SAUYIN RAYUWA (BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
MONDAY, 4TH MARCH,2022.
(3)
______________
Cewa yayi cikin wata narkakkiyar murya "Dan Allah baby ki dawo,ki dawo,Zaki dawo please,uhmm?"
Wannan magana yayi ta cike da shagwaba kamar irin yaron daddy din nan.
A yayin da yake wannan kashe muryar ita Kuma Abida ya kashe mata jikin ta murus.
Gyara zama tayi tana jingina bayan ta a kujera tare da sake sauraran ci gaban maganar sa domin Jin da yayi tayi shiru.
Cewa yake "Uhm Uhm ,baby zanyi kuka fa ,talk to me manaaaa"
Cike da kasala hadi da mutuwar jiki gefe guda ga bugun zuciya tace "what do you want me to say?"
Murmushi yayi Dan Jin yadda jikin ta ya yi sanyi ko daga alamun muryar ta,Hakan shi ya tabbatar mata da cewa sakon sa ya Isa a karo na biyu.
Ce mata yayi"Baby kice komai ma"
Kan ta Kai ga yin magana se waya ta fara shigo mata,Abid ne yake Kiran ta Wanda ya kasance saurayin ta da suka shafe shekaru hudu tun tana yar tatsitsiyar ta.
Tana ganin Abid ne yake Jira tace wa Hashim .."please let me answer this call, I'll call you back"
Wani tururin bakin ciki yaji Dan Hashim irin mazan nan ne Masu mugun kishin jaraba.
Amman ya ya iya? Sahun giwa ya take na rakumi,dole yana ji yana gani yayi yake ya ce ba komai ya kashe waya ..
Har wayar tayi missed call ma,dole Abida tayi dialing number din Abid din ta kira shi.
Kan yayi picking bari muyi tsogwami.
Abid Asalin sunan shi Naufal,Dan shekaru 22 a duniya Wanda ya girme wa Abida da shekaru 5 cif cif ,Dan Asalin garin na Kano ne me cikakken tarihi.
Mahaifin sa Alhaji Ahmad Abubakar haifaffen garin Katsina ne ,Amman zama ya kawo su Kano da aiki , Katsina se da ziyara.mutum me dattako da sanin kimar dan adam.danshi Daya tilo wato Naufal,kamar yadda matar shi ma ta kasance Daya wato Hajiya Aminat .ita kuwa Asalin ta bayerabiya ce.
Kuna mamakin yadda Naufal ya koma Abid? Toh ku daina.Soyayya ce ta Maida Mai sunan shi haka ,dole Kuma ya amince ,kamar yadda tarihin Naufal ma ya dade da shafewa a bakunan mutane dan musamman ma shi Naufal se da ya Siya rago aka chanza Mai suna saboda sunan budurwar sa da yake so ne Abidan,shi kuwa male version of za name is Abid. Toh Kun dai ji
"Assalamualaikum hello cutie "
Yace bayan ha daga wayar.Daga dayan bangaren tace "wa'alaikassalaam Abidina"
Yaji sanyi ya sauka a dukkan Wani makwarari na zuciyar sa,yace "cutie kin manta yau ko?"
Cewa tayi "Na manta ka Kuma,ah ah ni ban manta ka "
Cewa yayi "Yawwa cutie,toh ya Akai ba'a kira ni ba,tun dazu fa kika ce "just a minute Abidina, I'll call you back" seda na gaji na kira ki
Dariya ta sa saboda ya kwaikwayi yadda tayi maganar a dazun da suna waya tace tana zuwa
Cewa tayi "wallahi Wani ne ya amshi number na shine fa ya kira muke magana "
Wani irin mugun bugu kirjin Abid yayi,Dan be taba kawo wannan irin kalan tunanin ba a Kansa.sanin da yayi wa Abida Bata taba bawa ko Wani namiji fuska ba,bare har a Kai ga number ,ko Kuma ma waya.kai duk sauran maza ma a gun Abida mata ne,saboda yadda Abid yayi gin soyayyar sa na shekaru hudu a zuciyar ta musamman yadda ya tabbatar ya gama da ita duk duniyar soyayya yasan shi kadai take gani take ji.kenan tashi ta same shi matukar Abida ta fara Bada number wayar ta ai an samu matsala.
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
Fiction généralelabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...