, idan mahaifin ki ya ga haka me kike dauka zai kalle  ki? Karki kuma kamanta irin wannan shirmen a ofishina, ki cika wannan takardun." Ya ajiye min, jikina yana rawa na dauka, tare da cikawa na mike zan fita.
"Dawo?" Da sauri na dawo na zauna.
"Kin ci abinci?" Ya tambaye ni cikin kulawa.
"A'a. Abie" wayar da can ya danna, yayi magana cikin fulatanci. Murmushi nayi tare da cewa.
"Abie anani fulfulde?"
Murmushi yayi sannan yace min.
"Eh, Wodaadabe Bororo" ya faɗa tare da kallona, kamar na saka ihu."

"Laa nima Wodaadabe Bororo ce."
"Daga ina?"
"Niger"
"Libya Mali"
"Kai Amma Abie kai ma aiki ne ya kawo ka nan?"
Kwankwasa kofar akayi, yace a shigo, katon basket aka shigo dashi, aka ajiye Mishi, tare da mishi gaisuwa, kafin ya ciro kuɗi. Ya bata, tana fita yace min.
"Akwai goran fura da nono, ki duba can akwai kofi, sai ki zuba min sai ki kawo min, abincin kuma naki ne"

   Idanuna ne ya cika da kwalla, na nutsu na fara abinda ya sani, kome na Office din tas yake, na dauraye na kawo, na zauna nayi duk abinda ya sani. Bayan na gama na mika mishi.
"Abie me yasa ba zaka ci abincin ba?" Murmushi yayi sannan yace min.
"Abincin mata uku naci a duniya na gamsu dashi, Mahaifiyata, mai sunanki dan ke sunan babata ce, sai Kanwata Kabo itama ma ina son girkinta, sai mace daya da tayi tafiyar ƙaddara da rayuwata."

Hannuna na had'a tare da kallon shi ina bubuga index fingers dina.
"Abie itace Crushed dinka?" Na fada ina kallon shi da yar murmushi.
"Ta wuce crushed sai dai rayuwata."
"Ta rasu ne?"
"Zuwa yanzun kan bana jin tana raye?"
"Ayya kayi hakuri, na fama maka ciwon da yake ranka" na dauki abincin zan fita.
"Ina zaki? Ki ci anan"
"Abie, Hammah yana waje"
"Toh jeki"

   "Nagode sosai Abie"
Bai d'ago ba, kuma bai amsa min ba. A duk lokacin da ya kalle ta wani irin abu yake ji akanta, haka kawai muryanta da shiririta yake dibi da ita, idanun shi ce ta cika da kwalla, ya mike tare da tsayawa a bakin window yana kallon yadda mutane ke zirga-zirga.
*Jewel* ya ambata a hankali, yana tuno yadda tayi ta kuka da abinda yayi mata, idan ya tuno yadda take daura kanta, a kafadar shi tana kuka.
_Wai meye aka miki ne? Kawai dan na tawo dake? Meye na kuka? Toh kiyi shiru zan mai daki gida_
A lokacin dud duniya baya jin zai iya rabuwa da ita, baya jin akwai wanda ya isa raba shi da ita. Sai gashi kai tsaye mahaifinta ya karya karfin shi da yake jikin ta.

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Where stories live. Discover now