BABI NA SHA TAKWAS

956 178 13
                                    

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

_*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
Domin samun labarin masu kayatarwa na Hausa danna Link din nan a sha sauraro lafiya....

BABI NA SHA TAKWAS.

A sanyayye na shiga cikin dakin yana tsaye kamar ba zai shigo ba, fita nayi na shigo dashi dakin ina cewa.
"Zauna a kan na shiga ban daki na fito."
Na zaunar dashi na shiga ban dakin na gama uzurina na fito, sannan na dauko mishi maganin shi, na nutsu na tofa mishi addu'a kafin na mika mishi, wani irin duba yakewa maganin cike da kyankyame.
"Ka sha maganinka ne" na fada ina tura mishi maganin a bakin shi, dakyar ya sha yana yunkurin amai, sororo nayi ina mamakin shi. Dafa goshinsa nayi naga ya rintsa idanun shi da karfi, alamar baya son na tab'a shi. Janye hannun nayi ina kallon shi, koda na dauko wanda nake shafa mishi ma, kamar ala dole nake mishi.

   Ina gama shafa mishi nace mishi.
"Kayi hakuri kaji magani ne da alamun kafara samun lafiya shi yasa baka son ina tab'a ka, amma Insha Allah idan ka samu lafiya zan tafi na koma inda na fito, sabida kai nake nan" na fada ina shafa mishi ayatul shifa a kafar shi, kwalla na zuba akan gwiwar shi, ina gamawa na mike na mai da maganin sannan na fita niman abinda zamu ci.
Ina gamawa dan Ba'are yana shigowa gidan shi da Malik. Abincin na gabatar musu, kallon Hammah Mohan suka yi da yake tsaye astep ya kura musu ido,  yaki saukowa. Mik'ewa nayi cikin rawan jiki zan tafi gurin shi Dan Ba'are ya dawo dani.
"Rabu da dan iska kar yazo taci ya zauna da yunwa dan Ubanshi"
Juya nayi gurin Hammah Mohan Gandhi tsaye, kan shi a sunkuye.
Kwace hannun nayi tare da nufar shi, yana tsaye bai matsa ba, gaban shi na nufa na tsaya tare da kamo hannun shi muka tawo gurin cin abincin. Na ja mishi kujera ya zauna, sannan na zuba mishi abincin. Kallon abincin yake yana kallon nasu, kamar ba zai ci ba.
"Banza dan iska karka ci dan kaniyar ka" haka yayi ta juya abincin sai da na hakura da cin nawa na fara bashi, yana yatsina fuska.
"Ayya abincin babu dadi ko?" D'ago kai yayi yana kallona, kafin ya ture hannuna ya shiga amsa dan ya lura da yadda kwalla yake cika min idanuna, sosai yake cin abincin yana gamawa ya mika min na kara mishi, shafa kan shi nayi tare da cewa.
"A'a ba zaka ci dayawa ba, kaji sha ruwa haka ya isheka kana magani ba a son kana cin da ya fita Muslunci."

  "Ai da kin bashi, tunda shi ya zama tumbi iza hana gaya rub'a."
"Auchewww" inji Dan Ba'are, yana kallon Hammah Mohan, cikin takaici da zafi.
"Lafiya?" Na tambayr shi a rud'e.
"Ban da wannan dan iskan zai karya min yatsu shege ciwo bai saka ka daina mugunta ba, Mahaukacin banza kawai" ya faɗa lokacin da ya tashi a kujeran yana dingishi.
Rike kunnen shi nayi tare da zaro mishi ido, kawai sai ji nayi ya dauke ni cak ya daura akan cinyar shi da hannu daya. Ya saka ya matse ni.
"Sake ni! Kyale Ni bana son haka" na kwace kai na ina ajiyar zuciya. Make keyar shi nayi tare da kwashe kayan da aka ci abincin. Na nufi kitchen da shi.

    Haka dai yanayin shi yayi ta sauyawa har Hammah Khalil ya bar garin, ina kuma kula dashi. Wannan karon karatu yayi zafi bana iya dawowa da wuri sai Malik ya je ya dauko ni, ga Malam Ansar ya taso ni gaba. Kamar zanyi kuka haka yake disgani a gaban jama'a. Bai tab'a sani naji a raina zan mishi yadda yake so ba.

Yau ma da wuri na shigo makarantar, na nufi ajin mu. Ina shiga na same shi yana karatu, dan haka na shiga tare da sallama.
"Zoka fita min a aji"
"Malam kayi hakuri na san sai bakwai da rabi kace zaka..."
Ban idar da abinda yake bakina ba ya kifa min mari, tare da daka min tsawa.
"Fitar min a cikin ajiye, dan iskan Yaro kawai" ya turo ni waje tare da rufe min kofa, gashi ana wucewa tare da kallon mu,haka na juya na bar makarantar sabida ko ina na zaga dariya ake min, danne kuka na nake har ba samu abin hawa, na nufi Jacader. Ina isa na samu sun bude min gidan, ina shiga na taradda sabon tashin hankali. Domin Matar ranar ce ta zo, ina shiga na same shi kamar Almajiri a gabanta yana zaune.
"Sannun da zuwa Hajiya" na fada ina danne kuka na,
"Takowa tayi tare da kifa min mari." Sai da na zube kasa.
"Akan me zaka na barin shi a gida bayan kasan bai da lafiya? Toh wannan ya zama na karshe kar a kuma, ga kuma maganin nan ka tabbatar ka yi amfani dashi maza dauka ka kai daki" jikina yana rawa na kwashe kayan na nufi sama dashi,
"Kai kuma a haka zaka kare, saura kiris burin mu ya cika ba sai kana raye zaka iya taimakawa iyayen ka ba, idan ka isa ka hana mu kashe Ubanka da ita mahaukaciyar Uwarka" ba iya Ni na kad'u ba hatta shi dai da naga ya girgiza, balle ni domin a haukace yake kallon shi, ai kuwa ta shiga marin kyakyawan fuskar shi, da sauri na iso gurin tare da had'a fuskar shi da kirjina, ina bata hakuri.
Nima duka na ta shiga yi tana gaya min.
"Idan baka min aikina ba, tabbas sai na kashe ka kai ma bayan na samu ka kashe shi matsiyata."

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Where stories live. Discover now