🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza...._Eh toh nayi ritaya daga Rashin Daraja! Sai dai kuma an koma Gaba gad'i🤫_
BABI NA ASHIRIN DA HUƊU.
Kura mishi ido nayi, ina son ya kuma ce min koda Sannun ne amma fir yaki kallona, da na gaji da zaman kurame yana miko min tea din na dauke kai na. Sake tura min cokalin yayi na kauda kaina. Ajiye kofin yayi tare da mik'ewa yana duba maganin da zai mika min. Shima naki kallon shi sai ma ƙoƙarin sauka akan gadon da nake yi.
"Ina zaka?" D'ago kai nayi ina son kallon shi amma yalwataccen gashin kaina ya hanani ganin shi sosai. Sake yunkuri nayi tare da zamowa zan fad'i, cikin wani irin kulawa ya tare ni.
"Gida zan koma" na fada mishi ina maida numfashi.
"Ok ince kana da kudin jirgi?"
D'ago kai nayi ban san lokacin da kuka ya kwace min ba, tare da kokarin kwace jikina, a hankali ya mai dani saman gadon, sai shesshekar kuka nake? Daukar rigar shi yayi tare da wayar shi ta fita. Bai damu da halin da nake ciki ba. Koda ya fito shekar isa yayi tare da fesarwa. Sam bai iya rarrashi ba, asalima kanen shi basa rikici wannan da alamun shine auta a gidan su, shi yasa bai rena kuka. A hankali yake walking a cikin harabar asibitin hannun shi zube cikin aljuhun rigar shi. Karar wayar shi yaji sannan ya dauka."Ya?" Ya tambaya,
"Ya me jikin?"
"Am think da sauki"
"Mohan anya kana kula da lafiyar shi kuwa?" Inji dan Ba'are,
"A'a Alhaji ina ganin me zai hana ka kwashe min albarka tunda ka bani aiki na gaza" ya faɗa tare da shafa kanshi,"Toh tunda haka ne ai gwara Ansar yazo gare shi" ya caka mishi bakar magana yadda shima zai ji zafi, tsaki yaja tare da katse kiran, yana me jin haushin Dan Ba'are kuma yadda yake ji da zai same shi dan Ubanshi sai ya kirb'a mishi naushi a fuskar shi. Da dan sassarfa ya nufi cikin asibitin.
Yana shiga ya same ni na cusa kaina a tsakanin cinyoyina ina kuka, banging kofar yayi da dan karfi wanda ya razana ni. Na d'ago kai ina kallon shi wani b'ata rai yayi sama da koyaushe.
"Oya dauki tea ko na zane ka" ya nuna min kofin, kallon shi nayi naga yana niman inda zai zauna. Bayan ya leka inda yake saka cajin shi. Wayar cajin ya dauko. Ban manta ranar da Malam Ansar ya zane ni ba, jikina yana rawa na dauki shayin. Na kafa kai na fara sha, yayi sanyi toh kuma sai na fara jin zan yi amai."Idan ka sake ka min amai sai na zane ka" ya zaro min idanun shi. Gyada mishi kai nayi tare da kurb'an ruwan tea din, ina sha ina shafa wuyana. Ina gamawa na je ajiye cup din kawai ya fadi kasa, ya tarwatse. Kafe ni yayi da ido.
"Kayi hakuri ba da gayya bane"
" A cikin albashin ka" ya faɗa min tare da dauke kan shi. Tunawa da nayi, ina aiki dashi ne dan na saya mana gidan da zamu zauna na budewa Babana shafi saura kadan na karasa kudin gidan ban san lokacin da na fashe da kuka ba. Domin nasan kawo ni asibitin ma da kudina ne."Hammah Mohan" a masifance ya kalle ni, sunkuyar da kai nayi ina kallon kasa. Share ni yayi ya cigaba da duba wasu takardun shi, yana turawa a Laptop din shi, da na gaji kwanciya nayi ban san lokacin da barci yayi gaba dani ba.
Jin ya daina sauraron kananun kukan shi ya sashi d'ago kai, sai ganin shi yayi yana barci.mikewa yayi tare da gyara mishi kwanciyar shi, ya lullube shi sannan ya koma ya cigaba da aikin shi. Wayar shi ce ta dauki kara, ya kurawa Number ido, wanda ya saka.
"Abbu" cikin sanyin jiki ya dauka tare da sallama."Babana ka kyauta? A ce tsawon lokaci bamu nime ka ba kai ma ba zaka nime mu ba? Toh duk inda kake ina son ganin ka cikin sati me zuwa kana jina?" Gyada kai yayi kamar yana gaban shi yace mishi.
"Afwa Abbu Insha Allah"
"Khalil ne ya bani Number ka da ba zaka tab'a niman mu ba, ina kewar ka."
"Nima haka" ya faɗa a sanyayye, kafin suka yi sallama,
![](https://img.wattpad.com/cover/273911756-288-k359039.jpg)
YOU ARE READING
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mystery / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....