*🐂🐂BOROROJI🫀🫀*
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
BOOK ONE
https://www.instagram.com/batool_spices
Fatima Batool enterprise
Yaji
Ginger and garlic
Onion powder
Pepper soup
Curry
Biryani spices
Mixed spices
Indian spices
Arab spices
Chai masala
Baharat blend
Tandoori blend
Thai masala
Garam masala
Provence
Tea spice
Zobo powder
Gu garzaya Domin samun kayan kamshi na fatima batool Enterprise. Domin samun yajin suyar na naman layya 😋Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azi_zatDuhun Damina....
BABI NA SHA UKU..
Tun daga ranar da na shiga cikin gidan, nake fama da ciwon kai. Gashi Mutumin baya barina, idan ya kama ni niman hanyar cutar dani yake, amma Alhamdulillahi tunda duk abinda zai min Allah yana kawo min Malik akan lokaci.
Yau kwana na tara da zuwa gidan, zuba min kaya yayi yana faɗin.
"Duba ka gani, sun maka?" Ya tambaye ni,
"Wallahi ba zan saka matsatsun kaya kamar dan iska ba, dube su fa, wannan duk gwiwar a yage?" Na fada ina kwalallo idanu waje."Toh wallahi ban isa ba Yallabai dan Ba'are ne yasani na sayo maka duba har da kayan kwalliya irin na mu, koda yake dan kana yana yi da Mata ne yasa baka son." Yadda ya ga na haɗe rai yasa shi jan bakin shi.
D'aga kayan nayi, sai da tsigar jikina ya mike, idanuna suka cika da kwalla.
"Yanzun don Allah Ni ne zan saka su, gaskiya ba zan iya saka kayan ba"
"Toh kwashe ka kai dakin kasa, ka ajiye." Haka na kwashe kayan ina mita.
"Kawai dan kashe kudi za a wani tattaro min wasu kaya kamar dan iska"Kuma ban da jaraba wallahi babu muni a kayan kawai ban saba bane. A hankali na zuba kayan tare da shirya su. Ina kallon kayana, na shafa su. Kafin wani tunanin ya fado min a raina. Matse hannuna nayi ina me jin kwalla na ciko min idanuna.
"Kai Dan daudu, dalla fito mun yi baki daga Niamey"Da sauri ka sake kayan na fito a hankali, ina raba idanuna.
"Zo nan munafiki bakin munafiki, gaka baki ga bakin zuciya, wato dan Ba'are ya kawo ka? Ni Khalil Ibrahim zai ja dani?"
Ta nuna kanta. Sannan ta kalli Malik,
"Ai kaji abinda Firaminista ya faɗa? Dan haka kar na kuma ganin ka a cikin gidan nan,kai kuma duna muje"Haka ta sani a gaba har zuwa dakin shi ya farka daga barci, kifa mishi mari tayi cikin tsoro ya sauka a gadon, jikin shi yana rawa. Sake marin shi tayi, idanuna suka cika da kwalla dan ji nake kamar Ni take duka. Zata kuma na kare kanshi, da bayana tare da rungume fuskar shi.
"Don Allah ranki shi dade kiyi hakuri, wallahi bai da lafiya bai san meke damun shi ba." Na fada ina kuka.
"Guard" ta faɗa da karfi, cikina ne ya cika da ruwa, sautin tsoro.Suna zuwa suka yakinceni ajikin shi, suka shiga takani tare da duka na, abin tausayi ya koma gefe can ya zauna yana kallon yadda suke duka na, kanshi a tsakanin cinyoyin shi. Sai da suka ga bana numfashi.sannan suka jani kamar kayan wanki suka watsoni ta step, nayi ta dungure ina fadowa har na iso kasa, dariya ma'aikatan gidan suka saka sannan kowa ya kama gaban shi.
Tana gama abinda zata yi ta fito daga dakin shi, haka ta kira Hurayyah ta kawo mata ruwan sanyi, ina kwance suka zuba min ta kunne na, sai da na tashi zaune, da gudu na haura sama, ina kai last step ya saka hannu ya turo ni, rike rigar shi nayi, ina kallon shi kafin ya ingizani na fado da baya, rayuwar duniyar nan cike take da al'ajabi, idan kana cikin talauci kace Allah ya kika? Idan kana cikin wadata fitinar zamani ta addabe ka, idan kana mulki rubabbun mutane su hana ka aikin kwarai.
أنت تقرأ
BOROROJI....The Journey of Destiny!!!
غموض / إثارةlove and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....