SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)
BY
UMMKULTHUM AHMAD
AKA AUNTY DIVAA
(58)
Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries0308165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________💕✨💕✨
✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨Washegari da suka tashi ma Wani shagalin aka dora zuwa yamma ,kowa ka gani ana ta haya haya ana son barka zuciyoyi sun wasai..
Bakunan da yawa sun ki rufuwa ,yayin da wasu bakin ciki yake nema yayi ajalin su...
Wannan dalilin yasa Sarki me rangwangwan be ga Sarauniyar zuciyar shi Fatima ba,..
Hakan Kuma yayi sanadiyar kasa tsayar da hankalin sa guri guda a wajen shagalin na budar ido na sabuwar Sarauta na sabon Sarki..
Ita kuwa tana chan da Mama suna waya da Abulkhairi..
Inda yake shaida musu nasarar da ya samu a karatun da yake yi,Wanda yanzu saura kiris ya rage masa ya kammala..
Don ba daga farko ya faro ba, courses ya amsa gaba daya Wanda zeyi ya cikashe shekara ukun sa da ya faro a Nigeria ..
In no time ya karance su tas tas ya fahimci komai tunda photographic memory gare shi..
Se da an ka zo yin exams ma se shi yace bazeyi a lokacin ba,se gaba ze hada gaba dayan courses din ya yi exams a wuce gun..
Mr merkus da suke maganar da Abulkhairi abun se ya bashi dariya sosai yana mamakin yadda Hakan zata yiyu ma,ace kamar keru, Nigerian yazo yayi exams na courses almost 20 a lokaci Daya?..
Yeah it's allowed student ya shigo zeyi exams in yaga question din ya ga baze iya yin su ba,yace ya fasa se next day or week ze dawo yayi..
At this point I'm talking about developed countries ne fa,ba a Nigeria ba,a nan kasar dai yadda aka damo ta haka ake Shan ta ..
Shi Mr merkus be taba ji ko ganin student din da yayi kundumbala ba irin ta keru..
Heads on kace zakayi exams na courses kusan 20 a rana Daya?
Tabbas Mr merkus ya Sha dariya,Amman tunda Hakan Keru ya zaba kamar yadda suke Kiran shi da shi,se Mr merkus yayi respecting wannan decision din yace it's his choice...
Mutumin ku Abul se ya samu damar yin yawon shi a kasar engila, kamar Wanda yaci kafar kare..
Binini binini ya fice kullun baya nan,yayi amfani da damar sa ne yayi yawon gurare matuka gaya yaga gari yayi exploring da kyau da kyau,ya I abincincina mabanbanta...
Tunanin shi,wannan ma a scholarship yazo,ya sani ko zai dawo ,in da ma ace kwankwaso yaci zaben kasar nan da se ya sa ran sake komawa yin karatun a wata kasar a wani scholarship din,duk da Yana fatan sake samun damarmaki manya na rayuwa..
Amman yanzu ma ana fatan Alkhairi ga wanda yaci...
Se da ya gama exploring sannan ya koma ya nutsu ya Sha karatu yayi exams,exams din da ya lashe ko wacce ba tare da ya rage ko daya ba a cikin courses din...
Nasarar da ta sanya yayi Wani irin tambari na shahara a cikin makarantar tasu...
Mr merkus kan sa ya kasa barin Keru ya huta tsabar yadda ya shayar dasu kindirmon mamaki..
A karshe Keru guduwa ya fara yi saboda yadda kowa ke zuwa kallon sa,abun ku da jajayen kunnuwa,Basu iya hassada ba da bakin ciki, congratulations ne Keru ya amsa ta Fi miliyan,masu flowers ne, chocolate ne, invite ne date duk suna yi..

YOU ARE READING
SAUYIN RAYUWA ✅
General Fictionlabari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yaga kamar shi kadai aka tsana,ko kuwa ya mance da rahamar Allah a gare shi,da jarabawar da Allah yayi Alkawarin jarabtar bayin Sa masu imani.s...