HAKKIN MALLAKATA
#wed-Aug-2021BOROROJI
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....BABI NA SAB'ANI DA ƊAYA.
-----------------------------------------------
Ina kuke matan alfarma muna da kayan ado da kawa... Musamman turaren kaya wanda zai yi awa ashirin da hudu a jikin kayan ki, muna da scentball wanda ake wurga shi a wardrob sannan muna da Oil mai dan karen kyau da dad'i! Ina uwar gidan ina Amarya, maza garzayo kar a baki labari kayan mu free order! Sannan ina uwaren gida da amare nesa tazo kusa, muna da kayan Mata ingantattun masu kyau, Muna da gumba mai kyau yar asali, muna da hadin kazar amare mai kyau yar asali sannan muna da Sha daka mai kyau na amare da uwargida! Akwai parkege na amare mace da ta yarda da kanta Hajiya taɓa Ni ta wannan Number:08130269841 sayan na gari mai da kudi gida*
Kaza
Tara bala'i-
Gumba bucket ƙarami-
Gari-
Hatsabibiyar zuma
Hatsabibin gari
Zobe-
Tsumi-,
Maina ya rikice
Zazzogau
Haɗin gigita shi
Maƙale mataSayan na gari mai da kudi gida..... Sai kun zo muna maraba da ku
_______________________________
Cikin kaunar da soyayya mai karfi Beenah ta kula da al'amarin mijinta, shi kuma ya nuna mata yayi kewar ta, anan take shafa mishi Mommy na da ciki.Dariya yayi ta mata, yana cewa.
"Eyye kice zamu yi wasu kanen!"Gyara kwanciya tayi a jikin shi tana cewa.
"Eh mana, Allah yasa ta haifa mana yara maza dukka."
"Kuma kyakyawan irin ku!"
"Kwarai Abie ne ko Mommy kasan shi yafita kyau domin shi baki ne ita kuma fara ce, shi yasa Addah Munah tafi mu kyau.Kaga Baby Widad mana yadda Allah yayi mata kyau ba Uba ba Uwa ba, kamar na boye kayan ta."
Sumbatar wuyarta tare da rungumo ta, ta baya yana shinshina gashin kanta, har barci ya dauke su.
Da asuba bayan sun yi sallah suka kuma komawa, barci.
***
Bayan kwana uku, suka tattara sai Nijar, inda suka yadda zango a Niamey, Khalil ya wuce da matar shi. Mommy kan ita dangana ta akayi da asibiti. Domin laulayi take sosai.Yumnah da Innah suka dawo gida, tare da Baby Widad, abin tausayi yarinya da iyayen ta amma ta zama marainiya, dan ma bata damu da nonon uwar ba, ga Innah tana tattalinta haka sata take ganin Innah kamar uwarta.
... Umma Khalil sun je har asibiti suna gaishe da Mommy, sannan suka nemi a basu Widad. Abie bai hana su ba, sai dai yarinyar taki fir musamman da Hajiya Latifah ta nace dai ta dauke ta, nan yarinyar tayi ta kuka. Haka yasa Abbu yace mata,
"Kina son Yarinyar kika shegenta ta tun bata bata taka doron kasa ba, ai ban zata da kanki zaki ce a baki ita ba, na fi daukar cewa k'iyayyar uwarta ne zai damammali yarinyar ashe ba haka bane "Wani irin kunya ce ta kama ta, karshe haka ta sunkuyar da kai, bata iya mika hannunta ba.
"Hammah Mamman, kayi hakuri ta dauki gudar jinin Mohan, haka zai kara mata imani da tsoron Allah, kuma tayi tuba irin wanda ake son musulmin kwarai yayi.""A'a ai babu amfanin bata, yau Maimunari tana fuskarta rayuwa ce sabida ita, da yau bata rabata da mijinta ba, taya har wani zai samu damar cutar da ita?" Ya tambaye su ranshi a b'ace,
"Amma kuma ƙaddara karban shi ma ibada ce" inji Innah.
"A'a ban da irin wannan,.domin Kuwa son kai ya shigo cikin al'amarin na yarda da ƙaddara amma ban yarda akan cewa kaddara ce tasa Lateefah kashe musu aure ba a daren idan aka yiwa Nairah ko Radiyah ya zata ji?"
YOU ARE READING
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mystery / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....