https://www.wattpad.com/1108559379?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza.BABI NA TALATIN DA HUƊU
Murmushi yayi sannan yana me kallon hanya.
"Sabon Allah ba a girma yake ko a shekaru ba, abu ne da kowa yanka iya aikatawa idan Allah ya zare mishi imanin shi, duk wanda kika ga bai sabawa Allah ba Toh Allah ya tsare imanin shi ne, dan haka ki daina tunanin zan miki wani abu dan kawai ina son ki. Idan har kina mata masa ban ji wani abu ba."A hankali na jingina kaina a jikin kujeran motar, kwalla yana zuba min, na kalli rayuwata tun daga farko har zuwa yau, akan tsarin Innah yake, ko sau daya ban tab'a bijire mata ba, Toh me yasa ba zata fahimci abinda nake ji ba? Me yasa ba zata gane yadda nake ji ba? A iya sani na ban tab'a sha'awar na kwatantata kwanciya a tare da namiji, sai da ya zama dole lokacin ina mata maza ya sani kwana daki ɗaya da maza, ban tab'a tsayawa sun shirya a gabana ba, ban tab'a yarda mun shiga wanka tare ba, kafin su tashi sallah Asuba na riga su. Bana sallah a tare su, kome ma bana yi a gaban su, amma haka Innah ta jefe ni da kalmar karuwanci.
Kofar wani katafaren gida ya tsaya tare da danna horn, da sauri sojojin suka bude gidan, ya tusa kan hancin motar cikin gidan, ashe gidan shi na Maradi wasa ne, a hankali yake jan motar har muka yi ta tsalleke get by get, sannan muka shiga cikin gidan. Kallona yayi sannan yace min.
"Wannan gidan shekara biyar kenan da na fara gina shi, da Alamu kece zaki fara bude min shi. A da ban shirya kome ba, amma dawowar mu daga Dubai ya sani kara himma domin kuwa ban sami soyayyar gaskiya bane yanzun kuma na samu soyayyar gaskiya,muna ga gidanki nan da zamu shirya rayuwar mu."Ya fada tare da parking motar shi a wani gefen,. Fita yayi sannan ya bude min motar na fito, ma'aikatan gidan duk suka fito. Tare da gaishe shi sannan suka gaishe ni. Haka muka yi ta ratsa cikin gidan, har zuwa babban falon. Katon hotona ina Almamoon ne a falon sai na shi kusa da nawa.
Kallon shi nayi sannan ya ce min.
"Tsakiyar nan hoton dan mu ko yar mu na fari zamu saka, gefen can kuma na biyu zamu saka hoton shi a can, amma nafi son idan Allah zai bamu ya bamu Y'a mace, ina son Y'a mace musamman me kama dake"Ya ja hancina, ture hannun shi nayi ina faɗin.
"Ni mai kama dakai nake son, idan har na haifa maka."dariya yayi sannan ya nufi kitchen ya samu babu kome amma kuma alamar ana kula da gidan ya nuna, dan gaba da gidan akwai masalaci, kiran sallah aka yi na kalli agogon hannuna.A hankali na mike tare da nufar hanyar kitchen ɗin, ina shiga na same shi ya cire rigar shi ya daura afro, ya mai da hankalinsa kan girki, nad'e hannun nayi a kirjina, ina murmushi.
"Hammah Mohan" d'ago kai yayi yana kallona,
"Zan yi sallah ashe girki kake?" Na fada ina murmushi.
"Nasan Abar kaunar nawa ba iya girki ta iya ba, shi yasa na mai da hankali akan girki mijinki yana son a raya mishi cikin shi."Jingina nayi da bangon ina kallon yadda ya mai da hankali akan aikin.
"Sallah" na fada a hankali,
"Ok" ajiye aikin yayi tare da kai ni wani dakin ya nuna min, sannan ya dawo ya cigaba da aikin shi, lokacin da na idar da sallah kuka na sha sosai, ina ƙoƙarin tuna ta ina iyayena suke.Ta ina zan gansu? Yaushe zasu zo gare ni tunda Innah ta gaya min gaskiya guduwa suka yi,su kuwa akan me zasu gudu su bar ni bayan ina bukatar su a rayuwata. Karan bude kofar nayi ya sani kallon hanyar da aka bude kofar, shine ya shigo yana goge hannun shi, alamar shima alolan yayi zai gabatar da sallah. Ganin ina kuka bai saka shi ya fasa ba sai da ya gama yayi min magana.
VOUS LISEZ
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
Mystère / Thrillerlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....