(33)

54 5 0
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(33)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

💕✨💕✨

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Tun daga sanda Zahra ta fara waya Maman su bata iya koma wa bacci ba,se ma kasa kunne da tayi tana sauraren irin hirar da suke yi,duk da amsar Zahran kawai take iya ji.

Bata ji Wani hirar banza ba ko hirar wofi,se hankalin ta ya kwanta.

Amman kuskure daya da ta tabbatar bazata sake yi ba a a rayuwar ta shine ,sakacin da tayi a lokacin da ta yi zaben abokin rayuwar ta ga mutumin arziki na kwarai,ta yadda shi ta zabi kyalkyale banza.

Shigo dakin Zahra tayi Sadaf Sadaf zata kwanta,se maman tace "Dama kin daina sanda dan zaman jiran ki nake yi a nan, ido na biyu,zo nan ki zauna"

Zama Zarahn tazo tayi kamar munafuka..

Mama ce tace "abu na farko da zan gaya miki shine,duk wata waya da zakuyi da shi,kar ta sake haura karfe goma na dare,ki gaya masa cewa Mama tace duk inda karfe goma tayi an gama waya.

Abu na biyu kuwa na yadda ki ajje duk wata kunyar ki chan a kaina,duk wayar da Zaki, toh kiyi ta a cikin mu,a  gabana Zahra sedai in ba wayar Arziki bace dama..

Na gaba kuwa shine yanzu ki gayo mun hirar da kukai har ta dauke ku tsayin wannan lokacin Zahra..

Cike da tsoro Zahran ta gaya mata yadda sukai gaba daya ,har cewa da yayi auren ta yake son yi ba wasa ba..

Hamdala Maman su tayi sannan taji dadi,anan ta ruga bata shawarwarin da ya kamata ,tare da tsawatar mata a kan wayar banza da hirar rashin kamun Kai ..

Sannan tace "kar kiyi saurin sakin jikin ki Zahra saboda kar ki gamu da ciwon so tun yanzu.ki bari se ya fara magana da iyayen sa sannan ,dan Ina ganin kamar ba lallai bane iyayen sa su yadda ya aure ki..

"Zahra ko ban gaya miki ba Kinga halin namiji a gun baban ku.

ba irin wahalar da ban Sha ba a gun shi tare da ku, sanadiyar baban ku hatta Yan uwana seda suka juya mun baya Kuma kin gani,Kuma wallahi da ba haka yake ba.

Kafin na Aure Baban ku ba irin dadin bakin da be mun ba,Allah ya gani ni ba mutuniyar banza bace tun ada,Shima Kuma haka,se dai akwai irin yadda yake da hikimar fitar da magana da bakin shi,se ki zata gaskiya yake fada,Amman a karshe Kinga yadda rayuwa ta ta koma,nifa asalina ni yar gata ce Zahra,su daddy na ji dani sosai,haka na taso ban San Babu ba se da na auri Baban ku komai ya sauya mun,ji yadda muka koma a rayuwa Zahra ba Wanda zece nice,ban taba auno cewa zan taba iya cin karo da irin wannan Sauyin rayuwar ba ko a mugun mafarki na.

Nayi makarantar da take top 5 a garin nan,tun lokacin duniya na kwance.

nazo naje university a level 3 Baban ku ya katse mun karatu na ya hanani koma wa.

A yau da nayi karatun na da ba zamu tagayyara ba,ko Yaya se na zama Wani abun.

I had my dreams a rayuwa,Amman yadda duk na tsara ba haka ya kasance ba.dama Kuma tsarin Allah shine dai dai.

Ko a haka Ina Gode wa Allah da irin rayuwar da na tsinci kaina a ciki...

Zahra ki guji dadin bakin da namiji,kar ki kuskura dadin soyayya ya rufe miki ido ki fada irin wannan rayuwar mara yanci da galihu. Làllai ki kula Kuma ki iya boye soyayyar namiji a ranki,ya kasa gane kina son shi ko bakya son shi,kar kizo kina rawar jiki ki zubda ajinki a gun namiji ko wanene ..

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now