SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(38)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________💕✨💕✨
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Fita sukai daga dakin suna tafiya a jere gwanin sha'awa,matsalar dai guda daya ita ce ,yafi ta tsayi sosai,sannan tsayin nashi yana tafe ne da jiki kamar yadda na gaya muku.
Ita kuwa bata da jiki,sannan ba doguwa bace chan sosai,tsayin ta dai yafi kama da na yan shekara 16 ba 19 ba.
Lab din da za'a dauki jinin nata suka wuce .da yake da Dr taje,ba maganar bata lokaci ,yo wama yake da Wani lokacin bata wa?.kan ace komai har an dauki nata,se Shima yasa a dau nasa a musu gwajin tare.
Cike da tsoro suka baro lab din,kusan ma shi Sufyan din shine me tsoron dan ita kam ma bata gama sanin karatun genotype da consequences din sa ba har yanzu..
Memakon su dawo dakin se ya zagaya da ita a cikin asibitin sannu a hankali suke tafiyar su cikin yaren na kurame ..se fa sakon zuciyoyin su da suke ta karakaina wajen ganin sun aikawa juna a tsakanin zuciyoyin nasu..
Wani kallo ne suke yi lokaci zuwa lokaci me kayatar wa da tsada,irin shaharraren kallon soyayya Wanda ke sake tabbatar wa da masu kallon su wallahi Hira ce suke da zuciyoyin su ..
✨💕✨💕✨💕
Kwanan mama uku a asibitin kafin a sallame ta da gargadin cewa ta cire damuwar da duk ta Sanya a ranta ko ba dan komi ba,domin lafiyar ta.
Dan komai na rayuwa mukaddari ne daga Allah ..
kar ma taje ta sa wa kanta wani mugun ciwo a banza a wofi su zahra su shigangade..
Sannan Kuma duk tsanani yana tare ne da sauki,se dai kuma me hakuri,ko nace kalilan daga cikin Al'umma,su ke iya gane hakan.
✨💞✨💞
A ranar da aka sallame su suka wuce gida,Sufyan ne ma ya kaisu da kan shi,mama se nan nan take yi dashi kamar Wani kwai ko dalar amurka me matsayin dala billion daya da million tara da dubu dari biyu da da tamanin da bakwai da naira chasa'in da hudu da digo biyu..
😂 Ku lissafa mana muga nawa ze kama ..ni ba ruwana
✨💞
Su Zahra dai Yan kallo kawai suka zama ita da Abul baki bude suke kallon mama yadda ta maida su gefe kamar irin kwanannan tuwon biskin nan,Kun San baya da farin jini ko kadan.
Soyayyar Sufyan din ce taaa shiga zuciyar mama har bata san garin Yaya ba.
Wato Sufyan yaro ne me tarbiyya da sanin ya kamata da kimar mutane da Kuma darajta Dan adam.
Ku jifa yadda duk ya kasa zaune ya kasa kwance akan maman bata da lafiya se kace uwar sa ce mahaifiya a kwance ba uwar Zahran ba.
Amman saboda sanin kimar Babba,da darajta soyayyar dake tsakanin su da Zahra, kun ga doke ya tsaya Kai da fata dan yin abun da ya kamata,ya ruga ya dauki mama Abida a matsayin uwa ce , shiyasa ya kula da ita iya karfin sa.
sannan Kuma kamar yadda ko maman tashi ce hakan dai ze yi domin kula da ita ..
✨💞
Kai mama kam wannan lamari ya dada ta da kasa .
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
Художественная прозаlabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...