(26)

65 4 0
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(26)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

"ai wai Sufyan ne ya ganta ya mata magana,shine fa tayi watsi da kayan ta gudu ,ya damu ne yana zatan ko Wani abu ne ya sameta..."

Maman Abul ta juya ta Kalli queen dake zaune tana ta share kwallar dake silalo wa daga kyawawan idanun ta,se ka rantse laifi aka yi mata.

Cewa Maman Abul tayi"Ai lallai, daman queen dan an yi miki magana shine kika zubda abinci a kasa,abinci fa saboda sakarci kenan komi,shi Wanda ya Miki maganar dodo ne shi ?" Kwafa tayi .

A waya Kuma tace "shiririta ne wallahi da sakarci kawai,ni fa nan na zata Wani abu ne ya biyota ko Wani abun cutarwa.har Ina taya wa da danne kofa"

Dariya suke dukkan su,banda queen dake zaune ta chuno bakin nan malam.ita a dole me yasa wannan mutumin ya mata magana,ya Bata tsoro.

Bayanin kayan da Hajiya mama take mata ne a waya ya dauke su dan time kafin sukai sallama.

Da kallo Maman tabi Queen wadda har a lokacin take share kwallar ta.

Cewa Maman tayi" yanzu dama abunda kikayi kenan Zahra? Daga an Miki magana se kiyi watsi da kayan hannun ki harda abinci Zahra,abinci fa? Gaskiya Baki kyauta ba Kuma kar na sake Jin Hakan.

Duk Wanda yayi Miki magana in dai a cikin gidan nan ne ai kinsan yanada alaka da gidan ko?

Daga Kai tayi tana Wani shagwabe fuska saboda maman ta dan sassauta fadan nata..

Se tace "Mama fa kawai Ina tafiya ta ban San da Wani ba agun naji ance mun ke zo nan,gashi da na juya na ganshi Wani katoto ,shine fa na gudo abina " ta fada tana sake turo bakin.

Ita maman Abul ma abun Haushi yake bata da dariya.

Da yake bata taba ganin Dr Sufyan ba ma ita Maman Abul,sanda ya dawo ta bar zuwa gidan daman.

Amman ai kafin tafiyar Yayan Yara school yana ce mata oga Sufyan kaza oga Sufyan kaza.ta San shi a Baki ta Kuma San yanayin kirkin shi.

Cewa Maman tayi "toh iya kuka,kukan zakici ko dambu?"

Aka Wani jujjuya ido aka ce "Kai mama ,Gwamma inci dambu tunda dai ba'a cin kuka "

Dariya suke dukkan su gwanin sha'awa,sannan maman ta zubo musu dambun suka ci suka koshi suna dan taba Hira.

Kusan hiran kayan da suka samu ne daga gun Hajiya maman tana ta gaya wa Maman su "harda sabbin dinkuna wai ta dade Bata Saka su ba shine tace a kawo miki su ,Kinga kayan kuwa Mama,Kai maasha Allah.

✨💕✨💕

Dr Sufyan ne zaune bayan Mama ta gama wayar da suke da Maman Abul wato iya Abida,se yake ce mata ...

"Mama wai ita din wace ce ne ?"

Se mama tace "kanwar Abulkhairi ce fa diyar iya Abida ce,ita ke bi mishi.."

Kada Kai yake alamun gamsuwa da abunda yaji.

Se yace " Kuma me tazo yi nan gidan ?"

Mama tace " aiki na kira tazo ta tayi "

Ya sake cewa "okay ,Kuma shekarun ta nawa ne?"

Cewa Mama tayi "Eh toh, gaskiya ban San exact shekarun ta ba ni"

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now