🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
_Don Allah ina niman wata baiwar Allah daga lafia takirani sati daya zuwa biyu da suka wuce idan ta ga sakona don Allah ta min magana 👏🏼_BABI NA HAMSIN DA TARA
ALLAH KA RUFA MANA ASIRI RANAR JIN KUNYA! YA ALLAH KARKA KUNYATA MU RANAR DA BA ZAMU IYA KARE KAN MU BA! DUK WANDA YA NUFE MU DA SHARRI UBANGIJI MUNYI TAWWAKALI DA KYAWAWAN SUNAYEN KA KA KARE MU BA DAN MUN ISA KO MUN KAI BA! YA ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU DA NA YAN'UWA MUSULMAI BAKI ƊAYA 👏🏼👏🏼👏🏼
ASSALAMUN ALAIKUM....RANAR DA BA ZAN MANTA BA...
Na gani a jikin littafin farko da na dauka.
_Ba zan manta ba, kasancewar Tabbas ban san kuskuren da nayi a baya zai saka ni kuka a gaba ba, duk da ba laifina bane! Sai dai babu macen da za a keta alfarmarta bata yi abinda nayi ba! Duk inda aka kai aka kawo karshe dai nice mai daukar laifin.... Ya Allah karka kamani da laifin da zuciya ta kai ni! Ina kewar abinda na haifa_Tsayawa nayi ina kallon kwanar wata da ranar da tayi rubutun, kafin ta cigaba da cewa.
_Iyayen mu Fulani suna da kunya da YAKANAH amma basu tsayawa ya'yan su, musamman idan ƙaddara ta faɗa musu! Da ace bai tafi dani ba da babu abinda zai faru! Yayi nasarar juya min duniya ta! Ban san cewa fad'a mishi ba sai da Khalid ya fahimtar dani! Duk da ya cutar dani a lokacin amma dan shi da shi kan shi sune maudu'i na_
Idan na fahimta tana son Abie ne? Idan na gane dama can ta fada kaunar shi!Mutumin da ya cutar da kai, ban da mahaifina ne sai ka kai shi bango. A hankali na bude shafin gaba.
_Sai dai kuma zuciya tana son mai kyautatta mata. Khalid yayi nasarar samun matsuguni a raina, na kuma manta da duniyar shi wancan burkina Abinda na haifa na kuma saka shi a ido ko sau daya ne! Burina na daina kuka idan na kwanta, na daina mafarkai akan abinda na bari, ina zanga Iyayena?_Tayi tambayar kamar tana bawa wani labarinta,a hankali nake bude shafi bayan shafi idan na gama wannan na bude wani, nayi kuka nayi bakin ciki, na tausaya mata. Ina son Mahaifiyata. Duk inda zata yi rubuce-rubuce zata ajiye har da kwanan wata da shekaru, littafin na karshen da na duba shine ya tsaya min a raina.
_A ranar da aka kawo ta asibitin akan matsalar fyade ban san ya aka yi zuciyata ya karkata akan ta ba, sai dai kawai na tsinci kaina da son binciken lafiyar ta, a nan na Fahimci tana da angurya, garin a shigeta ne ya fashe har bakin farjinta ya ji ciwo! Abin ya tsaya min a rai shi yasa na roki abokan aikinsa mika mata aiki! Sai dai kuma yarinyar ta kuma tafiya abinta! Ina son ta_
Tsayawa nayi tare da fashewa da kuka, ina rungume littafin. Sai da Yumnah ta shigo. Ta zauna a kusa dani.
"Adda Munah! Mommy tana sonki sosai, ki daina kin kulata tace zata zo!" Kallon yarinyar nayi domin ban san me zance mata ba,.banbancin mu da yarinyar ita fara ce kuma tana kama da baban ta, hatta gashin goshinta irin nawa ne, sajenta da (Kai Bororoji fansa musamman matar Sadeeq ko Matar Yau wai na gaya mata spirit din da alamun yake shafawa gashin baki yake tsirowa 🤣🤭 very funny 😂🤣 Wayyo Allah na, wato mutanen nan ba zaku kashe ni da dariya ba🤣😂)"Didi Yumnah jeki wasa zan kiraki anjima" da sauri ta fita na dauki littafin na karshen da nake dubawa.
_Ranar da na ga daurin auren yarinyar a tv sai da nayi sallah nafilla ta tsaya min a rai, tausayin ta da Sonta sun cika min zuciya. Ban sani ba ko dan tana yanayi da nice oho! Sai dai kuma washi gari bikinta da kwana biyu aka kawo ya cikin rai kwai-kwai mutu kwai-kwai ya sani jin tashin hankali! Da naga Mutumin nan da ita sai naji kome ya dawo min sabo! Ban tsinke ba sai da ya gaya min ita din Rayuwata ce!_
YOU ARE READING
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mystery / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....