(48)

66 5 0
                                        

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(48)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

💕✨💕✨

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Kofar dakin ta bude,sannan ta debi takalman ta ta ruke a hannu,tayi Shirin guduwa da ta gama abun da zatayi zata fece..

Yana kallon ta ta kasan ido har tana tattare riga yadda zata fi jin dadin gudun nata..

A ranshi yace "a Ina,gudu da aure na? No way!"

Bedai bude ba se tace "toh haaa"

Se yayi haa din kuwa cike da garaje da sauri ta nufi bakin shi tana kallon kofar da zata bi ta gudu..

Yatsan ta daya ta saka ta shafo saliva in shi ta mayar baki ta shanye ta juya da gudu zata tsere taji ya ruko ta ...

"Innalillahi " tace

Wanda Hakan da ta fada ne ya sa ya fara wata irin dariya , dariya yake yi sosai na yadda wai yar Zarah zata mai wayo,yar tatsitsiyar yarinya irin wannan da ita,hmm.

"Ina zaki gudu kije?" Ya fada yana dariyar still har Yana kwalla tsabar dariyar da yake yi..
.rufe ido tayi tana cewa..

"wallahi na sha ai dai ka gani ko?"

"Na gani mana ,toh amman in Kika fita a haka ba takalmi gashi kin tattare riga kina niyar gudu mutane na kallon ki fa?,Ina Zaki da wannan Shirin?"

"Gida" ta fada tana rufe fuskar ta

"Ai duk wacce ta shigo nan dakin bata fita ai,a nan zaki kwana mun yau nima"

Ido ta budo tare da cewa "laaa"

Kallon ta yake Yana cewa"laaa me?"

Wani irin tafiyar tsutsa ya fara mata a hannu kafin ya ce mata "just a minute "

Fita yayi ya debo tarkaccen su daga mota.

Zama yayi a kasa Yana cewa "Zauna Fatima"

Ba musu ta zauna ya bude pizza din nan ya Yagi daya ya gutsura sannan yace mata "Haa"

Bude bakin tayi a nutse ya sanya mata pizza ta gutsira..

Ci ya sake yi sannan ya sake Bata,se tace "Dan Allah zan ci da kai na"

"Bismillah" yace mata

Nan suka ci suka Sha suka koshi kan nan yace ta hau kan gado ta kwanta zeje gun su Hajiya mama ya dawo..

Tana kallo ya juya ya fita daga dakin Wani bala'in burge ta yake yi ,wallahi tsabar soyayya kamar ta dauke shi ta dulmiya shi a cikin zuciyar ta ko ta huta ..

Ajiyar zuciya tayi kafin ta tattare kayan kwalin pizzan da suka gama ci ta ajje su gefe, sannan ta kwashe kayayyakin kan gadon da na kasa ta zuba masu datti a kayan wanki,ta lunke wasu ta Sanya su a gefen wato one seater dake dakin..

Zama tayi tana jiran shi ,se ta dau wayar ta ta fara yin game da ita. .

💕✨💕✨

A cikin gida yana shiga sauran mutanen da suka rage na biki suka runga tsokanar sa suna hada masa da Allah ya Sanya alheri.

Ba ko kunya Sufyan ya runga amshe wa Yana murmushi yana Sosa keya..

Da yake ma ba mutane da yawa ,duk gaba daya Yan uwan Alhajin su ne ba wasu ba..yayyun sa ne duk su uku Wanda zasu wuce a gobe ..

SAUYIN RAYUWA ✅Stories to obsess over. Discover now