SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(23)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Toh Ina Yan #teamHashim ne? Ya rayuwar ku ?
✨💕✨💕✨💕
Ta bangaren kasuwancin hashim kuwa yana tafiya dai dai gwargwado Alhamdulillah.
Tun asali Mai nasibi ne dama Kuma Allah ya rufa masa asiri sosai yana da rowar Kuma Amman yana samun kudin.se dai fa Shima ba Wani ci yake ba yanzu sosai.har Gwamma Gwamma da.amman yanzu kam? Se godiya!
💕✨💕✨💕✨💕
A gida da ta Isa take gayawa su Abul sabon aikin da aka chanja mata.
Da suka zauna ne Kuma suna magana da Hajiya mama take tambayar ta wanne tafi so,se take cewa zata ruke aikin ta duk ,Indai maman ta yarda ,saboda ko ba komai in ta kawo Abul ai se ya maye gurbin tukin akan tana ji tana gani ta bari a kawo Wani .
Bata dai gaya wa Maman ba,se dai Koda tazo gida a washegari se jikin ta ya matsa mata Wanda dole yasa ta aika Abul gidan yaje Koda mama zata fita kafin ita ma ta taho in taji dadi jikin ta ..
Da Abul ya Isa gidan yana yiwa Ibrahimu bayanin shi Dan mama Abida se ya Bude Mai suka shiga ciki.
A landline din da ta kasance a ko Wani guri na gidan hatta dakunan masu aiki da me gadi ,shi Ibrahimu ya kira cikin gida.
A nan ya sanarwa Zahra cewa Abul yazo yace maman shi ta Aiko shi gun Hajiya mama .
Akai wa Abul iso yana falon kasa ya samu gefe guda ya tsugunna Hajiya mama ta sakko
Kallo Daya ta masa taga tsantsar kyau da Allah yayi masa,sannan ga wata irin bayyananniyar natsuwa wadda batayi kama da ta aro ba,irin natsuwar da Yara masu ladabi keyi in sunga manya ,manyan na wuce wa su koma sak halin su,Koda ba rashin natsuwar bace .
Ta lura shi kam kamar haka yake,domin komai na jikin sa ma a hankali yake motsa shi.
gashi hatta maganar sa a nutse yake yin ta Sam bayada kawaramniya.
Zama tayi suna gaisawa,a inda yake gaya mata cewa "Maman su ce bata dan Jin dadi tace yazo ya ruke mata aikin tukin nata.."
Abun yawa mama Dadi dan dama fita take son zatayi yanzun,se aka ce mata iya Abida bata zo ba.
Daman shiryawa take aka Sanar mata da zuwan Abul,gashi tunda Abida take bata taba fashin zuwa ba,se ta fito taji ko lafiya,Ashe ko ba lafiyar ba.
Natsuwar Abul tayi mata sosai sosai.sannan Kuma batayi musu ba tace ya Jira ta,zata fito .
Koda ta sauko ta same shi suna dan hira da Ibrahimu,kusan duk hiran irin kirkin iya Abida ne da yadda duk kowa na gidan ke son ta.
Shima Dan zaman shi na mintuna kamar 30 a gidan ya fuskanci yadda mutan gidan ke girmama masa mahaifiyar sa.
Se abun ya Mai Dadi matuka,saboda tunda aka ce ga yaron iya Abida yazo suke ta zuwa suna ganin shi.
Ba ma Zahra da ta kile tana ganin shi taji ya burgeta.
Daman Dan karatun da take a yanzu yasa ta dage fada take da iyayen ta kan cewar wallahi baza tayi aure a shekarun ta ba.ita karatu zatayi,Kuma tafi son in ta tashi yin auren tayi shi a birni ..
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
Ficción Generallabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...