https://www.wattpad.com/1107772644?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=bf4OKGFXFm%2BbTBcRYFtIWwkeTpAjYWx%2Ft%2B8piwgYnGj%2BHz02%2BCq8Olw61eWGNCGWLrWoWOYkU9DLRDRLwKRvQ2vFDZM4QGfJKL8gnNicMhI2rfKBsb98bQg%2Fv%2BXS7kmh
🐂🐂BOROROJI🫀🫀~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....BABI NA TALATIN DA BIYU.
"Na gaji wallahi na gaji, ina son na rayu da abokin tarayya, babu amfanin boye ni da kike yi. Don Allah ki barni na rayu kamar sauran Yan matan don Allah kinji na had'aki da Allah dan girman Manzon Allah karki hanani rayuwar da ta dace dani" na fada cikin kuka, ina me rokon ta ina kuka ina. Bata hakuri amma bai saka Innah tausaya min ba, duk da tana dukana amma ban fasa rokonta ba,, sai yau zancen Baba nasiru ya dawo mata. Lokacin da Malam ya ke gaya mata zancen sai yanzun ta kuma kara fahimtar dalilin da yasa Munari take sake kin zama wajen ta,ashe soyayya ya faɗa.
_Duk abinda zai sanya shi bayyana kanshi tabbas shi zai sanya shi kuka! rayuwar shi zagaye take da zanen ƙaddara dan haka babu wanda ya isa sauya ƙaddaran wani_Kura min ido tayi sannan tace min.
"Ba zan baki damar ki salwarta da rayuwar wasu sabida naki ba. Soyayyar da zata zame miki masifa? Ko ba soyayyar da zata zame miki Bala'i ba, Munari ina miki kallon mutuniyar kirki ashe idanun ki sun bude har kina yarda namiji ya dauke ki ko ya rungume ki, Munari tunda kika iya haurawa katanga ya sani fahimtar soyayyar da ta saka ki kika iya haurawa katanga, soyayyar da tasaki kika tambaye ni zaki rayu akan jinsin ki ba karamar abu bace ko ya kwanta dake ne? Kike tsoron kar ya gudu ya barki"
Dariya nayi domin yanzun kam na fara hango tsagwaron zalinci da son zuciya na fara fahimtar abinda Innah take nufi dani?.
"Innah zargina kike dan ina son shi! Abinda na sani na haukace akan shi. Innah ina son Muhammad ina mishi mahaukaciyar so ne. Amma duk da haka ban tab'a kusantar zina ba, Innah wallahil billahi azim ban tab'a zina ba, amma kike tambaya na ko ya kwanta dani? Innah tun ina yar miciciya nake kare kaina, Innah na shiga jami'a na kwana a dakin da maza suke ban yi zina ba sai yau rana tsaka ai wallahi ko wani ne ya gaya miki zan iya bazaki yarda ba, balle balle kuma ke da kika da na dauke ki kamar Uwar da ta haife ni"Da mamaki take kallona, kafin taja wani itacce ta rufe ni da duka. Tana kuka tana dukana, ban yi mamakin dukar ba, amma yadda nake jin zuciyata ko zata kashe ba zan fasa ba.
"Ki dake ni, ki zage ni matukar zaki barni a raye toh wallahil ba zan fasa ba, kuma ba zan bar kaina a matsayin namiji ba, Ina son rayuwa dan haka duk abinda Kiyi min matukar zaki bar ni da shi ba zan tab'a zama a ?matsayin namiji ba da bakinki kike kirana karuwa bayan ban tab'a ba, ko ciki nayi na kawo miki bazaki kirani da karuwa ba sai dai ki min Uzuri. Innah kawai rayuwa nace zanyi mike min haka ina kuma da nace zan gudu sai kin kashe ni duk abinda zaki yi kiyi
"Ni zaki tozarta kamar yadda Iyayen ki suka tozarni, ni zaki wulakanta kamar yadda iyayenki suka wulakantani, bakar ƙaddara, ai tunda iyayenki suka gudu suka barki babu wanda zai iya zama dake, Shegiya yar iska, ni zaki watsawa kasa a idanu?"
"Nasan da iyayena suna raye ba za su bar ni haka ba, kuma da suna nan ba zasu wulantani haka ba, zasu bani abinda nake so ki dake ni idan har dukar zai cire miki bakin cikina Innah ki dake ni, na gaji ina son Yancin."
Shigowar Baba yaga yadda take dukana kuma ban fasa fadar abinda yake raina ba, yasa shi amsar itaccen.
"Baki da hankali ne? Kan me zaki tirsassa mata? Dole ne?" Ya fada da karfi, tare da tasowa ya d'aga ni.
"Baba don Allah ka barni na rayu kamar kowacce mace, wallahil zan kama kaina, don Allah ka Amince min na rayu."
ESTÁS LEYENDO
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Misterio / Suspensolove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....