SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(55)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________💕✨💕✨
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Kwalliyar aka cigaba da yi wa queen,yayin da me kwalliyar take ta faman tsatsubo da duk Wani boyayyen kyau da queen din keda shi ..
Bayan kamar mintuna gonna da yin waya da umma hassana,se ga wayar shi Uban gayyar da kan sa,dauka tayi cike da farin da idanuwan ta da aka gama zuba musu nau'ikan ado domin su fito su kayatar da kwalliyar da ake rangada wa fuskar queen din..
Murmushi yayi kafin yace "Amaryar Dr,I can't wait"
Murmushin tayi ita ma tana cewa "Kai Yaya"
Mene na cewa Wani "Kai Yaya" ya fada yana kwaikwayon ta..
Dariya tayi me dan jinjirin sauti,se yace "bama wannan ba,Mama ce ta kira ni,tace ko ba'a gama kwalliyar nan ba nazo na dauko ki"
Ya fada yana mata dariyar mugunta..
Cewa tayi "Kai Dan Allah Yaya,an fa kusan a gama mun ,Kuna kowa nayi se nice Banda ni"
"Ah toh,yace "ni dai dan Aike ne"
Bayan ya shaida mata cewa Yana nan Tafe.
Sauke wayar sa kenan wayar mama na sake shigowa ,an samu kusan mintuna talatin ,maman ta sake kira taji ko sun taho,wai Ashe har a lokacin ba'a gama kwalliyar ba,balle Azo maganar daurin dankwalin Amarya,kafin a zayyana mata vidiyoyi da Yan fotuna irin na al'adar wannan rikitaccen zamanin..
Hawaye queen ta fara ganin cewa mama da gaske take wannan fadan..
Dama Kuma fa kafin ma su tafi gun kwalliyar seda mama tayi ta fama akan queen ta shirya ta tafi da wuri kar taje ta samu matsala..
Ba tare da queen tayi hanzari ba ta gama nuku nukun ta kafin ta tafi suke biya suka dauki su yusaira Yaran cousins din Sufyan din da suke wa queen qawaye na biki sannan fa suka tafi gun makeup..
Isar su gun make up suka tadda amare biyu a gaban su se queen ta uku.dama Kuma ma se da daddaren jiya alhamis ne ma Sufyan yasa maman Amal ta nemo wacca zatayi wa queen din kwalliya..
Kudin kwalliyar ma da aka biya har 100k domin anyi late payment,sannan event din rana ne,da yake sunje gun wata me kwalliya a Kano wai ita mumue (mumue ni na hada abina,in Kun ga dama kuje Kuna binciken wace mumue 😂),wacce ta shahara wajen tsara kwalliya ta amare da mabiyan su,se kawai ta Bata time din first bride don kar ta makara,tace Amarya ta tabbatar tana cikin studio din by 12,toh Amaryar ku salalo salalo se bayan biyu taje..
Shine Kuma Duk bayan wayannan wahalhalun Kuma queen tazo ta makara,Dan me kwalliyar ta bata 12 ba queen ta Isa wajen ba se past 2..
Ina ce kunga yanzu ta Hawa kanta fada a wannan babbar rana tata?
Sauri sauri me kwalliyar tayi wa queen final touches bayan ta tsaya tayi sallar maghrib sannan sukai dauri,cikin hikimar ubangiji har se da Dr ya qaraso aka samu akai musu pictures kafin suka shiga mota suka tafi venue din Kamu da ta koma dinner ..
Ba ko shakka Uncle Baba ya daddage ya fidda su queen kunya,domin ya kama wannan shahararren gurin bikin nan ne me suna Maltidives events center.(Shima in Kun ga dama ku binciko shi 😂)
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
Beletrielabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...