SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(56)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

💕✨💕✨

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Amsa wayar tayi cikin sauri tana ambaton Sallamar ta ta ka'ida "An kusa fa"

Yace mata bayan ya amsa Sallamar tata

Murmushi tayi tana cewa "An kusa Yaya,me aka kusa?"

"Komai ma " ya fada yana murmushi..

A  zahirin gaskiya shi maganar tabbatar shi a Sarkin Babban gari kachokam yake yi..

Ita kuwa da yake tana ta wasi wasin daurin auren ta,se ya zamana yana magana se ta dora maganar sa a kan wanchan tunanin nata ta bawa kanta amsar cewa goben ne dai daurin auren ta ..

Murmushi tayi tana cewa "in ta yi wari maji"

Dariya yayi Yana cewa "aww har su Karin magana aka iya,toh ba laifi"

Se tace "Yaya Abulkhairi ne ya kira ni muke magana,nayi holding din shi "

Cewa yayi "kice masoyin ki ne ,hada mu mu gaisa toh"

Dariya tayi tana hada wayar..

Abul da be San ta hada conference call ba,se yace "uhm wato dan kina waya da Oga shine kika shanya ni ko,ho yarinyar nan kin baci da rashin kunya,Amman ma ba komi,wallahi Nima na kusa aure in Sha Allah "

Dariya tayi tana cewa"Ai de yana jinka wallahi"

"Subhanallah" Abul yace

Sufyanu ne yayi dariya Yana cewa "ya muku kyau,Dan na gane dukkan ku gulmata kuke haduwa Kuna yi"

Dariya sukai sannan Abul ya gaishe sa yana  tambayar shirye shiryen ( na nadin sarautar sa),dan shi Abul ya sani,Sannan Kuma Mama ma Sufyanu ya gaya mata..

Still dai queen ce kawai bata sani ba ..

Se Sufyan yace "Alhamdulillah,ana ta fama Kaine dai baka nan"

Ta background din Nabila ke cewa "Adda queen,mama na kiran ki,tace kizo ki qarasa hadawa Yaya abinci"

Cewa tayi"tohm gani nan"

Se tace wa Sufyan"Yaya Dr zanje mama ta kira ni"

Cewa yayi "okay,Amman kar a hada mun abinci,zan zo na dauke ki muje mu siyo Wani abu,yau kwadayi nake ji"

Cewa tayi" tohm bari naje Kiran maman Ina zuwa "

Ajje wayar tayi ta tafi Kiran maman...

Maman ce tace "yanzu Zahra memakon kizo ki hada abincin Dr,shine ki ka zauna kina ta dumi a daki ko?"

"Ah ah mama ,Yaya Abul ne ya kirani muke magana da shi,yace base anyi abinci ba"

Queen na fadar haka maman tasan nufin shi,se tace "wai ni shi Dr baya gajiya da ciye ciye,wallahi Zahra in kika biye wannan ciye ciyen kiba Zaki yi,sannan Kuma duk namiji me jiki baya son mace me kiba ,kina yin kiba wata zeje ya auro "

Nan da nan queen ta ji ranta ya baci sosai,Kuma fa da gaske ya shaida mata baya son yaga mace da jiki ..

Cewa tayi "tohm mama"

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now