🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....*Barka da Sallah Ubangiji ya maimaita mana*
BABI NA SHA TARA.
Da mugun gudu na danne kofar, tare da sake wata irin kara, me had'e da kuka.
"Ashhhhhh! Ohhhh Auwshhhhhhh" ya faɗa tare da banging kofar, sai da na kuma faduwa, ashe na rufe da hannun shi ne, ina jin ya bar jikin kofar na koma ban dakin na dauko kayana, na saka kafin na fito da sauri. Yana zaune tare da zubawa hannun idanu, zuɓewa nayi akan gwiwa ta, na sake wani irin kuka tare da jin nadamar me yasa na matse mishi hannu, riko hannun nayi tare da sakawa a bakina ina tsotsa su, can na kuma mik'ewa zuwa kitchen na dauko kankara na saka a cikin towel na nad'e shi sannan na shiga matse mishi hannun. Duk abinda nake idanun shi kumshe bai bude ba, sai leka fuskar nake jijjiyar goshinsa sun mike sosai.Mik'ewa nayi ina kallon shi kafin na shiga inda first aid box yake na dauko na mishi dress din hannun sannan na koma na shiga duba hannun.
"Kayi Hakuri" sai lokacin ya bude idanun shi tarr akai na.
"Kayi hakuri kaji"
Lumshe dara daran idanun yayi, tare da gyara kwanciyar shi, haka nayi ta kula da hannun a binka da farin fata sai gashi gurin yayi jajjur bayan ya kumbura, shafa mishi man zafi zanyi yayi maza ya rike hannuna. Idanun shi har lokacin bai bude ba. Sai tauna bakin shi yake tare da lumshe idanun shi duk da a rufe suke, amma haka bai hana shi yin yadda zan Fahimci yana jin matsanancin zafi ba."Kayi hakuri ka ji, nasan da zafi amma haka shine mafita domin zaka ji dadin hannun" a Sannun a hankali yake zare hannun, tare da kauda kanshi yana me jin kamar ya kurma ihu, domin shi kad'ai yasan yadda yake ji.
Shigowar Hammah Malik yaga halin da muke ciki.
"Subhanallahi taya haka ya faru"
"Eh wallahi garin garin garin" nayi ta maimaitawa sabida wani irin kallon da yayi min wanda ya sani jin saura kiris fitsari ya zubo a wandona, kai ban tab'a ganin mugun kallo irin na yau ba. Sannan ya juya ga Malik, ya zuba mishi ido. Shima kuma kamar mara gaskiya shan jinin jikin shi yayi tare da cewa.
"Sir ko zamu kai ka asibiti ne?"
"Ok bari na kawo mishi jacket din shi ya daura akan kayan zai fi kyau kam a kai shi asibitin."
Da sauri na haura sama na dauko mishi rigar Black yayi mishi kyau sosai, ga gashin nan irinta buzayen asali ta wani nad'e akan shi, ba zaka tab'a kallon fuskar shi ka dauka bai da lafiya ba. Saboda kullum cike yake da kwarjini da kamala, haka muka nufi asibitin domin yaki bin Malik sai da nace mishi.
"Toh muje"
Haka ya saka kai ya biyo mu, baki daya ina walwala ne amma bani da nutsuwa domin kuwa ina tsoron malam Ansar sosai,haka aka gama duba mishi hannun shi, sannan muka dawo gida.Zuwa dare sabon zazzaɓi ya rufe mu dukkan mu, dakyar na shiga dakin shi tare da taimaka mishi yayi wanka, amma yana fitowa yanki jiki ya fadi, gashi tikeke, haka nayi ta jan shi.
"Ko zan kira Hammah Malik ne baka da lafiya" lumshe min idanu yayi yana kallon yadda nake son kuka nima zazzaɓi nake ji. A hankali ya dafe jikin gadon tare da rike Ni da karfi sai da na kusan faduwa, sannan ya mike dakyar ya faɗa gadon, tare da fisgo ni jikin shi. Hakoran shi suna haduwa da juna.
A hankali na saka kafana na janyo bargon na lullube shi, sannan na gyara kwanciyar shi, kafin na fara ƙoƙarin zamewa a jikin shi, wasu irin kananun surutai yake tare da faɗin.
"Zasu harbe ni, karka bari su same mi."Ya fada tare da matse ni a jikin shi, yana ƙoƙarin boye fuskar shi a jikina, tsoron kar ya cutar dani ya sani fara mishi addu'o'in, can naji yana sauke ajiyar zuciyar, sai barci me mugun karfi ya tafi dashi. A hankali na gyara mishi kwanciyar shi, kafin na fara ƙoƙarin saukowa a gadon ya rike hannuna, haka na dawo na kwanta a gaban gadon, hannun shi cikin nawa, haka nima barcin ya dauke ni.
YOU ARE READING
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mystery / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....