https://www.wattpad.com/1112993401?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=lW5RihoQ3v8FZFWeHyymHjbPBLOXqm7aK4EKMuRrfSy%2BfSjbHsNuLRY8JQnuIpGqm8aZk9dQwvCQ4LSVWXgTHbqEvuaBGA%2Ba9UjO%2FHjd0TMtTTHl8QCE2uzXe1MDgaIR
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....BABI NA HAMSIN DA DAYA.
Ina dawowa ya tare ni da wani shirmen shi, taya zan saurarre shi. Bayan ya gama min duk abinda zai kuma yace zai tab'a mutuncina, akan Mohan na fada gararin rayuwa. Yau shi yake zagin mutuncina, saboda ƙaddara ta faɗa min.
A hankali na shiga ban daki nayi alola nazo na tadda sallah, ina idarwa na kwanta. Gashi auta bata nan ta tafi gida, bani zuwa ko ina.
Tsawon kwana uku ko kofar falon mun ban leka ba, ina kwance. Nasan ban da lafiya amma na rasa waye zan kira, ranar da jikin yayi min tsanani kamar zan mutu. Shine na tashi tare da ɗaukar wayata da ta mutu, dakyar na jonata, tana kawowa na kunnata.Sakon shi sun kai dari dai na Abie da Auta, a hankali na shiga sakon Auta na kirata.
"Auta..... Kizo... Zan ... Mutu" na fada mata, kafin na kashe wayar, na kuma kiran Abie.
"Abie.. zan.. mutu... kirjina... Numfashina" a hankali na fada tare da komawa na kwanta.** Ya fito kenan daga Shari'a, suna tattauwana da wani Alkali, kawai ya ga kiran Maimunari, dauka yayi tare da sakawa a kunnen shi, yana faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, gani nan"
Da sauri ya shiga ofishin sa ya dauki abinda yake da muhimmanci, sannan ya fito. Driven shi ya mike.
"Maza kai ni, Apartment din yarinyar nan"Da sauri ya shiga motar, suka bar kotun. Ita kam Auta tana katse kiran Mohan ta kira dan tana da number shi, yana ganin kamar ba zai dauka ba, ya saka a kunnen shi.
"Hammah Mohan, Maimunari fa bata da lafiya wallahi ta kira wai zata mutu."
Bai san lokacin da yayi watsi da abinda yake ba, ya nufi gidan. Yana isa ya samu ana ta kokarin bude kofar dakin su. Yana zuwa ya daki kofar da kafad'ar shi, amma bai bude ba, cikin zuciya ya ta fi da gudu ya tokari kofar dai da ta balle, ya hangota kwance daga ita dai kayan barci riga da wando, rigar me hannun shimi. Kuma rigar irin shara shara ne.Da wani karfi ya maida Abie waje.
"Don Allah ka tsaya, Iyalina ce karka je kanta haka wallahi mutuwa zanyi idan wani ya kuma ganin matar da zan ajiye a Ƴaƴana" ya faɗa idanun shi na kawo ruwa. Murmushi Abie yayi tare da jin tausayin yarinyar, cire ƙatuwar jacket din shi yayi yana faɗin.
"Kaji a ranka ni Ubanta ne, ba zan tab'a ganin wani abin da zai d'aga min hankali ba, saka mata bamu da lokaci."Haka ya saka mata sannan ya dauko ta cak, ya fita da ita, motar shi ya saka ta. Suka nufi asibiti da ita, kuma dukkan su. Cikin rawan jiki aka amshe ta, tare da nufar dakin gaggawa da ita, tun da ya dauke ta, yaga yadda take zubda kwalla. Haka ba karamin d'aga mishi hankali yayi ba, zama suka yi kowannen su da abinda yake damun shi. Lokacin da Khausar ta fito.
"Me ya faru ne hakan jinin ta ya hau sosai ga zuciyarta yayi mugun kumburi, wallahi aka Cigaba da haka. Zata iya rasa rayuwar ta, don Allah a kula sosai domin rayuwarta yana cikin hatsari" ta faɗa tare da mikawa dan uwanta, takardan fita yayi da mugun sauri. Kifa hannun shi yayi a fuskar shi, tausayin halin da yarinyar take ciki ya kara raunana mishi zuciyar shi, kaunar yarinyar a jinin shi yake jin shi.
Haka ya dawo da kayan da aka bukata, kiran Khausar yayi ya mika mata, ta shiga dashi. Yana zaune a gurin har zuwa azhar, sannan suka fita zuwa masallacin sabida lokacin sallah da ta shigo, bayan sun idar, suka dawo lokacin an sauya mata daki,haka suka zauna a jikinta, aka rasa waye zai tafi ya bar dan uwan shi.
Dole Mohan ya kira Radiyah, ita tazo ta zauna. Sai da ta kwana ta wuni sannan ta farka daga dogon barcin da ta samu, tayi.
VOCÊ ESTÁ LENDO
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mistério / Suspenselove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....