BABI NA ARAB'IN DA HUƊU.

885 218 19
                                    

https://www.wattpad.com/1110763041?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=PYEroEpzcfPkMnsivXwBeeuxpzKGK0fkWNcFQtCIRTayJ6sMVuy4zCFcXax%2BjsXVmcWqYu7JpcasekmM2WVikzyWFlN%2FH2zr4nlW%2F5vRpIWR%2BVC4yv60%2F1T6BeQc23Yo
🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA ARAB'IN DA HUƊU.

Ajiyar zuciya na sauke lokacin da na fahimci na bar Maradi naji burkina ya cika, hankali na ya kwanta. Taya zan fuskanci Innah da wannan abun. Share kwalla nayi tare da alkawarin ko wuta tace na fada sai na shiga saboda na kyautatta mata.

***
Karfe tara na safe.
Fitowa tayi tare da kallon falon a gyare, zama tayi tana kallon hanyar sama, tana nazarin yaushe zasu fito. Karar sautin takalmin Benazir ne ya sa ta, d'ago kai tana kallonta.
"Beenah ina Addah Munah?" Wannan shine tarbiyyar da tayiwa yaranta da ita kanta, indai Babba ne zata kira shi da sunan manyan tare da nuna musu cewa babba ne a bashi girman shi.
"Mommy bata dakin ki ne?"

Kallonta tayi sannan tace mata,
"Kamar ya bata dakina bayan ni nake tambayarki,"
"Toh ai bata dakina ne, dan ta shigo da asuba tana fita na farka"
Wani irin rawa Jikinta ya dauka bata san lokacin da ta nufi waje ba.
"Malam Idi bakuwar yarinyar nan tana iya?"
"Hajiya ai ta tafi, gashi wannan tace na bawa bakin jiya da suka shigo." Ya mika mata, fararra takardan, ganin har da tambarin Asibitin su yasa ta koma cikin gidan, ta duba jakarta. Samun nata tayi, jikinta a matukar sanyayye ta bude shi.

*_Assalamun Alaiki, Dr Zainab. Ina kara mika ta'aziya ta na rashin mijinki, na tausaya miki kamar yar da ta rasa mahaifinta Uwar da ta rasa mijinta. Allah yayi miki ni'imommin rayuwa ta ko ina, na gode da ƙaramcin ki a gare ni. Nagode sosai sai gashi ina tsaka da miki bayanin zan koma gida. Mohan Mamman Nasir ya zo min, don Allah ki taimaka min da rufe sirrina, kisan yadda tafiyar kaddara take, baka shirya mishi. Idan ya same ka haka zaka yi hakuri dashi, sannan kiyi hakuri na miki sata ban tab'a sata ba. WALLAHI ban tab'a zina ba. Kiyi hakuri ki rufa min asiri kodan rayuwar Yaranki nan Benazir da Yumnah. Suma mata ne idan kika boye nawa Allah zai boye naki da nasu, naso ace Mohan shi ya fara ta'adina amma sai gashi ƙaddara ta faɗa min. Ban sani ba ko iyayena dayan su ya tab'a wata ne ko yar wani ne ban sani ba, amma nasan zina Bashi ce. Idan kuma biya aka yi a kaina Ubangiji yasa haka ce mafi Alkhairi aka ina bashin ya tsaya haka kar ya cigaba da tab'a halina nagode sosai ina jinki kamar uwar da ta haife ni Maimunari I Umar Wodaadabe_

Kuka take kamar yanzun aka mata mutuwar mijinta. Wani irin kaunar yarinyar take ji har cikin ranta, ta kasa magana sai kuka kawai take tana karawa.

"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, Ubangiji, me yasa? Allah na tuba"

"Assalamu alaikum" Mohan da Dan Ba'are suka yi sallama.
"Wa'alaikimun salam!" Benazir ta amsa musu itama tana share kwalla, yarinyar tana da hakuri kamar mahaifinta tun rasuwar mahaifinta sai ta nutsu sosai,

Tun ba a gaya mishi abinda yake ba, jikin shi ya bashi Moonah ce tayi wani abu. Shiru yayi yana jin sautin kukanta har cikin kanshi, ya tsani yaga mace tana kuka komi kankantar ta kuwa.
"Meke faruwa?" Dan Ba'are ya tambaya,
"Sai ka tambaya ne? Moonah ta tafi?" Ya fada kamar baya son maganar. Kallon wai haka ne dan Ba'are yayiwa Benazir. Mika mishi takardan da Dr Zainab ta amsa a hannun Malam Idi, shi kuma ya mikawa Mohan.
"Ka karanta mana" inji dan Ba'are,
"A'a kai ka karanta" kallon shi yayi sannan yace mishi.
"Na yarda da kai ne"
*_Amincin Allah ya tabbata a gare ka ma'abocin tausayi da taimako ban sani ba ko zamu sake haduwa, amma dan darajar iyyenka karka nime Ni! Idan ka Kuskura ka tawo nima na. Zan tafi zan tafi zan tafi garin nisan nisa! Mohammed Mamman Nasir Mohan Aghali! Nasan kai waye nasan kai dan manya ne! Mohan nasan kana Sona! Amma kuma a yadda kake son ba zai mana amfani ba! Son ba zai mana rana ba, son ba zai amfane mu ba! Mohan ka duba mana yanayin mu! Ni yar talakawa ne futtik kai kuma ɗan shugaban kasa! Gaskiya kayi hakuri bamu dace da juna ba! Nagode sosai daga me kaunarka Maimunari_*

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt