SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(29)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨A kofar gidan su,se dai Yana fitowa daga mota tana dannowa waje da gudu Nabila ba biye a bayan ta ..
Ganin farko da yayi mata ya shaida ta,a ransa yace "Sarauniyar gudu kenan" no wonder ,chafko rigar ta yayi ya tsayar da ita daga gudun da take yi ..
Ta firgita iya firgita,Amman kallo daya ta mai ta gane shi ne wannan katoton da ta gani..
Nabila ya kalla ita ma se yace mata "zo nan ,me ya same ku kuke wannan gudun,Ina zaku ?"
Ba tare da ta San shi ba fa ,Amman se tace "Kunama ne ya hau kan kafar Adda ,shine muka gudo.."
Yana ruke da hannun gefen rigar dai na Zahra,Dan alamu na nuna in ya cika ta zata iya Dina da gudu ne,Dan still tana Jin abun kunamar kamar yana mata yawo a kafar tata..
Kallon Nabila ya sake yace "Kuna ma Kuma,Ina Iya Abida?"
Kallon sa sukai da tunanin Ashe ma ya San maman su.
Se Nabila tace "Bata nan ta fita"
Cewa yayi "toh muje ciki a kashe kunaman kar suyi Wani gun Kuma "
Nabila ce ta fara juya wa ciki,se shi da ya danna wa motar sa remote yayi locking din ta,Jan Zahran yayi cikin gidan tana ta nokewa tana tsoron shiga
Yan biyu na zaune suna yin wasan su hankali fa kwance kamar ba su San me ya faru ba..
Da sallamar sa ya shigo yana tambayar ta Ina ne kunaman,dan be ci ace har sun gudu ba a gansu ba..
Abun ya bashi mamaki sosai ganin su Asif zaune suna wasa..
Suna ganin shi suka gaishe shi,amsa musu yayi Suma kamar ya San su.
Kun San in kana son yarinya har akuyar gidan kana so in akwai ta,so nan take yaji kaunar Yan biyu sun kama shi..
So se yace "me sunan ku,Ina kunaman take?"
Seda suka Kalli juna se suka ce "Ba wani kunama"
Nabila ce tace "oh karya muke muku kenan ko?"
Ita dai Adda baki ya mutu murus..
Nabilan ce tace "Baba kaga,kwaffi sukai wa Adda na kunama wallahi har biyu,Kuma ta Dora ruwa zata dama mun Koko Amman ruwan yaki yi,shine Dan tayi musu magana se muka ga kunama a kan wannan kafan"
Nuna Mai kafan tayi ya kalla ,Zara Zara yatsun kafar kawai se da ya tafi da imanin shi..
Hannun ta ya kalla da yake gefen jikin rigar shi ya Sha Jan lallen da ko bushes wa be yi ba,ya ma gama shafuwa akan yadin da yake jikin shi cream color me kyau da tsada ..
Kallon ta yayi se yace "Zahra,me ya hada ku da twins?"
Ai yana magana kawai se ga hawaye sharrrr na zuba daga idanun ta ..
Abun ma mamaki ya bashi sosai da sosai ya saki Baki kamar Wani sakarai Yana kallon ta..
Sallamar Maman su ce ta dawo da hankalin kowa kan ta..
Tun daga kan Zahran har kasa suka nufe da sauri suka fada jikin ta,kamar wadda ta Wani shekara bata nan.
Kallon fuskar Sufyan take yi na rashin sani,se Kuma mamakin abunda ya shigo da garjejen katon nan har cikin gidan ta..
YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
General Fictionlabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...