59 (tarewan queen)

56 5 0
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(59)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

💕✨💕✨

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

A bangaren su Mallam Hashim ma jinya na nan bata ragu ba se karuwa ma da tayi ..

Sannan Sakinatu tabi hatta Yan uwan shi ta gaya musu cewa ya tafi Niger baya Nan saboda ma kar su cigaba da mata sintiri a gida ana Saka ta yaken karya da kula da Hashim din..

Koda suka tambayi ba'asi se tace "magani yaje yi,Kuma ita ma yace ta ma ta tafi gidan su zuwa sanda ze dawo din"

Da wannan ta yaudare su suka dauka cewa gaskiya ta fada musu duk da sunyi mamakin tafiyar tashi ba sallama..

Amman ganin cewa matar shi ce ta fada da kan ta se sukai Mai fatan dacewa da samun lafiya.sannan sun San halin shi tsaf wannan kadan daga ayyukan da Hashim din ze iya ne..

A haka yake ta rayuwa a cikin gidan,ba kula ba kulawa ta yi kutun kutun ta hana shi yancin shi..

Tun yana tuno rayuwar shi ta da yana kuka Yana fatan ganin tsoffin mata sa ya neme su gafara,musamman Abida,har ya hakura ya zuba mata idanuwa ya dukufa istighfari Dan ya fuskanci ita ce rayuwa ..

✨💞✨💞✨💞

Ta gefen Soffy da iyayen ta Suma suna chan A Abuja suna rayuwar su,ita tana aikin ta,mommy Kuma ta koma islamiyya sannan ta kama Business din ta dan ta bude car wash kerarre a unguwar Apo dake Nan cikin birnin Abuja..

Rayuwa nata tafiya a hankali,wasu tana musu dadi,wasu kuwa se godiyar Allah..

Abu daya ne wanda musulmi zeyi,ko wani irin sauyi ko yanayi na rayuwa ka samu kan kan,se kace Alhamdulillah...se Allah ya duba ka ..

Allah kasa mu dace ..

💞✨💞✨💞✨

Yan makaranta ma suna ta faman kokarin round up,Wato Aminatu da Saudatu,Kuma Alhamdulillah,ko waccen su tayi kokarin ta matuka sun bawa mara da hatta masu dan ma kunya..

Kamar yadda yake a rayuwa tsarin Allah shine tsarin,ba na mutum ba..

Se kawai Suma zaman su ya Kara tsayi,sukai har masters din su sannan suka fara doctorate degree din su..

Dalilin kenan da ya Sanya basu iya dawowa ba suka cigaba da karatun su...

Ba kamar yadda har sun fara packing kayayyakin su don tahowa gida ba..

Se kwance kaya sukai Wanda shine tsarin Allah..damuwar Saudatu Daman maman ta da Yan uwanta,Amman da yake kullun sun kan waya se ta samu nutsuwa..

Sannan maman ta gaya mata Sufyanu yace zasu tafi da ita da queen su Gani Saudatu,shekenan nutsuwa ta samu

Se fatan Allah ya basu sa'a

💞✨💞✨

Tsaye yake kikam a gaban queen ,yayin da yake yi mata wani irin sanyayyen kallo zuciyar shi fal bege...

Mutsu mutsu ta fara yi tsabar yadda kallon nashi ya ke zuba mata dafi a dukkanin sassan jikin ta..

Daga hannayen sa yayi sama Yana sake Gode wa Allah da ya tabbatar masa da wannan alkhairin ,yau ga queen a gidan shi an mai handing over ta zama tashi se yadda yayi da ita..

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now