(37)

48 5 0
                                        

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(37)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

💕✨💕✨

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Kallon Sufyan Abulkhairi yayi,se yace masa ,"zo muje kaga,inda zan zauna a office in da Wani abu se kazo ka kira ni"

Cewa Abul yayi "Tohm insha Allah"

Tare suka fita daga dakin zuwa office din da Sufyan din ze zauna me gadon marasa lafiya a ciki Abulkhairi ya ga office din,sannan ya koma.

A kan yar kujera ya zauna cike da gajiya ya fara yin karatu ,beyi me tsayi ba ,ya rufe da Addu'a ya tofawa maman su,sannan ya dan gyara zama,Shima baccin ya dauke shi ..

💕✨💕✨

Washegari

Ba masu lafiyan ba,hatta mara lafiyan ma bata motsa ba har se da Asuba ,balle suji motsin ta suma su tashi..

Se da Asuban da suka tashi fa sannan,shi Abul ya fita masallaci.

Zahra kuwa wanka tayi tunda Bata sallah,se azkar da tayi.kafin ya dawo ta gama Shirin ta tayi tsaf da ita.

Allah da ya taimake ta kuwa se gasu shi da Sufyan din.yana shigowa ya ganta tsaf da ita

Seda ya dudduba mama duk da tana bacci sannan ya zauna.

Gaishe su Zahra tayi shi da yayan ta.

Amsa mata sukai da tambayar me jiki,tace "Alhamdulillah"

Karfe 6 nurses suka zo suka duba su ,akwai alluran da sukai wa Mama,suka chanja mata drip tunda dama wannan ya kare ..

Gida Sufyan yace ze je ya dawo, fita yayi ya tafi,da yake sassafiya ce ba Wani maganar cikowa.shaaa se gashi a gida har ya Isa .

Part din Hajiya mama ya fara zuwa ,a palon ta ya tadda su Nabila sanye cikin Uniform din su suna cin breakfast me rai da lafiya. A jiya shi ya ma manta da batun wata makaranta,ashe Nabila ta tuna ita tunda sune masu zuwa.ya mace kenan.

Gefe guda an zuba musu abinci a cikin kananun food flask da robar ruwa da robar lemon,abun gwanin dadi.

Shi Kuma iya ciye ciye se yace "Ah lallai Yan gatan mama,ni Kuma se na bada chocolate da biscuit kenan ko"

Gaishe shi sukai cike da murnar ganin shi. Suna cewa "eh"

Nabila ce tace "Yaya Ina Adda,ya jikin mama?"

Yace "jikin mama da sauki sosai,tace a gaishe da Dr da Yan biyun ta.Adda ma tana asibiti tace tana gaishe ku"

Cike da murna suka amsa,gaida Mama yayi ita ma a mutunce sannan yace zeje yayi wanka ya fito,se yayi dropping din su off a makaranta.

Cewa Mama tayi "Toh in ka tafi dasu a mota in hajara bata san makarantar ba taya zata koma ta debo su,Dan dama yanzun ma ita ce zata raka su?"

Cewa yayi"eh haka ne Kuma,se muje da hajaran se ta gano daga chan se ta dawo "

Cewa Maman tayi"Toh hakan yayi kyau"

Fita yayi daga palon ya nufi part din maman shi Dan su gaisa duk da yasan ba lallai ta fito ba iyanzu.

su Kuma suka cigaba da dan Hira, mostly ma maman ke musu tambayoyi su Kuma suke bata amsa .

Aiko duk nawar Sufyan a wanka yau kam be dade ba yayi ya fito,dan ma ya tsaya yayi pupu gaye ne da tuni ya gama tun dazu.

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now