BABI NA TALATIN DA D'AYA

1K 214 39
                                    

https://www.wattpad.com/1107772645?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=It8W%2FoFtRBNmtv626Ht7hoebrG%2FLVlSJZLNfj7SZVFb70I%2BU8R57oeYt0nQfprrru5On2xw2q9Wa9DKvsVlrhYzw3HNW938T6zol7nYvstpRTnu2EztkBZZewXp3wWvE

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA TALATIN DA D'AYA.

Dafe goshin sa yayi tare da lumshe manyan idanun shi, ya bude tar akan likitan.
"Karka bari iyayena su sani"

Ya fada yana me gyara kwanciyar shi a jikina matashin, yana jin kamar ta cire zuciyar shi ya huta. Ya gaji da damuwar Almamoon, allura likita yayi mishi wanda zai sanya shi barci. kuma anyi nasarar haka, domin yayi barci cike da mafarkin Mamoon tana sanye da wasu shegun kaya. Ga kai yake tare da mika mata hannu.

    Amma sai wani ja mishi rai take tana wani yauki.

   **
Kallon juna suka yi tare da Amincewa da bukatar su, kafin suka ce.
"Idan muka bar shi zai cigaba da kare Ubanshi, idan muka tab'a shi zai iya daukar kasadar tab'a mu, amma idan muka saka Ubanshi ya kashe shi wannan alfarma ne kuma samu.

   Ranar da kasar mu ta samu yancin kai ranar zamu basu kyauta da ya dace dasu, daga dan har Uban zamu bashi kyautar da zasu iya daukar shi."

    Sannan ya cigaba da tsara musu kome, cikin nutsuwa da sanin ya kamata, kafin ya mike kamar mutumin kirki, ya bar dakin da suke taron sirrin.

   **
Yau kwana biyu.
"Wallahi Yaron nan mace ce ba namiji ba" inji Mohan.
"Kamar Ya?" Ya tambaye shi a rud'e.
"Mace ce kamar yadda ka sani, taya hankalina ba zai tashi ba yaron ya gama cutar dani." Kasa magana yayi yana kallon Mohan,

"Ban san yadda zan yi ba, amma ina cikin tashin hankali" ya faɗa a sanyayye,
"Tashin hankalin Uban me? Malam kana son Yarinyar nan tun tana namiji, dan haka yanzun ya dace ka fidda abinda yake ranka, idan kuma ka b'oye toh wallahi damar da wasu suke nima kenan, ka tafi ka tambaye ta meye yasa ta boye kanta na tsawon lokaci haka? Yaron bai iya karya ba, sai dai idan bai dagamar fada ba, sannan ban ga abinda zaka daurawa kanka yawan jini ba, kana son ta sosai duk wanda yake tare da kai yasan kana son Yarinyar."

   "A'a ba soyayya bane, kawai shakuwa ce. Na shaku da yaron kuma ina matukar tausayin shi. Ashe mara mutunci bai damu da yadda na damu dashi ba."

   "Komo meye malam me taurin kai mun san kome, tunda har ka iya hana mu mishi magana yana namiji shine yanzun zaka kawo min gulma me ciwon soyayya kawai."  Gyara kwanciyar shi yayi tare da Lumshe idanun shi, yana kara tabbatar da kanshi yanawa Almamoon wani irin mugun SO ne kuma shi kanshi bai san da me yake son Yaron ba, idan yace da zuciyar shi ce toh ba mamaki karya ne amma idan yace da ranshi ne wannan gaskiya ne. Dan haka ya cigaba da sauraron shawarar da Dan Ba'are yake bashi.

        Murmushi yayi sannan ya mike da karfin shi, ban daki ya shiga yayi wanka sannan ya fito k'ugun shi daure da towel, hannun shi rike da wata karamar towel yana goge kanshi, murmushi ya sake irin gashi ga Mamoon suna cikin farin ciki.

    Shiryawa yayi cikin jamfa da wando kaftani, sai wata hular dara wacce ya murza akan shi, yau yake jin shi kamar zai tafi zance. Dan haka ya shirya kai yadda yake shiryawa kamar ba shi ba, domin kuwa shi kan shi yasan yayi kyau. Privet jet zai bi domin idan ba shi ba zai isa Damagaram a kan lokaci ba. Kiran Dan Ba'are yayi ya gaya mishi. shi kuma ya kira sojojin da suke Damagaram akan ga Mohan nan zuwa.

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Where stories live. Discover now