SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(51)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________💕✨💕✨
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Da sallama Zahra ta shigo gidan ba kowa a tsakar gidan ta San suna daki tunda yanayin sanyi ake ciki..
Dakin taje ta Sanar da mama Zuwan Sufyan din a waje,cewa Mama tayi "je kice ya shigo mana,se kace Wani bako?"
Zugui zugui Zarah ta wuce waje dan shigo da sahibin nata da take fushi da shi..
Cewa Akai "Yaya ka shigo ciki wai inji mama"
A tare suka shigo har an wa Sufyan shimfidar zama ma,nan ya zauna suka gaisa da Mama bayan nan aka gabatar mai da abincin dare ..
Bayan yaci ne yake wa Maman maganar makarantar Zahra.yajr cewa "Mama Ina son Fatima ta fara karatu gaskiya saboda Yana da amfani sosai,kar in biye nata dan tace bata son tayi in Kyale ta,nazo daga baya abun ya dame ni"
Numfasawa maman tayi kafin tace "toh wannan ma shawara ce me kyau,nima zan fi so tayi karatun gaskiya,saboda yadda nawa karatun ya Sha ruwa bana son nayi wasa da karatun Yaran nan"
Kallon ta yayi da tausayi na yadda yaga rauni da Karaya karara a tattare da ita.
Cewa yayi "in Sha Allah kuwa za suyi karatu me zurfi mama,har se sun gaji "
Ya sake cewa "Mama Nabila ma da an maida ta boarding school,rannan ake maganar su ilham (yayan yar su) zata tafi boarding se nake Sha"awar wa Nabila ita"
Cewa mama tayi "Hakan ma Yana da kyau Dr,se dai fa tarbiyyar Yaran yanzu ko a gaban ka ma se a hankali balle boarding school,ban kama wannan ba "
Cewa yayi "toh shekenan mama in shaa Allah yadda kike so haka za'ai,Amman Mama fa da Nabila zamu tafi mu barki da Yan biyun ki " ya fada yana murmushi ..
Murmushin tayi ita ma kafin tace lallai abun naku son Kai ne,Amman ba komi Allah ya Kaimu,in ta yadda fa Amman,ba Wanda zewa yata dole,taje ta maida mun ya agogo..
Dariya yayi kafin yace "Kai mama son Kai fa ba kyau "
Dariyar tayi itama .yayin Kuma da wayar sa ta kada ta katse masa maganar sa ..
Ganin call din hajiya Mama ne se ya dauka da wuri Yana cewa "Maman Dr Sufyanu .."
Da yake ta amsa masa da "sannun ka Dr'n mama,kana Ina ne ?"
Kallon mama yayi kafin yace "Ina gidan su Fatima mama,lafiya dai"
"Hmm Maza kazo gida yanzu Baba Sarki ne, Allah yayi masa rasuwa" ta kashe wayar
Salati ya fara yi gaba daya ya rude se innalillahi yake ta maimaita wa..
Maman ke tambayar sa me ya faru,nan ya gaya mata cewa mahaifin Baban sa ne ya rasu,wato Sarkin kuzoma garin su..
Cike da Alhini mama ta jajanta masa ta masa gaisuwa ,sallama ya mata ya kama hanyar gidan su.
Yana shiga motoci biyu na shigowa a bayan sa ..
A daddaren ranar iyalan gidan Alhaji Badamasi Dan sarki suka kama hanyar tafiya garin Kuzoma cike da tashin hankali..
Basu Isa ba se kusan karfe daya na dare,koke koke ne ake ta faman yi gidan kamar ba dare ba,ko da Yake,daman ita masarauta ai ba dare ba Safiya a cikin ta,ko yaushe hidindimu ne ake ta faman yinsu kullum da ko da yaushe .
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
General Fictionlabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...