(18)

49 6 0
                                        

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(18)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Yau Hashim be dade a waje ba Dan kafin ayi sallar isha'i ya dawo.

Jin shirun na Abul yayi yawa yasa Abida ta fito Neman shi.

Daga dan nesa ta hango shi ga Kuma duhun dare,se dai Hakan be Hana ta gane cewa Abul Khair din ta bane .

Cikin Wani yanayi ta gano shi Wanda yayi sanadiyar sa zuciyar ta yin Wani irin mugun bugu,yayin da tsoro ya kamata cikin ta Kuma ya duri ruwa.

Sannu a hankali yake tahowa cikin buguwa,kaduwa da maye,kallon farko zaka mai ka fuskanci cewa yana cikin tsananin rikitar hankali duk kuwa da cewa ba magana yake ba .Amman da ganin yadda yake yi za'a iya yanke Mai hukunci kamar baya da hankali,lafiya ko Kuma dai a maye yake .

Wato ba sauri ba da gudu Abida ta Isa gare shi ta ruko shi,ziiiiii haka ta runga Jan hannun shi har suka shiga gida ..

A ranta tana Allah Allah kar Uban masifa ya gansu har ta Kai Abul dakin shi.

Amman suna Sako kafa gate din gidan tunda da hasken Kwan fitilar lantarki a kunne suka ga Baban Abul din,da alama ma ita yake nema,ko yana neman Wani abun da ze sa ya sake kare mata tanaji.

Gaban ta ya sake bugawa dama tun daga waje take kwallar tausayin Kai,jarabawa Allah ya jarrabe ta da shi,se dai fatan Allah ya bata iKon cinye wannan kalar jarabawar.

Kokarin tsayar da Abul take yi dan a Dan boye Wani abun.amman Abul ya kasa tsayuwa ...

Da Baban Abul ya bugo Wani salati se Kun zata irin mace aka kama tayi cikin wofi.

Har Yana tafa hannu kamar Wani mace .

Me nake gani haka?
Dan tabbas abun ya taba shi,naga ko Dabba dai zata so ace Dan ta baya rashin hankali matukar tana da hankali.

Balle Baban Abul da na San ba wai hankali ne bayada ba,zunzurutun iya hege ne kawai..

"Abul shaye shaye kake yi Daman?"

Ya fada yana matsawa kusa da Abul din ,basu Ankara ba sukaji Shauu ya zabga wa Abul mari..

Ya sake daga hannu Maman Abul ta janye Abul hannun shi ya bugi iska ..

Jan hannun Abul tayi ta kaishi daki cikin raunin zuciya,ruhi da ta rayuwa.

Kwanciya yayi Yana kallon ta kamar Wani mahaukaci,se Kuma ya fara hawaye ,wannan alamun suka nuna mata Abul be idasa tafiya ba,Dan tayi imanin wannan ba wai rana dubu bace ta barawo.

Ah ah wannan rana Daya ce ,Dan tana da tabbas akan yau Abul dinta ya taba shaye shaye.kuma ta sake imanin cewa Allah ne yaso ta da har ta gane a ranar farko Kuma bi'iznillahi na karshe kenan .

Bama haka ba a yau kam Bata sake kwana cikin gidan nan saboda iyakar hakurin da zata iya kenan.

Gashi sanadiyar bakin cikin Baban Abul yana so ya lalata mata tarbiyyar Yaran ta da yi sacrificing a lot a Kai ta Basu.

Se kawai a cikin mutane ma a rasa Wanda ze lalata mata su se Uban su saboda baya da mutumci?

Sallar isha tayi sannan ta nufi dakin Abul ta tarar yana bacci..

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now