https://www.wattpad.com/1106761947?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=96bc8j7ajP40xeHpU1lx3Iq9KNgJDweWbOsQ2t4marCDkKriXYt89TwgT%2BmS3tOH%2FA0PvkmbeXh9jXQ8GnCAYeKrGW2Uqpce1Fx0xCDcXJXOV%2BHIdFegRFE9fS%2FUP7i8
🐂🐂BOROROJI🫀🫀~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....*Wannan shafin gaisuwar kune Mutanen Jikar kulu 💞💓😍 da Masoyan BOROROJI Novel tare da Masoyan MOHMOON da MOONSAR*
TeamOneLove❤️😘BABI NA ASHIRIN DA TARA.
A wani firgice na kalli Innah, jikina yana rawa, ta daka min tsawa.
"Ina kuka je?"
Dakyar na sami bakin magana na gaya musu abinda ya faru. Cike da mamaki take kallona yau dan da ta rena shine har da bin wani namiji wata ƙasa. Zama tayi tana nazarin ta ina ta gaza a tarbiyyar da tayiwa Mamoon. Cikin kuka ta nuna kanta.
"Ta ina ma Gaza? Meye nayi maka da zaka zabi bin namiji? Mamoon wata biyu bana barci cikin sa'ida kullum mafarkin mahai...." Rufe mata baki baba yayi tare da mika mata ruwa."Kisha" karba tayi tare da sake wata irin kuka.
"Gaya min meye yayi maka? Ko kuma na saka wuka nayi maka yankan rago""WALLAHI bai min kome ba na rantse da Allah, ki duba jikina." Na fada mata, wani irin kuka take sannan ta riko hannuna da yake b'ari, ta rungume ni.
"Daga yau ba zaka kuma komawa bokon ba, ina tsoron sanadin boko karka bijiro min da tashin hankalin da zai hanani sukuni""A'a ki bar shi yayi karatun."
"A'a malam, tsoro nake ji ina son shi kamar yadda nake son dan uwana." Ta fada tare da kallon shi bayan ta rungume kan Mamoon a kirjinta.Cikin hikima take bugun cikin Almamoon, wanda tsoro ya sashi ya fadi gaskiya ba tare da yasan dabaranta ba.
"Kuka kwana daki ɗaya? Ban san iya abinda yayi maka ba Almamoon anya kayi mana adalci.""Innah kiyi hakuri" na fada a tsora ce, sai da ta gama jin abinda muka aikata, sannan ta kama kunne na ta buga min katon kashedi tare da cewa.
"Ka gama zama a wani gurin, sannan kudin da ya baka da kayan shi zaka mai da mishi kwadayayyen banza irin haka ake cutar da ku saboda mugun kwaɗayin ku, baku zama inda Allah ya ajiye ku, burin ku kawai kuyi ta bin masu kudi suna baku abin hannun su, ana amfani da ku. Waye ya sani ko ya gama abinda ya gadama da kai malam bani guri na duba shi"Duk yadda Baba yaso ta hakura Innah fir taki, sai da ya fita ta jika wani saiwa, ta mika min masha, sannan ta sani na cire kayana, ta kwantar dani ta duba lafiyar jikina, sosai wani irin ajiyar zuciya take saukewa bayan ya sani na juya baya ta duba mazaunaina, sujada tayi tare da mika min kayana bayan ta mike.
"Kana barin ana tab'a maka kirjin ka ne?" A tsora ce na lalle kirjin.
"A'a kawai na sayi wanc.." na bude jakar na ciro mata bra ɗina, kifa min mari tayi. Tare da cewa.
"Ina yadin da na baka?"jikina yana rawa na dauko tare da mika mata, ganin ma na daina amfani dashi yasa ranta yayi mugun b'aci."Waye na shi da ys canza maka duniyar ka? Nasan ba Ansar bane, waye shi da idanun ka suke nuna min kana bukatar shi anan?" Ta fada cikin kuka, anan ne kuma na kasa mata magana, duk yadda taso na gaya mata waye ne shi naki.
Ta dake ni a ranar kamar bata kaunata, tayi juyin duniyar nan na gaya mata waye haka, naki naki karshe ma kin magana nayi sai kuka domin idan na bude baki nace mata Mohammed Mamman Mohammed Nasir Aghali ne toh ba makawa ba zata kuma barina saka shi a idanuna ba.
YOU ARE READING
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mystery / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....