🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....BABI NA ASHIRIN DA BIYU.
Karar bude kofar yasa shi maza ya mike tare da mai da hannun Almamoon, daidai shigowar Dan Ba'are. Wani irin b'ata rai yayi kamar wanda aka zo amsar wani abu a gurin shi.sai wani hura hanci yaƙe. Dariya yaso bawa dan Ba'are amma ya share shi dan bai da lokacin sa. Gashi ya wani tsare inda Almamoon yake sai wani b'ata b'ata rai yaƙe irin me kazo yi?
Ƙoƙarin leka Almamoon yake ya wani tare shi.
"Meye kake nufi?" Ya wani fada yana hararan dan Ba'are,
"Kai bana son Iskanci ka bari na ga halin da dan mutane yake ciki indai na so kake a fara sintiri munyi kisar kai"Matsa mishi yayi tare da zama yana kallon su,.kai hannu Dan Ba'are yayi zai tab'a Almamoon yayi maza ya dauke kan shi saboda har cikin zuciyar shi yaji haka amma bai wani nuna a fuska ba. Kamar ance ya kalli inda Mohan yake yaga bai wani damu da abin da yake ba, dan haka ya sha jinin jikin shi bai kai hannun ba ya fasa tare da kallon Abokin nashi da yayi mishi mugun sani.
Idan ya fahimtar kamar dai kodayaushe baya son mu'amalar wani da abinda yake tare da shi yanzun sai ya iya cire abin a ranshi yayi mamaki da bai yi haka akan Mamoon dan yasan sun tab'a yin haka akan wata budurwan shi, yarinyar ta makalewa Mohan ba laifi ya fara kula ta, ba wai dan yana son ta ba, kwatsam sai Dan Ba'are ya fara kula yarinyar irin wasan abokin saurayin nan. Har su zauna su sha hira. Tunda aka yi haka a kan idanun shi ya b'ata rai bai ce kome ba. Aka kuma ba biyu bai yi magana ba. Yana tare da su.
Wata talata ya dawo daga tafiya yana shiga gidan su yaga yarinyar me suna Sayyidah tare da dan Ba'are suna jiran shi, yana sauka a motar Mohan ya tattara kashin su ya watsar suna mishi Barka da dawowa, amma fir yaki kallon inda suke asalima kamar bai gansu ba.
Allah Sarki kallon Dan Ba'are tayi sannan tace mishi.
"Ko na mishi laifi ne?" Ta tambaye shi a dame, tab'e baki yayi sannan yace mata.
"Babu abin da kika yiwa ɗan iska" ya faɗa tare da mik'ewa zai bar gurin,
"Ko zaka raka ni na tambaye shi?" Cikin takaici yace mata.
"Dalla can sai kace ba mace ba dan banza ya dawo dan bai kula ki ba sai ki damu karki sake ki fara nuna miki zakalewarki tun ynazun dan wallahi zaki wahala da Mohan.""Toh uban munafukai zaku fitar min a gida ko sai na watsa ku a waje?" Ya fada yana daure fuskar shi alamar babu wasa da sassauci.
"Mohan yarinyar nan tun safe take jiranka kuma ka dawo ka watsar da ita, ai ko babu kome zaka girmama soyayyar da take maka"Kallon mamaki yayi mishi kafin ya gyara tsayuwar shi bayan ya zuba hannun shi dukka biyu a cikin aljuhun wando shi domin wandon unifoam ne a jikin shi sai wata shimi ta soja. Kallon yarinyar yayi daga sama har kasa kafin ya mai da idanun shi kan Dan Ba'are.
"Kanin Ubana ka gama?" Ya tambaye shi tare da mishi kallon kurilla.
"Ayya Ayya Mohan wallahi ina kaunarka da dukka zuciyata karka wulakantani""Ka dauki wannan abin ku bar min gidana idan kuka sake na fito sai na saka bindiga na harbe yan iska mara sa mutunci irin ku masu cin amanar Abota."
Ya juya a fusace kamar zai wuce dakin, yarinyar kamar zata yi hauka, amma Mohan bai saka shi jin ya hakura ba, Dan Ba'are yayi mishi bayani amma fir yaki kula zancen kuma ba iya ita ba yan mata dayawa sun sha wulakancin shi.
Ajiyar zuciya Dan Ba'are ya sauke lokacin da ya koma bayan shi ya tsaya tare da cewa.
"Kayi duk abinda ya dace, Ni zan tafi dashi kai ka koma bakin aikin ka" ya faɗa tare da mik'ewa yana gyarawa Mamoon fuskar shi da take kara tsutsewa.
YOU ARE READING
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mystery / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....