SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(46)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________💕✨💕✨
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Bayan tafiyar Sufyan se mama ta zaunar da Zahra tana ta bata baki tare da bayanai akan yanayin aikin likitoci daman se anyi hakuri..
Tace .. "Sufyanu mutum ne mai gaskiya da amana Zahra,ke da ya kira abokin sa ma a gaban ki dan kiji gaskiyar zance ki gasgata gaskiyar sa,ba kowa bane ze iya wannan ba Zahra,bana so ki daukar wa kanki rayuwar da zata kaiki ga Shan wahala da hannun ki,a wannan duniyar ta yanzu ba'a zafafawa a kan komai,ke shaida ce a kan idanun ku nayi irin rayuwar da nayi a gidan ubanku.
Ba irin son da be nuna mun ba,nima kuma haka,amman haka be tseratar dani daga cin zarafin sa ba
Kina so ki maimaita abun da ya faru dani a baya ne?, memakon tunda kin gani a kaina da rayuwa ta ki kuka ki samu sauyi, se kike kokarin yin wa namiji mugun son da ka iya janwo koma bayan ki?
Ni bance kar ki so shi ba,ki so shi,so dan Allah ma,amman Kuma ki sani, komai akwai limitations a rayuwa,so se kin kula gaskiya..
sannan ma kina ji abokin nasa da ya kira yana duba wata mata kuma sarai kina jin me yake faruwa ko,toh Kinga kenan wannan ba abun damuwa bane ba a gunki tunda ba abun rashin dai dai suke ba, yanayin aiki ne haka"
Chuno baki tayi kafin tace "ni wallahi mama duk na manta da wannan irin aikin nashi ma,da bazan yadda ba wallahi mama"
Cike da mamakin yadda Zahra keta cika tana batse wa wai ita kishi ya sa Maman cewa..
"zaki iya ganin mata na Kiran shi ma ko a waya saboda likita ne,haka Kuma zai ta duba su matukar sun zo asibitin basu da lafiya Gwamma ki kwan da sanin haka.
sannan a dazun da kuke waya yace miki yana zuwa ,in da kin yadda kin ajiye wayar duk da hakan zata faru ne zahra,nace zata faru ne,za kiji abunda ze daga miki hankali? Ina ranar musu,shin yanzu wa gari ya waya kenan?"
Hawaye aka goge sannan aka ce ..
"nikam mama bazan iya ba gaskiya,na fasa auren gaba daya ma"
Sake da baki mama ta Kalli Zahran, tsananin mamakin sabon halin na Zahra Wanda ba ko shakka soyayya ta koya mata shi,ma kasa yin kyakkyawan motsi maman tayi tsabar mamaki..
Rufe bakin ta da ta bude tsabar mamaki tayi tana cewa ..
"yayi miki kyau..dadi ne yayi miki yawa Zahra ,ai ko ba domin aiki ba Sufyanu mijin mata hudu ne ,gwamma ki ma kwana da sanin hakan"
Wani irin mugun duka maganar maman tawa Zahra,cewa tayi ..
"Allah ya sawwake,wallahi mama bazan iya ba,kirjina kamar an dafe mun shi haka nake ji fa mama"
ko ban fada ba muku ba Kun san Zahra kuka take yi..
✨💞Allah sarki rayuwa,toh fa girma na kokarin kama Zahra ga Wani rigimar na kokarin tunkaro ta..kishi? Irin wannan,a wannan duniyar ta wannan zamanin ? A soyayyar yanzu? Wahala kenan 😂
Toh malama Zahra bari a baki gu ki huta ko?...ma zagayo Muji me ake ciki daga baya
✨💞✨💞✨💞

YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
General Fictionlabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...