Wata tafiyar..

1.5K 167 13
                                    

I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx
     '''Zaku iya samun kayan mu daga turaren zamani na wuta, shu'umar humra, dambun nama na mata, tsumin. Da sauran su kayan mu ba irin nasu bane sai an gwada akan san na kwarai..... Akwai haɗin kayan amare da na uwargida...🗣️🗣️Friday  Promo!!! Buy 13pcs @15k only : Turaren wuta 5pcs, humra 3pcs, Turaren tsugunno, shu'umar humra, mopping and toilet perfume, curtains and carpet parfume &kasko💃🏻💃🏻'''

🐂🐂BOROROJI🫀🫀 
                   
~The Journey of Destiny💔~
  Mai_Dambu
Littafi na D'aya...

Sadaukarwa ga
  Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris

_🙄 Daga farawa naga yadda kuke sakawa Dan baki namu ido fa😛🤭 Wallahi ko hmm_

BABI NA UKU.
Wata tafiyar.

Sake baki Salihu Muhmuda yayi tare da Amadu.
"Amma zamu haɗu" suka fada mishi,.mik'ewa yayi cikin rashin tsoro yace musu.
"Idan muka hadu abinda kuka bani ku hanani" ya faɗa yana fita daga kujeran,
"Mara mutunci"
"Lokacin da aka zo rabon shi bana nan"
"Mugu"
"Eh gadon shi nayi"
"Dan iska kawai"
"A'a sai dai guguwa"
Ya fada tare da barin tabirin su, kamar zasu fasa jarabawar, karshe haka suka mike zasu kai, sai a lokacin Amadu ya kai idanun shi kasar tabirin su ya lura da rubutun da Almamoon yayi ya ajiye musu. Da sauri suka dauka. Murna kuwa baki yaki rufuwa.

Koda suka gama, fitowa suka yi. Tare da samun shi a kasar bishiya ya zauna yana ta rubutu, idan ka ga hancin shi har baki, daga gefen fuskar shi kuwa saje ce ya kwanta gwanin ban sha'awa.
"Kai mara mutunci" banza yayi musu.
"Mun gode"
" Da aka yi me?"
"Da bamu amsar da kayi"
Kallon su yayi sannan yace musu.
"Ai ina mamakin yadda Uwayen ku suke kashewa jakuna kudin makaranta." Ya fada tare da mik'ewa.
"Wawa kawai dan baki duna"
"Eh toh ta yiwu ni bakin ne, amma kuma ina takaicin haduwa da katon jaki" ya faɗa tare da nufar hanyar ajin su.
"Almamoon dan me gadi"
Cak ya tsaya tare da juyawa ya sake murmushi, kafin tace mishi.
"Eh toh dukda haka yafi cirani" da Yaron ya ji abinda ya gaya mishi fasa ihu yayi tare da burgima, an zage mishi uba an can dan cirani.

      Haka yayi ta kuka har Malamin su ya shigo tare da tambayar su meye ya haɗa su.
"Zagina yayi na bashi hakuri" inji Almamoon,
" Karya yake cewa yayi Ubana dan cirani"
Tsaki malamin yayi sannan yayi musu fada.
... Bayan sun gama jarabawar suna nufi hanyar gida, yau ya shirya musu tsiya shi yasa bai kula su ba.
"Yau idan muka je gida zan samu anyi mana abinci me dad'i?" Suna son yayi magana amma dake yayi shiru basu kuma takalo shi ba.
 
Haduwa da wasu yan samarin unguwar su, suka tsaya tare da make su, amma ban da Almamoon, wuce su yayi. Sai da suka bar gurin.
"Mamoon kai wani irin mugun mutum ne ka ga sun tsare mu ba tsaya ba."
"Me ya faru daku?" Ya tambaye su, kamar bai ga abinda ya faru ba.
"A'a babu"
"Nima naga alama" ya ga musu tare da wuce su, matasan nan ba kome yasa suka make su Amadu Bukar da Salihu Muhmuda ba, sai dan tsokanar su da suka yi, kuma akan idanun shi suka tsokane su. Shi kuma baya tab'a bin bayan karya.

  Haka suka isa gida idan suka gaya mishi maganar banza ya gaya musu wacce tafi tasu muni.
"Dan banza munafuki wanda baya yarda yayi wanka a gaban mutane." Wannan maganar tayi mishi zafi, da gaske ne baya tab'a wanka a gaban mutane, kuka kamar yadda babba zai shiga ban daki yayi wanka, haka shima yake. Rasa amsar basu yayi har suka isa cikin gidan, zasu nufi dakunan iyayen su yacewa Salihu..
"Ka tambayi Iyakar me yasa bata wanka a waje"
Ya gaya mishi sannan ya shiga dakin su. Samun Innar shi yayi tana ta daman cura fura da aka kawo mata aikin shi take.
"Sannun Innata"
"Sannun D'an albarka, dauki abincin ka yau Allah ya taimaka malam ya samu dan albashi ya sayo maka shinkafa aka dafa, duba ka gani har da nama."

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!حيث تعيش القصص. اكتشف الآن