SAUYIN RAYUWA (BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

SATURDAY, 19TH MARCH,2022.

(4)

_______________

Wannan shi yafi yiwa iyalan Baban Abul Dadi,musamman Abul da ya kasance yafi su wayo,sannan shi yana da lura musamman da duk Wani abu da ya shafi mahaifiyar su,saboda Abubuwan da Baban su yake wa maman su ya tsane shi nesa ba kusa ba.

Gashi duk yadda suka Kai da nishadi da ya shigo gidan ze hau masifa,ba dama suyi wasa da dariya se ya fara musu hayaqaqa.

babu dai kyakkyawar alaka a tsakanin shi da Yaran shi gaba dayan su,Suma basu damu da shi ba kuwa .duk da Maman su Bata Basu wannan fuskar ba,so a bayan fage suke kiyayyar tasu,sedai a hankalce ai  tasan basason ubansu.

Kamar yanzu dai suna nishadin su sun kachame suna ta tuntsira dariya Saudatu na basu labarin Wani sabon malami da aka kawo musu yau a islamiya,Ina malaman nan masu mugun kalkala da iyayi,toh haka uztazu izzu yake. sun dage suna ta dariya Dan Saudat ba dai iya kwaikwayi ba,ga iya gwada yadda mutum ke yin Abu, se kawai ganin shi sukai tsulum.

Dama da tsaki ma ya shigo falon,Cha yake "Toh toh ,toh toh.oh ni na rasa se yaushe Zaki girma kiyi hankali wallahi Abida,ke kenan kullum ki zauna a cikin Yara kiyita kyakyata dariya kamar wasu sa'oinki?

Haba duk makota sun San ku Baku da hankali ..Wani wawan tsaki yaja ya juya ze fice ,sake juyowa yayi yace .."Abul ungo nan akwai ledar tsire da naci a mota jeka dakko"

A kan dole Abul ya tashi,Dan maman su ko a wasa bata nuna musu Raina uban su ba duk da irin wulakancin da yake musu kuwa.

A waje yayi parking,saboda haka waje Abul din ya fita ya dakko tsiren a mota ya dawo ciki, straight ya nufi dakin Baban su yaje ya Kai masa ya Mika harda mukullin mota ya juyo abunsa se daki.

Ji Dan Allah dan dawowar nan da Baban su yayi ,Taron ya watse gaba daya.

Da ace ma yayi horn sunji alamun ya dawo toh tabbas baze shigo ya tarda kowa ba,se fa ita maman tasu,dan sun iya drama ,Dan a guje suke tashi su fada dakunan su,inko lokacin ya Kure yadda baza su iya tashi su gudun ba,se kaga sun bingire da bacci karya.se su bar maman su a zaune ita Daya .toh yau ba dama tunda shigowa kawai yayi

Ita ma da da yadda zatayi ,wallahi da Bata ruga ganin fuskar Baban Abul ba,Dan gaba daya yadda ya nuna mata soyayya a da,se ya zama yanzu kamar an chanja shi ne completely.

gaba daya ita baza ta ce ma tasan dadin aure ba ,yo wane dadin aure? Chab! Ai sedai a makota ko Kuma a mafarki ko littafi da film nan take ji da ganin soyayya,Amman Banda a rayuwar ta ta gidan Baban Abul.kyak

Yara dai sun watse ,Abul dama yana Kai Sako ya tafi daki,Kai shifa Abul yadda baya kaunar mutuwar sa haka ne baya kaunar Baban sa,duk randa aka ci sa'a fa Baban su be fita da wuri ba toh wasan buya ake tsakanin shi da Abul.dan Abul se ya wuni daki saboda ya tsani ganin maman su na kuka ko kwalla Kuma indai Baban su na gida wannan kwallar dole ne se ta yi.so se ya gwammaci zama a daki abunsa ,se in Baban ya fita sannan kagan shi tsulum ya fito nan fa Kuma zeta bin duk hanyoyin sanyaya ran maman su ,su wuni suna nishadi abun su .

Queen ma ta wuce daki ita da kannen ta,su kam sun ma yi bacci abunsu.don Allah ya yaye musu kwadayi,su garau garau ma yafi musu dadi a bakin su,Dan haka harkokin su tsire wannan duk daga baya ne .

Maman Abul ce a kofar dakin tare da tullutsetsen cikin ta,cikin yar siririyar murya take fadin "Sannu da zuwa Baban Abul".

Be amsa ba ,dama Kuma tasan baze amsa din ba,se ma sababi da ya cigaba da yi yana cewa ..kinsan zan sake fita tunda nabar mota ta a waje , Amman se na ce Miki ki hada mun ruwan wanka kafin ki hada,Abida me yasa wai gaba daya kin chanja ne,gaba daya kin debo wasu halayen banza su kike yi ne ?"

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now