https://chat.whatsapp.com/B50yxHYVIcVHx42qCXkmJ9
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....BABI NA ARBA'IN DA SHIDA.
"Mun yarda gaskiya da abinda ka fada,.indai haka Ammyn ta koma dai Du'ai amma wallhi Hajiya Karime bata ji dadin ta ba. Karfi da yaji ta lalata mana Mahaifiya, Allah ya isa"
Shikam apple yake gutsira a hankali, yana murmushin jin dadi, yana kara tabbatarwa kan shi da Kudinta ta saya mishi, wani irin gutsira yayi yana kara taunawa kamar mai ciwon hakori, ganin ya shiga shauki dariya suka yi ta mishi.
"Hammah Mohan yarinyar nan ta maka mugun kamu, kan Uba. Dubi yadda yake murmushi sai kace tana gaban ka"
Sake wata lallausar murmushi yayi yana kara jin wani irin dad'i a ranshi. Kwace Apple din Haddir yayi yana dariya.
"Salman don Allah kace ya bani kayana""Ka bashi"
Suka hada baki suka yi.
*
"Insha Allah, Mohan bai da matar da ta wuce ki, karki damu ina tare dake, karki gayawa Mahaifiyarki. Zan sami yarinyar na ci ubanta.". Share kwallar ta tai sannan tace mata.
"Babu kome Ammyn nagode" tana gurin har taga fitar yarinyar a cikin asibitin, sannan ta koma cikin asibitin. Tunda ta shiga cikin take cika tana batsewa, su kuwa yaran suka ajiye ta a gefe, domin dama babu wannan shakuwar a tare dasu.**
Tunda muka shiga taxi na ajiye kaina a gefe, ina jin wani irin kuka nason zuwa min, amma ban iya yi ba, har muka isa gidan mu. Ina shiga daki na zube a bakin gado tare da sake kuka me ciwo. Na rasa gane meke min dad'i, mahaifin shi ya tafi ya sa nazo, amma ya tashi yana wulakanta ni, meye nayi mishi da zafi haka? Dama baya sona ne?ko dai ya fahimci abinda ya faru ne?"Haka nayi ta kuka ina tambayar kaina, har na gaji nayi shiru, kafin na kwanta a d'akin, baki daya sai gashi na shiga wani irin kad'aici, bana son magana. Washi gari da na shirya da sunan zan tafi kotu, sai gashi na buge da nufar asibitin, har kofar dakin na isa amma na kasa koda budewa ne, haka na gama nazarin abinda zan yi kafin na leka yana rike da Alqur'ani, na jima ina kallon shi, kafin ba juya zan tafi muka yi kicibis da wata Nurse.
"Lafiya!"
"A'a babu kome!" Na juya na fita da sauri, bude kofar dakin yayi yana kallonta, kafin ya leka hanyar wajen.
"Kana niman wani abu ne?"
"A'a babu kome!" Ya fada yana dawowa dakin, itama kallon hanyar tayi tare da kallon d'akin.
"Kalaman su iri daya"Shiga tayi ta bashi magani, yana sha ya nufi window ta waje, ya hangota tana mai juyawa bayan ta kalli window, kura mata ido yayi yaga yadda take share kwalla.
*Meye nayi miki da zafi? Kika juya min baya*Tsare taxi nayi tare da shiga cikin ina dafe kaina, na juya na kalli window, yana tsaye. Sake labulen yayi tare da juya bayan shi.
_Baka min kome ba! Sai dai ƙaddara da ta had'a mu itace zata rabamu! Ni din wani namiji ya wuce iyakar ka ne! Kayi hakuri amma ina kaunarka_
Na fada a raina, tare da jingina kaina, muna isa kotun, biyan kudin nayi sannan na nufi cikin,ina isa Alkali yana fitowa da wasu abokan shi turawa.
"Bonjour Abie?""Lafiya lau, ya jikinki?"
"Da sauki Sosai" na gaya mishi. Tare da barin gurin su,"Alkali amma Yarka ce ko?"
Dariya yayi yana faɗin..
"Maimunari a'a ba ita bace, amma a ofishina take aiki"
"Kai Amma kamar ku ta b'ace, gaskiya."
Murmushi yayi sannan ya raka su, suka tafi shi kuma ya dawo. Ya samu ina waya.
"Eh Hammah ban san dai me nayi mishi ba, indai akan abinda ya faru ne Allah ya bashi hakuri, a'a bani bace yanzun haka ina gurin aiki ban je asibiti ba."
CZYTASZ
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Tajemnica / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....