(25)

47 5 0
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(25)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Waya ce Alhaji badamasi yake tayi cike da tashin hankali,ta yadda aka hado wata kitumurmura wadda ta shafi Wani Alhaji wada jibril.

Shi kuma Alhaji badamasi ne God father din shi,se ya zamana cewa maganar da ta fito ce aka rasa yadda za'ai a warware ta..

Ya dade yana ta waye waye sun rasa yadda zasuyi,gashi shi Alhaji badamasi dama yana da dabi'ar Saka waya a speaker phone,so Abul na Jin duk abunda suke cewa ..

A zuciyar shi yake raya yadda idan shi ne cikin sauki ze iya warware matsalar.be dai ce komai ba se ya cigaba da tukain shi cike da natsuwar sa ta kullum.

Abun ya damu Alhaji badamasi da ake yi masa lakabi da Baaba Shima.

Se kawai yake ta miyar abun a mota,Kai se kawai ya fara nawa Abul labarin abunda mutane suke Wanda basa kyautawa..

Shima fa Wanda ya fiddo maganar Wada jibril din da a cikin su yake,shine yayi musu zagon kasa ya yada abunda ze iya kawo wa wadan tangarda a harkar takarar sa ta gwamna da yake nema a jahar sokoto.

Abul dai yana ji yana Kuma nade komai da kunnen shi ke ji yana dauka yana kaiwa kwakwalwar sa tsaf ,a lokaci guda yana shirya yadda yake ganin matsalar zata Kau.

A lokacin sun kusan Isa apartment din,se Abul yake cewa "Baaba,ni idan nine,zanbi hanya kaza da kaza ......,............,.......... Se naga kamar za'a samu maslaha.

Tunda kace shi Alhaji Bako da tare yake daku ko?"

Girgiza Kai Baaba yake yi yana fadin .."haka ne,Amman Bako bayada kirki ,Wani irin mutum ne,Amman bari muga yadda za'ai zanyi magana da wadan se Muji.."

(Kar ku ga kamar Ina magana a dunkule,kawai Ina so na nuna muku Irin hikimar da Allah ya kunsan wa Abul ta warware duk wata matsala da ze gani cikin sauki Kuma ta warwaru.wannan ita ce baiwar Abul.

Shi Kuma wannan labarin siyasa ne ,Ina ganin kamar ze bata mun lokaci ne shiyasa ,Kuma ba wai ya shafe mu da labarin bane.kawai akan Abul ne se ku gane ba wai abunda ya hado su zan tsaya gaya muku ba.ina fatan Kun gane main point din? Toh Baiwar Abul ce)

Ko da Baaba yabi shawarar da Abul ya bayar se gashi anyi resolving matsalar da zata bawa Wada matsala a takarar sa .

Abun ya masa dadi sosai,sosai.

Daddy be boye Mai ba yace Mai yaro ne karami ya fadi yadda za'ai ,Kuma Akai aka wuce gun.

Alhaji wada dai yayi ta murna yana wa Alhaji badamasi godiya .

Sannan yace ze bawa Abul 100k saboda tsabar murnar da yake ciki..

Abul ya sauke shi dama ,so shi be ma San ya ake ciki ba.

✨💕✨💕

A gida kuwa an kachame ana ta ciye ciyen kayan dadi,ana ta murnar dawowar Sufyan..

Anan yake Kara Sanar dasu cewa ya zama consultant.haba nan Wani sabon murna ya sake ballewa Wani shagalin ya balle,ake ta yi ana sake wa.

Da yake be fadawa kowa ba,hatta Maman sa ma bata sani ba, Dan haka da taji ya zama consultant din se Wani murmushin take me kayatar wa.

Tana zaune akan sofa,kallo Daya zaka mata ,ka gane cewa irin hamshakan matan nan ne ,taci ado na ban mamaki Wanda ya zame mata kamar wata al'ada, toh kullum a haka ake ganin ta..

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now