BABI NA SHA BIYAR

1K 164 6
                                    

🐂🐂BOROROJI🫀🫀 
                   
~The Journey of Destiny💔~
  Mai_Dambu
https://www.wattpad.com/1099088650?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=4lwvUq4CDNgGO6G8hSqWOpKF0xTz1GVp6y7Sxeme%2Fg5OCwGdT5AJbfyarf93zolA7FBbhl2FOh%2FpFU0pdrB84Lq2xdZkHArH%2Bvs7uiWokSFzxRJ27Z5Ikm4Ezg7evEig
Sadaukarwa ga
  Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA SHA BIYAR.

"Sake min hancina!" Na maza na kwace kaina a hannun shi ina lailaya hancin nawa, kamar zanyi kuka. Harara shi nayi tare da cewa.
"Maza zauna a nan na shiga ban daki na yi wanka." Na nuna mishi inda zai zauna na shiga ban dakin.

Sai da na shirya sannan na fito, na same shi yana zaune kwayam.
"Kayi hakuri kaji na Barka kai ɗaya a daki."

Bai kula Ni ba, kamar yadda ban saka rai zai amsa ba, haka na cigaba da uzurin gabana, ban kuma bin takai shi ba, domin abubuwa da zanyi na maganin shi yana dayawa, dan haka na shiga haɗawa ina kaiwa ban daki nasaka shi ya cire kayan shima da kokuwa, haka na samu ta cire na fito na kira Hammah Malik yazo yayi mishi wanka Tunda suka fara yaƙe rawan sanyi.

    Har suka gama ya fito, na shafa mishi addu'o'in, sannan ya kwanta, ban yi tsammanin zai yi barci haka ba, sai gashi yayi dan haka ma na fita na barshi a dakin nayi sallah, ina idarwa na kuma leko shi, ina dawowa na samu bai farka na, dama Baba ya gaya min zai ta yawan barci.

  ***
Kasa zama yayi ya kasa tsayuwa. Kallon Mutallab yayi sannan yace mishi.
"Kasan me? Ba zan iya boye maka abinda yake raina ba, amma wallahi ina masifar kaunar Almamoon" ya faɗa a sanyayye, yana kallon yadda Mutallab ya sake baki, mik'ewa yayi zai fita Ansar ya riko hannun shi.
"Don Allah saurarre ni mana" fauce hannun shi yayi yana zare mishi ido.
"Shika min hannuna, da alamu ka haukace? Ba banza aka yi ta muku kallon masu soyayyar jinsi ba, ashe da gaske ne soyayyar jinsin kake ina zaka kai..."

"Dalla ka min shiru, ka bude banzan bakin ka sai maganar banza kake yaron nan mata maza ne!" Ya fada da karfi, zaro idanu Mutallab yayi tare da had'iye yawun.
"Kasan me yasa na gaya maka? Saboda ina son Yaron ne kuma zan taimaka mishi ayi mishi aikin ya tsaya a mace, wallahi ina masifar kaunar shi. Please my Friend kai ɗaya ne zaka taimaka min shi yasa na maka maganar please"

    Ajiyar zuciya yayi yana kallon shi, Kafin yace mishi.
"Ban san me zan ce maka ba, amma na tausaya maka. Kuma idan na boye maka yadda rayuwa take yana da hatsari, idan yaron nan yana son ganin shi a mace falillahamdu idan kuma ya fison ganin kanshi a matsayin mata maza TOH karka tirsassa mishi ayi abin da zai saka kowa damuwa."

       Riko hannun shi yayi sannan ya ce mishi.
"Na sani, amma abin mafi alkhairi shine a dawo dashi jinsin da ya fi karfi idan aka ce lallai sai an jira ra'ayin shi ba zai yarda ba."  Shiru yayi na wani lokaci  kafin ya cigaba da cewa.
"Tukun kasan inda yaron nan yaƙe? Kasan a inda yake rayuwa? Yana tare da dan primer minister ne, kuma abin takaicin tunda yagan shi ya makale mishi.

     Wallahi ina tsoron kar yaje a lalata goben shi! Ina tsoron kar abin duniya yasa a lalata mishi mutuncin shi, don Allah ka taimaka min ta yadda zan shawo kanshi."

    Shiru Mutallab yayi yana gyada kai kamar kadangaren da ya sha rana.
"Yaushe kenan zamu hadu da Almamoon din, tunda kaga kun kusan komawa makaranta?"

   Ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idanun shi yana kallon yadda Almamoon shi zai koma da yan nonuwa a kirjin shi yana takun kauna a dakalin zuciyar shi. Tashi yayi zaune yana faɗin.
"Insha Allah ranar friday"

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon