https://www.wattpad.com/1107324574?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=4ugJdhgGa4BvbsExr19Jvhrf8LWxJfS%2FSxI1B7ZzbxI65y3FAC%2F%2Bp5dONKBm%2FARRS1nZwKrYHg3%2FBE6YQ7n4aR6rGLUDTKvkAvezukOoIJGO6fac4VkMX5uB5%2FHWvZsK
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....Wannan shafin gaisuwar kune Mutanen Wattpad Nagode sosai..❤️💓💞
BABI NA TALATIN.
Har malam Umaru yazo ya wuce Mohan yana jikin motar shi kayan yana gaban shi, bai saka yayi fush ba, haka yana tsaye har dare yayi sosai yana tsaye a gurin.
.....
Bayan Baba Ya dawo, bata gaya mishi ba, kuma bata nuna mishi wani abu ya faru ba, domin ta gargadi ni da babban murya, ina kallon su suka kwanta,wato suka shiga dakin su, nasan yana kofar gidan bai tafi ba, dan haka na tashi a hankali na fito tare da dauko wani abu na saka a jikin katangar gidan mu, na haura katangar na diro. Sannan na kwasa da gudu, sai gurin shi.
Ina zuwa na fada a jikin shi ina kuka.Bude min hannun shi yayi tare da shiga cikin jikin shi.
"Hammah kayi hakuri, ka tafi"
D'ago kaina yayi tare da kallon yadda nake kuka. Sake maida kaina yayi, yana shafa bayana."Ina nan har sai Innah ta barni nayi magana da ita." Ya fada tare da dauke kan shi. Kallon shi nayi da gaske yake fa.
Dan haka na gyara tsayuwa na a jikin shi.
"Hammah"
"Hmm! Mamoon"
"Hammah"
"Na'am My Golden Boy" ya faɗa tare da shafa kaina.
Bayan ya riko hannuna, ya nufi kofar gidan mu dani."Don Allah karka buga musu kofar zata zane ni ne, don Allah karka bari tasan na fito ta katanga, please Hammah Mohan" bai saurare ni ba, ya
buga kofar yayi dakyar aka bude. Baba ne ya bude. A hankali ya ciro ni daga bayan shi.
"Maza shiga ka kwanta, ina nan har gobe."Ya fada yana tura ni cikin gidan, tsoron Allah da tsoron Innah yasa Ni jin fitsarin tsoro, haka Baba ya kalle shi tare da cewa.
"Nagode!"
"Baba kar a dake shi don Allah.""Idan aka dake shi zaka karya mu ne kamar yadda kayiwa Wancan Yaron?" Bai ce kome ba, ya tsaya a gurin har suka rufe kofar gidan, zama yayi a kofar gidan bayan ya ciro ƙaramar bindigar shi, ya gyara kunamarta.
Ganin yadda ina take niman abin dukana yasa Baba ya sha gabanta.
"Ya isa haka! Meye laifin shi, Kinga dukar nan da takurawa, wallahi shi zai lalata miki shi, tunda na dawo kika ki gaya min abinda ya faru nace miki wani abu ya faru ne? Kika ce min a'a, amma a can inda nake zaune aka gaya min Shago ya hadu da wanda ya fi karfinshi inda yabi Almamoon, na nuna miki na sani? Toh bari na gaya miki matukar Shago yana unguwar nan wallahil azim abinda kike boyewa zai fitar miki dashi domin ba dan Allah ya kawo shi ba sunan tattalin ki na shekaru sha takwas zai tashi a banza tsanani baya gyara sai lalatawa ba yau na fara gaya miki ba.Sabida ina son auna girman abinda yake faruwa ne, dan haka karki sake Almamoon ya fahimci dalilin ki na hana shi abinda yake so domin kuwa goben sa zai lalata da hannun shi. Ya ga yadda zakiyi, kai kuma wuce ka bani guri."
-- Haka muka kwana zuciyar kowa babu dad'i, Allah Sarki. Hammah Mohan anan kofar gidan ya kwana. Da asuba suka nufi masalaci da Baba, sannan suka yi hira bayan ya fadi abinda ya kawo shi da abinda ya faru a baya, malam yayi godiya sannan yace mishi.
"Mun gode, sai dai kawai abar aikin nan idan hankali ya kwanta za a yi miahi kaga mahaifiyar shi hankalinta yake s tashi, sannan ina son Yaron ya koma makaranta sabida kwazon shi don Allah kayi hakuri zan kula da kome, ina son Rayuwar Almamoon ya bunkasa sosai."
YOU ARE READING
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mystery / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....