SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(53)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

💕✨💕✨

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Bari mu leko Alhaji Aabid Muji yadda yake ko ba haka ba?

Kamar yadda alkawarin aure yake a tsakanin  Aisha da Alhaji Aabid dai rana ta kusan zuwa ga ango yana ta faman fama  da jinyar zuciyar shi...

Abubuwa sun hadu sun rinchabe masa ,ya rasa yadda zeyi da rayuwar sa..

Ga yadda maman sa tayi fushi da shi abun yana  matukar damun sa..

Saura kwana uku a daura auren nasu da Aisha,har a lokacin be taba Sanya ta a idon sa ba,Kai ko a wasa be San kalar ta ba,ko fara ce,ko baka ce me jiki,siririya..Kai koma a ya take be sani ba..

Gashi har yanzu yana asibiti Yana fama..

Ko ya wannan al'amari ze kasance oho ..

Rana bata karya se dai uwar diya taji kunya,a safiyar ranar da aka daura auren Alhaji Aabid da ya kasance magashiyan a gadon asibiti daruruwan mutane sun shaida wannan aure me Albarka..

A yayin da da yawa suke farin cikin wannan daurin auren,shi kuwa ango be San ma a wani yanayin yake ciki ba,domin dai aure ne Wanda aka daura bada masoyiyar shi ba,toh taya ze iya farin ciki?

Addu'a daya yayi akan Allah ya zaunar da su lafiya ko domin girma da darajar tsohuwar mahaifiyar shi..

Sanya Alhaji Aabid yake cikin manyan kaya na shadda me laushi kalar black wadda ta fidda kwarjinin shi ta Mai kyau matuka baya ga irin ramar da yayi Amman duk da haka gwanin ban sha'awa yayi..

Maman shi dai ita ta shirya shi saboda za'a kawo amaryar sa nan su gaisa anytime from now..

Nasiha maman shi ta fara masa me ratsa jiki,tana me cewa "Naufal,Dan Allah Dan Annabin Allah,ka saurareni kaji me zan gaya maka ,ka Kuma daure kayi amfani da abubuwan da zan gaya maka domin Ina da yakinin cewa ba zan gaya maka abun da zan cuce ka ba ,Dan Allah kayi hakuri ka daure ka maida komai ba komai ba,ka ruke amanar Allah ka samu ka sauke hakkokin da suka ruga suka rataya a kan ka,kaji tausayin yarinyar nan,kaji kunyar iyayen ta,kaji kunyar kunyatani,kaji kunyar Allah,ka ruke ta da kima..

A wannan karon ya kamata ka ka ba mara da kunya ka zauna kayi ibadar auren ka yadda Allah ya hukunta maka, yarinya ce karama ta yadda ta aureka da tsufan ka da komai..

Dan Allah kar ka cutar da ita ka ruqe ta Amana.

Kayi kokarin binne duk wata tsohuwar soyayyar Abida a ranka,chan kadan ranka ,ka manta da ita ,Kai facing din rayuwar ka kaima ko Allah ya bani iKon ganin jika na kafin kasa ta rufe mun idanu,kaji tausai na Naufal,ka samu ka girma haka kaima dan Allah"..

Cewa yayi "in Shaa Allahu zan yi yadda kika ce,Amman wallahi bani nake ruqe da tsananin soyayyar Abida ba, soyayyar da kanta ce ke ruqe dani,amman zan yi iya bakin kokarina naga ban sake Baki kunya ba,Amman Ina tausayin Aisha dan zuciya ta ta ruga da ta lalace ta kulle duk wata kofar shiga da fita a cikin ta..

Ina tsoron bazan iya son matata ba Hajiya umma,Ina tsoron kar ta chutu auren tsoho iri na Kuma Wanda ba lallai ya Bata dukkanin farin cikin da ya wajabta a kaina ba.."

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now