https://www.wattpad.com/1115798063?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=H4PLUmmQMtRivq0LpRHlS38%2Fr1hLcjzt2XEZ3yHCmyzI3xoWStQC02%2FROcdRbxcPubxgSNp7F%2BbsI7AVD0kyhHL5jlei18XLmYIFmbPXjnlRmUgtZXxtCYJkkmcIRyXT
#sun-Aug-2021
HAKKIN MALLAKATA
BOROROJI~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....BABI NA SITTTIN DA UKU.
Yana son duk abinda zai yi da amincewar mahaifiyar shi, yana son ita da kanta tace mishi ya je ya auro Radiyah, yana bin duk wani sharadin ta, dan a zauna lafiya.
Shi yasa baki daya yaƙi d'aga hanaklin shi, shi yasa yaki damuwa da irin hukuncin da ya yanke, baki daya ya ki mai da hankali kan Radiyah. Burin shi Mahaifiyar shi, ta ji dadin biyayyar da yayi mata, wannan dalilin da yanayin ya saka shi dauke kai akan Radiyah, kuma ita kanta tana mamakin yadda tunda tace bata son ganin su, har yau bai kuma mata magana ba, bai kuma kallon ta da batun ba.
Dan koda tace ya nime auren Yar kawarta amincewa yayi jikin shi har da rawa, haka da yayi ne yasa ta jin lallai zata barshi ya auri Radiyah, amma sai ta nunawa mahaukaciyar uwar su basu da hankali zata amince mishi.
*
Gefe Mohan ya motsa sosai kuma ya maida hankali, duk da yaki zuwa gurin Jalilah da sunan zance haka bai hana a fasa kome ba, Maimunari ce dai yasan ya rasata kenan. Shi yasa ya rungume auren Jalilah bawai dan yana da bukatar haka ba, kuma yau da gobe yana bukatar kulawar mace, idan ya dubi shekarun shi kara hawa suke, matar da yake so baya tare da ita.Dan haka ya watsar da damuwar shi, domin yayi imani da Allah. Tunda mahaifiyar shi taki Maimunari ba zata tab'a kaunarta ba, ya kan zauna yayi dogon nazari akan me yasa kome yazo mishi a jagule! Me yasa kome yake bukata sai ya rasa? Shin ko dan bai kyautatawa mahaifiyar shi ce? Ya rasa gane abinda yake faruwa da al'amarin shi.
Da sallama ya shigo falon mahaifin shi, sanan ya nemi guri ya zauna, kafin yace mishi.
"Abbu kana jin labarin Maimunari kuwa?" Yayi tambayar a sanyayye."Baka tambaye ni, me yasa naki auren Yar Sarkin maradi ba?" Sunkuyar da kai yayi yana wasa da capter din falon.
"Abbu kayi hakuri, nasan tun wata biyu da suka wuce ya dace a ce anyi bikin kuma Allah bai nufa ba, ban san me ya faru ba. Kuma bana son na tambaye ka kar na shiga abinda bai dame ni ba. Ba wai damuwarka bata dame Ni bane sai dai bana son na cika bincike ne!" Ya fada mishi.
"Eh toh da farko yarinyar ta amince amma daga baya taki, wai na mata tsofa, na zata ko wani abu nayi ashe iya kawai girman da nayi ne, shine nace mata toh babu damuwa, kuma Allah yasa haka shine mafi alkhairi." Ya fada yana kallon Mohan da ya sunkuyar da kanshi.
"Mohan Maimunari ta kusan haihuwa, domin cikin ta ya girma. Sai dai kuma tana cikin damuwa ne, domin ko kwana biyu da suka wuce naji labarin bata da lafiya jininta ya haura." Da sauri ya D'ago kan shi yana kallon mahaifin shi.
"Abbu don Allah, ka hada ni dasu, dan girman Allah ka taimaka min, ina son sanin halin da Mata ta, take ciki ne idan ma cire abin cikin za ayi a cire. Ta huta wahalar tayi yawa""A'a yanzun take da wata takwas, idan aka cire karfi da yaji, abin cikin ba zai rayu ba..Insha Allah sunce nan da sati Uku zasu mata aikin shi." Kamar Ya fashe da kuka,yana faɗin.
"Abbu don Allah" ya zube gwiwar shi a kasa, idanun shi jajjur.
"Kayi hakuri! Insha Allah akwai lokuta da zaka ganta.""Abbu kafin nan na kuma rasata kenan, na rasa ta har abada, ina kara hango nisan da take min, Abbu kayi wani abu, sabida ni Khalil ya hakura da Benazir, an tace ba zata aure shi ba dan zan auri Jalilah, don Allah Abbu kayi wani abu, don Allah ka taimaka min kar ya rasa yarinyar da take so, na yarda zan dauki kome amma ban da na zama sanadin rasa masoyin shi."
ВЫ ЧИТАЕТЕ
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Детектив / Триллерlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....