(28)

49 4 0
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(28)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Da niyar zuwa gun Zahra ya tashi,Amman maganar mama gaba daya ta kashe Mai karsashi.

Tsakani da Allah shi ba yaro bane ba,Shima a kan Kansa yasan yaci ace yana da iyali,sedai shi iyalin da yake so mace ce wadda ta San kanta ta Kuma horu da aiki ga tarbiyya wadatacciya.

Ba wai "Bae" ba,ya fi son wadda ta iya girki ,wadda ma ko auren sukai zata iya kula da shi sannan ta kula da gidan da ya'yan su.

A toh kar fa ku manta,shi fa likita ne,ba wai samun isasshen lokaci ze na yi na zaman gida ba,so a irin situation din sa,se yake so yayi kokarin ganin ya samu mace da zata cike musu wannan space din.

To amma daga yadda Maman sa ta ke ta zuzuta masa Sarah da yadda ta iya gayun ta,se yake ganin kamar ba irin Sarah bace ta dace da tsarin nashi..

Se dai Kuma yana tunanin,shin ya akayi yake tunanin cewa ita Zahra zata iya rike Mai wannan ragamar? Tabbas gare shi ita din ta iya aikin da girkin da komai?

Toh ta iya yiyuwa ko dan yadda  yaga Abulkhairi ne,daga yanayin tarbiyyar da yake da ita tunda Zahra kanwar shi ce ai yana sa ran ita ma a same ta da tarbiyya,Kuma Kila zata iya cika wayannan guraben da yake so ya samu macen da zata cike masa .

In ma ba haka ba,ai you can't judge a book by its cover,daga Zarahn har Sarahn I mean..

Amman tunda ranshi ya kwanta mai da Zarah,ze fara gwada ta,in be same ta a yadda yake so ba,se yaje gun Sarahn da Maman sa ke so. Dan dama shi ba wai ya ki bane ba

A wannan rana dai be iya tabuka komai ba,dan ko a asibiti ma beyi Wani aiki ba.

Files ma na wasu manyan mutane ne su biyar ya duba ya gan su sannan ya Kara wuta abun shi ..

Unguwar su ya nufo,kawai se ya kira Abulkhairi a waya yace mai ya turo mai address din gidan su..

Abulkhairi be nemi ba'asi ba ya aika da address wa oga Sufyan .

Shiko oga Sufyan hanyar zuwa gidan kawai ya dauka..

Oga Sufyan kenan ,manya gatan wasa!

❤️✨❤️✨

A shago me suna Go gorgeous dake kan titin Amadu bello way dake cikin garin Kanon dabo..

Humaira ce da Soffy sun baje se zaben kaya suke ,wai za'ai color picnic na bikin wata hadiza friend din su.

shine suka je Siyan dress ko Abayan da za su Saka suje color picnic din..

A zahirin gaskiya ma Hummy kawai dauriya take yi saboda sabanin da suka samu da Bashir Saurayin ta kafin su fito daga gida..

Shi dama irin mazan nan ne masu masifaffen zafin rai da fadin ran azaba,magana daya se fada.

Kwata kwata bashi da fahimta wallahi.

Kuma Ina irin fadan nan da se a share kwanaki ba'a shirya ba? Toh irin wannan abun yake se kace Wani yaro
.
se chan Kuma da kan sa se ya kira waya ko ya zo,dan iska se kace Wani me kwankwamai 😂..

Toh a yau ma fadan sukai,kamar wasa suna waya ana Shan hiran soyayya se take ce masa zasu fita Siyan dress ita da soffy zasu biki gobe ..

Yadda kusan Ubanta da ya fara zabga mata masifa wai bata tambaye shi ba zata Wani je biki wani biki,bikin banza bikin wofi ,fada fa ta inda ya shiga daban da inda yake fitowa? Hmm

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now