https://www.wattpad.com/1109328405?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=f4DtUHMnMYkq7YQxK69EHXzYx4qdYjE9KB3IVp12Bnb%2BzEoaanjkzsPH8vAt9jgM2j%2Blswb6qNSSL7B8%2FPrpejrjetMFg5iT6eRxuTuhL2RSdvHxFf9zphNfPityAhJD
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza...._Allah Nagode maka!🙆🏾♂️ Tunda Jannart ta da Malik suka mutu na shiga hannun mutane 😭 nace muku zan kashe wani ne?😩_
BABI NA TALATIN DA BAKWAI.
Idan na fahimci Innalillahi tana nufin, keb'ewa da nake da Hammah Mohan ba haka kawai bane ina barshi yana wani abu dani? Hmm tashi nayi tare da kallon shi.
"Tsaya a can zan sayi abu!" Na gaya mishi. Tsayawa yayi bakin hanya daidai kofar wani shagon sayar da maganin, sauka nayi tare da ɗaukar kudi a jakata, ban san nawa bane kawai ina zuwa shagon nace mishi.
"Bani maganin mura" na ajiye mishi kudin, yana gani ya shiga dibo min su, ya tara min, sunan su nake bi, zuba min yayi a laida. Sannan na dauki daya na bude take na shanye a gurin, na ajiye mishi kwalbar, na dauki sauran zuwa motar, tunda na shiga na zauna na juya mishi baya, haka nayi ya shan maganin nan bai tashi sanin abinda nake aikatawa ba sai da na kwalbe Kwalba uku, da na farko biyar yaji karan zuɓewar kwalabe a kasa, wani taka birki yayi tare da birkito ni.Ganin saura Kwalba biyu ina bude ɗaya yayi maza ya gangara bakin hanya, ya kalle ni. Ranshi yayi mugun b'aci, kifa kai nayi sabida maganin ya fara tasiri a jikina.
"Ka gaya min me yasa duniyar take shirin juya min? Innah tace kana samun damar kwanciya dani zaka gudu kabarni, Ansar Yace min kana kwanciya dani zaka gudu kabarni me yasa tunanin su yayi daya ne?"Jan numfashi nayi, sannan ba cire hijab dina nace mishi.
"Ka tab'a ganin mace a tube? Toh yau zaka ganin ni full naked." Na shiga cire kayana ina faɗin.
"Kawai zan baka kaina a wuce gurin, idan nayi haka zamu fi samun nutsuwa daga ni har su."Raba rigar jikina nayi gida biyu, kafin na juya na kalle shi. Kwantar da kujeran nayi baya, kafin na shiga ƙoƙarin cire zanin jikina. Komawa nayi na kwanta, sabida na kasa cire zanin sai na shiga ƙoƙarin cire bra din, anan idanun shi ya sauka akan dukiyar fulanina. Da na fitar da dayan shi. Dayan yana cikin rigar shi. Tausayin ta ya kuma ninka sama da baya, cire rigar shi yayi ya lullube ta, sannan ya motso da fuskar shi, yana kallon yadda take mutsu mutsu da bakinta, kunnen shi ya kai yaji tana faɗin.
"Ba zan tab'a kashe iyayena ba, Innah amma zan iya sadaukar da rayuwata domin shafe tarihina, ina son Hammah Mohan!" Gyara mata kwanciya yayi, sannan ya tadda motar tare da barin gurin da gudu, ina son ya isa Niamey akan lokaci.
*
Damagaram.Shigowa malam yayi ya same Innah tana fadar abubuwan da suka faru, akan rayuwar Moonah, kasakai yayi da bakin shi yana kallonta.
"Me ya faru?" Ya tambaye ta,
"Waye ban da wadannan lalatattun, yazo ya dauke ta har yana gaya min maganar banza ashe na cancanci wofantarwa Maimuna?" Ta fashe da kuka tana kallon shi.
"Baki cancanci haka ba, amma kuma daga ke har Sama'ila kun so kanku dayawa, ai dama na gaya muku dole gaskiya zata bayyana kanta. Ai ba yau aka fara ba. Ai ba yau Sama'ila ya fara ba, ba kuma sabon abu bane.Dan haka ki ha bakin ki kiyi shiru, kiyi addu'a kawai Allah ya takaita hakkin iyaye akan ku. Kin zata yaran da ya raba da iyayen su, hakkin su zai tafi a banza ne? Ba zai tafi ba. Shima gudun tafiyar Ƙaddara yasa shi bai tab'a tunanin aure ba, da ya kuskura yayi auren da yaji yadda ake yinta na gaji da halin ki Allah ya gani, yar dan Uwanki? Zaki wulakanta ta, kamar ba jinin ki. Ai ko da Sama'ila yace ki rike ta karta tab'a bayyana kanta sai ya dawo ce miki akayi zaku yiwa Allah yawo? Ai baba Nasiru yayi gaskiya, dalilin soyayya ta bayyana kanta, yau dalilin SOYAYYA yarinya karama tana kuka. Ki barta ta rayu da abinda take so abu ya ci tura, toh Ni dake muzuba mu gani Allah yabawa mai rabo Sa'a."
YOU ARE READING
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mystery / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....