I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx
'''Zaku iya samun kayan mu daga turaren zamani na wuta, shu'umar humra, dambun nama na mata, tsumin. Da sauran su kayan mu ba irin nasu bane sai an gwada akan san na kwarai..... Akwai haɗin kayan amare da na uwargida....'''
🐂🐂
*BOROROJI*
🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Littafi na D'aya...Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah IdrisMafarin labari...
BABI NA ƊAYA
Niger Republic.Tayi makotaka da wasu ƙasashen har guda bakwai.
Chad
Burkina faso
Benin republic
Libya
Algeria
Mali
Nigeria.Kuma dukkan su ƙasashen a zagaye suke da kabilar Wodaadabe Bororo da wasu dangin Fulanin...
2000/ May/08
Nishi take a hankali, tare da cizon bakinta. Iska ta kuma ja alamar tana cikin tsananin zafin nakuda, juya kai tayi cikin tsannanin takaici da bakin ciki, ga wani abu da ya tsaya mata a makogaronta. Yau kimanin wata goma sha biyar kenan da take jin abin a ranta, har yanzun bata ji saukar shi ba.
"Sannun Abuh ga ruwan addu'o'in sha Insha Allah zaki sauka akan gwiwar lafiya." D'ago kai tayi ta kalle shi cikin tsannanin k'iyayya da bakin ciki, sannan ta sunkuyar da kanta, tare da had'a kai da jikin itaccen da akayi gadon kara dashi. Ta kuma sauke wata ƙatuwar nishi a hankali jariri ya fado daga kasanta, cikin wani irin kakkarin kuka bayan ya zabga atishawa, Allah da idon shi ya diro da uwa baki daya.
Murmushi tayi lokacin da ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, tare da wuccewar abinda ya tokare mata kirjinta. A hankali ta mike tare da ɗaukar wani mayafi da zani ta daura sannan ta dauki babban zanin da yake sayo mata, tayi kunzugu dashi. Kafin ta isa gaban shi tace mishi.
"Kowacce rayuwa akwai samu akwai rashi, akwai nasara akwai faduwa. Kamar yadda ka zalince ni Ya Allah Ya ninka maka abinda kayi min. Kamar yadda ka saka ni kuka Ya Allah Ya sakaka kuka.Kamar yadda ka hanani farin ciki Ya Allah Ya hanaka, zan so Ubangiji ya jefa ka, kasar jahannama. Ya turaka ƙarƙashin fir'anuna da hamana, Ubangiji ya haɗaka da masifa da bala'i, Ya Allah Ya sanyaka bakin ciki sama da yadda ka saka ni."
Takowa tayi gaban Jaririn ta juyar da shi, tana me kallon Mutumin da yake tsaye, ta sake murmushi me had'e da kuka, tace mishi.
"Ba zan yi fatan kayi irin na wancan mujirimin ba, zan so kayi rayuwa cikin salama, wannan mutumin da ya samar da kai mugu ne, mugu mara alkibla, fasiki mara imani, kazami me dauke da datti da kazamta na bala'i da masifa da jahilci ya goga maka bakin fanti na har karshen rayuwar ka. Iya haka ma ya ishe ka, ka tsani wanda ya bada gudummawar jazaman ƙaddararka"Sannan ta tako gaban shi cikin bakin ciki mara iyaka, tace mishi. "Sama'ila kenan, gamu ga ka ga duniya ga Allah ya tsayawa me gaskiya." Ta juya ta nufi kofar dakin zata fita. Riko hannunta yayi tare da zuba gwiwar shi a kasa, cikin tashin hankali yace mata.
"Don Allah ki rufa min asiri, ki dauki Yaronki, bai da gatar da yafi naki, Zainabu zan gyara kuskuren da nayi a shirye nake na isa gaban danginki don Allah ki rufa min asiri karki juya mana baya a daidai lokacin da muke bukatar ki"Cak ta tsaya tare da sake wata irin kuka da sai yanzun ta samu damar yi, tare da shasheka.
"Aminci Allah Rahaman Allah, jin kan Allah Ubangiji ya hanaka su tun daga duniya har lahira" sannan ta saka ta bar dakin da rugar baki daya, tana tafiya tana kuka dukda sulisin dare ne, bai hanata tafiya ba, sai da tayi dogon tafiya kafin ta isa wata iyar karamar gari, tun daga nesa take hango kamar fili ne sahara babu kome sai rairayi. Kurawa gurin ido tayi alamar kamar ba nan take nima ba, dan haka ta cigaba da tafiya har alfijir ya keto sanyin Asuba ya kuma gabatowa zama tayi a kasar wata bishiya tare da kusa hannunta kasar cikin ta da yake murɗa mata jini na zuba a hankali. Barcin gajiya ce ya dauke ta.
YOU ARE READING
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mystery / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....