https://www.wattpad.com/1104788648?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=q5d7yQUTBcJ8BdXrs84PaortqtGlVo0sxj15rZPXOdrLAxFvWQgJa%2BsauKrirmCAI6CTRR9OwqxP0GgCqsNrnu%2B64lqmFiENdCsHVuJcnC%2Bq1rbT7zaXMbV7vn44ciXw
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza...._Ban san Meye Ansar ya tsare muku ba kowa sai haushinsa yake ji...😌😠_
Fatan Alkhairi ga Baroriji fans 😂 kuna abinda ya dace!💞💓😍😘Much love....
BABI NA ASHIRIN DA UKKU.
"Mohammed Mamman Nasir Aghali akwai abinda kake boye min" ya faɗa tare da kallon Almamoon da yake barci, dauke kai yayi yana kallon yadda Mohan yake kokarin barin gurin da Dan Ba'are yake. Rike hannun rigar shi yayi cikin damuwa yace mishi.
"Ko akan matsalar shi ne na jinsin mata maz..." Fauce hannun rigar shi yayi tare da nuna Shi da yatsar shi. Kamar wanda aka gaya mishi wani magana mara dadi.
"Karka kuma, kayi abinda na saka bana son kowa ya rab'e shi ne, ni nace ka nisance shi idan kuma ba zaka iya min wannan Alfarmar ba thanks you can go away."Mamaki ne ya kuma rufe Dan Ba'are, sama da baya. Kafin ya kalli Almamoon.
"Shi kenan, but i'm in your side babu wanda ya isa shiga tsakanin mu ina tare da kai."Bude mishi hannun Mohan yayi suka rungumi juna, duk da kowa yasan Dan Ba'are dan uwan Mohan ne ta gurin Uwa kuma sun tashi tare, kome nasu daya ne. Amma haka bai hana Mohan kafkafta mishi rashin daraja ba. Kuma bai tab'a fushi yace ya rabu da Mohan ba, domin kaunar su daga Allah ce.
"Toh sake ni zan tafi maganar tafiyar ku, duk da mun gama rabin aikin kawai saura naje na karasa sauran ne" inji dan Ba'are,
"Ok Yaron kirki kayi abu me kyau maza kaje" inji Mohan ya faɗa cikin zolaya,
Wani banzan kallo yayi mishi tare da barin d'akin, shi kuma ya koma jikin window yana kallon yadda ake training ta baya, kasancewar asibitin a cikin Barrack yake. Tsayawa yayi sosai yana kallon kome.Shigowar Dan Ba'are yasa shi juyawa yana kallon shi. Mika mishi wasu takardu yayi sannan ya kuma fita. Bayan kamar minti talatin sai gashi dauke har da jakar Mohan da kayan shi ya mika mishi. Sannan yace mishi.
"Toh na gama maka kome, Allah ya bashi lafiya"Bai rufe baki ba sai ga Nurse sun shigo da gadon marasa lafiya, daukar shi suke son yi, Mohan ya dakatar dasu ta hanyar daukar shi cak ya fitar da shi daga cikin ɗakin, lokacin da ya fitar dashi kallon su Dan Ba'are yayi tare da jin idanun shi na cika da kwalla.
*Karka manta Mohan yayi maka kome a rayuwa Mohan ya baka kome da kake nima! Dan haka ka bar shi da Yaron ko zai sake kamar kowa kafi kowa addu'o'in Allah ya sauya mishi murɗaɗɗiyar hali dan haka zaman shi da Yaron sai ka ga an dace*
Inji wani shashi na zuciyar shi yake bashi shawara. Ajiyar zuciya ya sauke tare da taka musu baya. Har gurin motar shi tun kafin Mohan ya isa sojoji sun bude motar tare da sara mishi kwantar da Almamoon yayi sannan ya shiga cikin motar dan Ba'are ya shiga gaban motar suka bar asibitin.Cikin abinda bai wuce awa daya na suna isa airport din, shi ya fidda Mamoon yana daukar shi tare da daura kanshi daidai kirjin shi. Mamoon ya sauke ajiyar zuciya. Cak ya tsaya tare da kallon fuskar shi jikin shi yana wani irin yanayi. Kallon fuskarshi yayi na few seconds kafin ya nufi cikin airport din dashi.
"Kamar yayi motsi ko?" Dan Ba'are ya tambayi Mohan, karamin murmushi yayi tare da gyada mishi kai,
"Alhamdulillahi don Allah idan kuka isa ka saka ido akan shi kaji"
YOU ARE READING
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mystery / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....