(21)

64 6 0
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(21)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Wai shin Ina Alhaji Hashim yake?

Bayan Abida ta bar office din Alkali Ibrahim Ibrahim,sosai Alkali ya wa Hashim fada akan yadda yayi wasarairai akan harkar iyalin shi.

Kuma ya gaya masa yadda rayuwa take ba yadda ya dauke ta bane,tare da bashi shawarar zuwa yayi ta istighfar saboda ya samu ya rabauta ko Yaya ne ..

Bayan ya koma gida ,gidan yayi Mai shiru sannan ya Mai girma,yana so yayi masifa ma ya rasa da wa zeyi,haka ya runga fadan shi da bokiti da kofofin  gidan Hadi da tukwane tunda yin fadan ya zamar masa kamar dole ne se yayi shi.

A haka rayuwa take ta dan tafiya dashi ba tare da yaso ba.kuma ko a wasa be fadi wa kowa ba cewa sun rabu da Abida ba.

Dama Hajiyar su Hashim ta Dade da gane cewa dan ta Hashim shi ne da Kansa ya Hana matar shi da Yaran shi zuwa gidan su.duk da irin kokarin da Abidan keyi na boye Hakan tana daura wa kanta laifi.

Da takan aika aje a gano mata su dan ta San halin Dan ta,gashi ba irin nasihar da bata Mai akan iyalin shi ko dan gudun hakkin su da hakkin Allah Amman inaa idon shi ya rufe baya ji baya gani..

Da ya Hana su zuwa.se ita ma ta daina sawa aje a gano su,ita ma da takan leka musu se ta Kyale su ta Daina.

Mata dai tashi ce ,Yara ma nashi,hakkin ma nashi ne na komai da ya shafe su,in ya ga dama ya gyara toh .ta dai bar zuwa gidan shi.

So yanzu Hashim be cewa kowa sun rabu da Abida ba.

domin ba me sani tunda shi kusan ko yaushe yana gidan su,masu zuwa Kuma sun Daina zuwa mai,se sakon gaisuwa kawai take aika musu.ya amshe yace za suji

Se Kuma Abida da Bata taba kin Kiran ita hajiya ba a duk juma'ar duniya ta gaishe ta.kamar dai yadda ta Saba.

amsar dai Daya ce a duk tambayar da zakai wa Abida,ita ce "Muna Lafiya" in aka ce ba wata matsala ko se tace "Babu ko Daya..se dai Wanda suka ga dama se su mata abunda sukai niyya.amman Dan Abida Bata furtawa.

Ai ko labarin halin da gidan Hashim ke ciki,masu zuwa ke jewa su fadi wa haajiyar su  abunda suka gani,amman Abida ko a wasa Bata taba fada ba.

Da yake Allah Me Adalci Ne se Yasa Yan uwan shi da kansu suka Kai rahoton yadda gidan yake tafiya gun hajiya.

Ko da Hajiya ta kira shi tayi ta fada da nasiha, daga haka se ya dau aniyar Hana su Abida zuwa gidan Hajiya tunda se mutum naje maka zaka zo mai.

baze Yu Kai ta zuwa gun Wani ba shi baya zuwa maka.

Da wannan hikimar Hashim ya raba hajiya da Abida se dai a waya suke gaisawa.se Kuma Sallah ko Babba ko Karama yana bar su suje.

Se Kuma jaje Shima se Wanda ya zamo dolen dole take zuwa,amman dama su suna ko biki duk baya barta taje.ko na nata dangin Kuma ko na nasu.

Toh ko a bayan rabuwar da Abida tayi da Hashim duk juma'ah take Kiran Hajiya su gaisa da jikokin ta.

Ita Abida tayi zaton hajiya ta sani,hasali ma dan kar Hajiyar tace dan ta rabu da Hashim din ta ne yasa ta daina Kiran ta ta gaishe ta.

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now