Sirrin zuciya..

1.1K 215 24
                                    

*🐂🐂BOROROJI🫀🫀*
                   
~The Journey of Destiny💔~
  Mai_Dambu
BOOK ONE

Sadaukarwa ga
  Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris
I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx

_Alhamdulillahi books dina baki daya wanda nayi su na kuɗi suna Okada akwai masu cewa suna bukata basu da Whatsp toh ga dama ta samu ku garzaya Okada na akwai su baki daya a can da sunan RamlatArManga_

_🙄🙆🏾‍♂️ Yanzun batun mata maza ya kare an koma Malam Ansar daga Taimako 😭 sai ya zama Shayyi 🙄😏_

*Assalamun Alaikum Jama'a, Ina iyayen da suke nimawa Yaransu malaman Lesson a cikin garin Kano! Dayawa basu da lokacin da zasu zauna sunyiwa yaran su extra lesson a gida toh shakurumin ku! Akwai dalibai mata shin ke Uwa ce? Indai har haka ne toh kin tab'a tunanin akan yaranki ko? Toh indai haka ne Mommy akwai Yan matan da suka kware a fanin computer, Islamic Studies! English da sauran darusa. Karki manta Yan matan nan dalibai ne, dan haka suke niman hanyar tsayawa da kafar su. Idan kika basu karki yi tunanin kome kisaka Allah a cikin lamarin zai tsaya mana Save our ladies please ku Basu damar koyar da Yaranku insha Allah zaki ji dadin haka, hausawa sunce a rashin tayi akan bar araha! Za a samu wannan damar ce idan kana garin kano a tuntube wannan Number 08147787720 mun gode only Kano sai an gwada akan san na kwarai,*

Sirrin Zuciya...
BABI NA BAKWAI.
Sai da Almamoon yayi musu bayani da irin taimakon da Malam Ansar yayi mishi, sannan ya daura da cewa.
"Bana tunanin kome akan malamina, sannan idan ma za ayi magana ne sai dai ace shi din Kamar Yaya yaƙe min, don Allah ku daina Yaɗa labarin karya akan mu.

   Wallahi Billahi azim, malam bai tab'a min kome ba, asalima Alkhairi ne a tsakanin mu, idan nace zan fadi Alkhairin shi yawa ne dashi, dan haka kuyi hakuri. Shima Malam Ansar yayi hakuri. Da bai shiga lamarina ba, haka ba zai faru ba, su kuma masu jin ba dad'i a kaina suyi hakuri." Ya fada tare da sunkuyar da kanshi.

          Hannun shi ya had'a a fuskar shi yana kallon yaron, idan ya nutsu yana magana a yangance wallahi sai ka dauka irin yan matan nan ne, Yayi imani da Allah da zai samu hutu fatarshi sai tafi haka kyau da haduwa. Balle kuma ya haɗa sabulai da mayukan shafawa.

   Kawai hango Almamoon yake cikin riga doguwa, kamar wanda aka buge kanshi ya girgiza kai yana kallon yaron da kyau. Malamai da sauran mutanen cikin dakin taron suka bashi hakuri, da kuma tambayar shi idan bai yafe ba a dauki mataki.
"A'a ni kam na yafe"
Ya fada tare da niman izinin zai fita, babu wanda ya hana shi, anan malam Ansar yayi magana me kama hankali, tare da nuna musu muhimmancin Almamoon a cikin makarantar idan har suka sake wani abu ya same shi tabbas za ayi ta.

     A kasar bishiyar lim ya same shi yayi nisa cikin tunani, dafa kafad'ar shi yayi da sauri ta cire hannun, yana karamin murmushi.
"Yallabai"
"Kaine Yallabai, me yasa ka yafe musu?" 
Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Suna jin babu dadi ne sabida ni ba kowa bane, kuma ina zuwa aka bani Matsayin da suka jima suna so, ko ni aka yiwa haka zan ji babu dad'i balle kuma su da suke tsofin dalibai na makaranta."

"Na zata kayi hakuri ne dan kawai an baka"  dariya ce ya subuce mishi a dan karamin bakin shi. Yace,
"Wai ni din banza? Ni din wofi akwai mutane dai da su din wasu ne, na hakura ne dan bana son tashin hankali, kome ya wuce A bar zancen" ya faɗa bayan ya mike daga kujeran, yace.
"Na gode da taimako, zan koma dakin kwanan mu"
"A'a ban yi niyyar ka koma dakin ku ba, idan kuma kana zargina da abinda aka fada ne toh shi kenan ka bar gidan."

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora