https://www.wattpad.com/1116236352?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=DqKeHmGUt4S00sTqK6tvHmTwBNce4WSrmwTCLuX9s0%2BZ90klAu0vYuC2%2BG9j3NPu%2BdEkCw%2BpmnVewyRnnYYsyNs%2BbDZEQEPwUVZmfNteR0xffTyfTM0XIqekJsZ5PDHF
HAKKIN MALLAKATA
#Mon-Aug-2021BOROROJI
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....BABI NA SITTTIN DA BIYAR.
Murmushi yayi yana mai kashe datar, yaso ya ga yadda Maimoon din shi take tsiwa, yasa so yaga yadda take masifa. A hankali ya shafa kanshi yana murmushin jin dadi,yace.
"Ya Allah ka zama shedana duk ranar da Maimoon ta shiga hannuna wallahi sai na gyara mata zama yadda ya dace insha Allah"Ya fada yana shafa kanshi, domin yayi wallahi yana jin matukar suka had'e toh ba makawa sai ya bi da ita yadda bata zata ba, sai ya nuna mata shi
namiji ne da ba'a rena shi cikin sauki, duk zai iya hakuri da kome amma ya tsani rashin kunya, musamman irin bata da ta rena shi lokaci guda, bayan yana ji a zuciyar shi da gangan jikin shi tana haukar son shi, shafa fuskar shi yayi yana murmushi.***
Ranar beenah ta sha fada a gurina, su Mommy watsar da mu suka yi, ranar da muka cika kwana biyar Abba da Abbu suka zo, abin ya bani mamaki. Amma ganin su bai rage kome ba, sai kara min kaunar Yaron su, na gaishe su ina kuka."Allah ya miki albarka, Ubangiji ya raya abinda kika haifa, Ubangiji ya shiga al'amarin ku"
"Amin Ya Allah, Amin Yallabai"
Mikewa nayi na koma dakin ina kuka.
"Ka ga ikon Allah! Yarinya ta raba gardama,kaga yadda ta dauko Ubanta, har da Kakanta. " Inji Abba,shi kam Abbu kiran matar shi yayi suka gaisa. Sannan ya gaya mata gashi a gidan su Maimunari, tare da sabuwar Amaryan da yayi,Nan suka shiga wasa,har aka kawo min wayar, sannan suka gama maganar su ne manyan, akan nan da wata wata biyu zasu tawo bikin Beenah da Khalil, anan suka ci abincin rana da na dare, sannan suka wuce,
...
Tana gefena tana waya, wallahi bana jin me take cewa, domin maganar ciki ciki ake yin shi da salon shagwaɓa. Make ta nayi tare da kallon ta.
"Ki kula min da Widad zan shiga ban daki" na fada mata ina nufar ban daki, juyawa tayi gurin Yarinyar tana mata wasa tana waya, bayan na fito, Naji tana sauke nishi a hankali.
Fisgar wayar nayi tare da sakawa a kunnena.
"Khalil karka b'ata albarkan aurenka daga waje, duk abin da zaka yi ka jira ta shigo gidanka meye na wasu abubuwa haka?"Na cilla mata wayar ta, mik'ewa tayi tana tura baki.
"Idan ke ba zaki kula da masoyinki ba, ki bar ni na kula nawa saurayin""Zo nan!" Na kirata, tana zuwa na rike kunnenta.
"Na makale a zuciyar shi ce, sabida soyayyar mu babu kazamta,ina rungume shi duk lokacin da naso, sau daya na sumbace shi ranar da muka sami sab'ani, ke soyayyar ku shirme ce. Ni tawa dashi guba ce domin idan muka hadu tabbas Allah ka dai yasan me zai faru" sannan ba ture ta, dariya ta saka min tare da cewa.
"Matar nan baki da alkibla, shekaranjiya kina ce kin tsane shi yau kuma kina haukar son shi. Duk wanda ya shiga tsakanin kuzari mutu wallahi"Share ta nayi, na cigaba da rarrashin Widad da bata gajiya da rikici.
Haka Mommy ta shigo da kayan da aka kawo mana, akwati hudu, tsayawa nayi ina mamakin wannan al'amarin, kayan yarinya kuwa babu laifi, wai dan ba a can na haihu ba, da na ga kayan jaririyar. Har da sarkar farin gold,
YOU ARE READING
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mystery / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....