(43)

39 4 0
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(43)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

💕✨💕✨

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Tunda suka fara tafiya shiru daga ita har shi ba Wanda ya tanka wa Dan uwan sa,se dai kowa da abunda yake sakawa a ran sa.

Ita a bangaren ta tunanin ta ya karkata ne wajen son nemo dalilin da ya Sanya ya taho da ita daga kofar gidan ubanta.aww ba gidan ubanta ba daga gidan su ya kawo ta nan unguwar..

A  gaban cafe 25 taga yayi parking inda ya kalle ta yace "just a minute" ya fita ya rufo kofar ba tare da ya kashe motar ba.

Tare da sakar mata sautin taushi cikin yaren larafci na wakokin Maher Zain..tuni shaukin soyayyar Annabi Muhammad (SAW) ya fara dulmiyar da ita ,tsananin dadin yabon da Maher yake wa Annabi Muhammad (SAW) ya Sanya ta dafe kirjin ta a dai dai saitin zuciyar ta..

Ji take tamkar tayi ta jawo ranar haduwa da Masoyin Allah,Dan gatan Allah,Annabin rahama fiyyayyen halitta ,Masoyin zuciyoyin da yawa,Amman inaa,Hakan ba dama ..ya Hayyu ya qayyum,ka bamu rabon saduwa da Masoyin ka,ka bamu rabon zama dashi a Aljannah madaukakiya..Ameen thumma Ameen..

✨✨

Famous coffee buns din Cafe 25 me azababben dadi ya siyo musu tare da chilled and thrilling signature melonylemony din su,gefe guda grilled chicken da wrap 🌮 ya fito yana takun sa na takama da sanin cewa akwai idon masoyiyar sa a kan sa..

Cike da tunanika da shaukin soyayyar Sufyan a  cikin zuciyar ta,gefe guda Kuma ran ta kuma tsoron irin matakin da Mama zata dauka a kanta take yi na biyo shi da tayi suka baro gida ta gano shi tafe da wata yarinya tana biye dashi da paper bags din cafe 25 a hannun ta..

Alamu sun nuna siyayyar da yayi ne aka zuzzubo mishi a cikin paper bags din tare da biyo shi da akai da su ..

Har ya bude motar Yana ce mata "hi" bata dawo daga sake saken nata da take yi ba..

Snapping fingers din shi yayi a gaba fuskar ta,yayin da ta sauke ajiyar zuciya sassaya,ta juyo tana kallon shi cike da sanyin jiki wanda ya kasance mata dabi'ar rayuwar ta tare da wani dunkulallen aiken soyayya na daga eye ball to eye ball..

Shagala sukai da kallon juna yayin da ita Kuma ta lumshe idanun ta saboda kaifin sakonnin da yake aika mata ta cikin kyawawan kwayayen idanuwan sa..

Wani irin yanayi me cike da nishadi da walwala da nitsar da zuciyar da ma take cikin damuwa suka tsinci kan su a ciki..

A zuciyar Sufyan yake cewa "Allah Kaine shaida akan irin son da nake wa yarinyar nan, soyyayyar ta da nake ji har sakani kuka take ni kadai ya Rabbi kana gani,kai mu alfarmar samun ta a matsayin matar Aure na ta Sunna matukar da akwai alkhairi a cikin tarayyar mu,ya Allah duk Wani fitinanne,ko fitina,Wala daga mutum ko akasin sa ya Allah ka Kore mana,ya Allah ka makantar da shaidan akan dukkan al'amuran mu da rayuwar mu ya Rabbi"

Hawaye ne yake gangaro wa daga idanuwan Sufyan cike da raunin zuciya tare da wata matsananciyar soyayyar ta....

Jin shirun da yarinyar da ta biyo shi da kayan shi waje ne taji  yasa tace "Uhm Sir sorry"

Sannan fa ya tuna ya juyo ya kalle ta dan dama kafa daya ce a ciki daya Kuma a waje ,dan da ya zauna se ya juya Yana kallon ta..shine fa soyayya ta tashi ta kamkame su suka tsaya kamar an dasa su..😂

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now