https://www.wattpad.com/1110533172?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=aSbcpjgn9asSsm9lZXK1GTYd1hkBoALGTEin2VPj2rrHh0qsHukAEkcdgVB%2Bbd47RHlGBNNnsyrNYAxk4FDLM8zZE%2BhDR1NGlY7Kh7sDrXNrEAQA9XmoAHfTO2Lcqj9H
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....BABI NA ARAB'IN DA BIYU.
Gurzawa yake cikin wani irin shauki me mugun dad'i, har yaji shi ya shige cikin jikinta kamar mahaukaci a zauce da ita, ya gigice domin bai tab'a kawowa zata kai mishi ba, dan haka lokaci guda yaji an shake mishi wuyar shi.
Ban san yadda zan kwatantata muku yadda nake ji ba, ban san wani irin yanayi nake ciki ba, sai dai duhun da na fahimta yana rufe min idanuna, karar da naji wanda ya tafi da jina da gani na baki daya, daga nan ban kuma sanin me ya faru ba, na ga dai ana tafiya dani da gudu, ina wuce wani irin haske. Sai muryan da ban san ta waye bana yana kirana can da nisa.
"Munnah!!!"Cikin wani irin faduwar gaba ta fito bayan ta gama sauya kayan ta, tana kallon abokan. Aikin da da suke mata magana, jin su take amma ba zata ce tana sane da abin da suke fada ba.
"Dr Zainab kina lafiya?"
Wani irin bugun zuciya taji lokacin da aka shigo da wata mara lafiya, mai da kallonta tayi kan yarinya domin a hannun wani mutum take yana niman agaji.
"Ku taimaka min don Allah," da sassarfa ta isa gabanshi. "Ku kawo min gadon dauka marasa lafiya." Ta fada da karfi, yana kawowa aka daura Maimunari, kallon Dr Zainab yayi tare da cewa.
"Don Allah ko nawa ne a duba lafiyar ta, don Allah" ya faɗa kamar ya cire ciwon a jikinta ya mai da nashi, da sauri suka wuce da ita d'akin tiyata, aka fara kokarin kunna wutar da zata iya haska inda ciwon yake, domin ta ga yadda mara lafiyan take.Domin zanin gado ce a jikinta, daga haka ya tabbatar mata da zargin da yake ranta, musamman da ta kwaye zanin da ya lulluba mata, kwalla ce ta shiga sauka daga idanunta. Tana kuka kasa kasa, kallon Nurse din dakin tayi tare da cewa.
"Kuje kawai ku kira min Dr Fadime da Dr Annah."
"Toh Dr" suka fita, a hankali ta mike tare da shafa kan Maimunari, kwalla na zuba mata, kwaso kayan aikin tayi tare da saka Safar hannun, ta fara duba ta sosai musamman gaban da ya fara alamar zai kumbura, yatsin ta gwada sakawa taga bai shiga dukka ba, da sauri ta cire tanadi mamakin yadda aka haka shigowar likitocin biyu ya sata kallon su . "Ban tab'a ganin irin wannan tashin hankali ba, ina ganin cases na Fyade, amma ban san yadda aka yi wannan case din ya tsaya min a rai ba."
"Kai Dr meye na rashin hankali, wannan case din ba sabon abu bane, idan kika yi dubi da Yadda ake samun kananun yara ma ana musu fyade balle kuma babban budurwa kamar wannan.Ina ganin ba wani babban tashin hankali bane, kawai a dubata idan aiki ne sai mu hadu muyi mata, amma ki bar kuka haka." Inji Dr Annah.
Kallon su Dr Fadime tai sannan tace musu.
"Amma ai naga mutumin da ya kawo ta ya biya kome, idan ba ita ta kai kanta ba taya zai sami damar lalata mata rayuwa yan matan mu na yanzun basu da kamun kai, gashi nan ya kai ta ya baro ta. Idan aka gaya musu su kame kansu maza basu da amana su ga kamar karya kake musu gashi nan bata wuce ashirin ba amma dubi yadda namiji yayi mata fata fata, wallahi na fi tausayin Yara kananu da ake musu haka sama da yan matan da ake musu wannan aika aikan, meye amfanin zubda mutunci ne? Shi ba aurenki zai yi ba kin je kin bashi jikinki""Akwai ƙaddara! Dr ki duba yarinyar mana, dubi fuskarta mana? Dubi yadda gefen fuskar ya kumbura sakamakon dukar da aka mata! Yarinya shekara ashirin, meye tayi mishi? Waye nata ya tab'a yar wani? Kisan yadda fyade yake da ciwo? Karki yi fatan haka ya faru da makiyinki ma balle masoyinki, karki yi fadan wannan mummunar yanayin ta faɗa kan wanda kika sani, wallahi akwai ciwo." Ta rushe da kuka, ta kasa aikata kome,."Dr Bawai muna zargin yarinyar bane, daga Yanayinta ya samu fahimtar halin da ta tsinci kanta amma kuma ai yan matan ne suka zama sai du'a'i,"
Gyada kai tayi zuciyarta yayi nauyi tace musu.
"Muna da y'aya mata, addu'a itace makamin mumuni, Allah ya kare mana su duk inda suke." Tana kallon su, suka gama aikin su tsaf, sannan suka mata sai da safe domin sun tashi aiki. Ita kuma ta Cigaba da lura da Yarinyar.
Sai da ta gama gyara gurin tare da rubuta magani sannan ta shafa mata wani cream kafin ta mike, faduwar da gabanta ya kuma ne yasa ta komawa ta zauna dabas, kuka ya tawo mata, sosai tayi kukan da rabonta da tayi tun ranar da ta rasa abinda ta haifa, mijinta abin alfahari ta, Uban Yaranta abin kaunarta. Kallon yarinyar da ta gama dubawa tayi, sannan ta mike, ta sanya mata ruwa da allurai. Ta gyara mata jikinta. Har lokacin kuka take.
أنت تقرأ
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
غموض / إثارةlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....