(32)

46 8 0
                                    

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(32)

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

💕✨💕✨💕✨💕

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Kasar Bahrain me dumbin tarihi da dokoki,ita muka shigo dan duba Yan makaranta .. wato Sudee da Mimi..

A dakin su Wanda yake dauke da dalibai mata su 6 na gan su,su mimi har sunyi Kawa wata yar turkey sunan ta Atishe (khadijat) sun kulla alaka me karfi a cikin satin su na uku a kasar Bahrain din..

Sun fara yin karatun su cikin nasara da sa'a yayin da suke amfani da shawarwarin da iyayen su suka basu Dan samun zama lafiya da yin rayuwa ne inganci a inda ba kwaba balle gyara..

Se dai cikas daya da Saudatu take da shi a rayuwar ta na rashin sanin inda ahalin ta suke..

Se Mimi da soyayyar Wani saurayi dan kasar indiya ya kamata tun ba'ai nisa ba duk tabi ta sukurkuce ta rasa yadda zatayi da ranta da rayuwar ta ..

Gashi shi be ma san tana yi ba fa,toh amman da yake wannan ba Wani sabon abu bane ba mu a gun mu da Kuma Yan matan zamanin nan ,se muke ganin abun kamar normal ne ai,tunda is very very common,ana yi sosai ma,son maso Wani ba, kenan koshin wahala..

Haka suke zama su Sha kukan su ita da sudee kowa na damuwar shi har a rasa me rarrashin Wani ma a cikin su..

A nan se dai muce Mimi Allah ya tsamo mana ke daga kogin soyayyar da kika rufta, shine Addu'ar da zamu iya yi Miki..

Bayan haka kuwa suna rayuwa ne cike da farin ciki da nishadi.

gashi kusan kullum suke face time dasu Baba domin dama ya Siya musu sabbin iphone 12 pro max tun fitowar ta ya Siya musu gal gal a box din su,se ya ajje be basu ba a lokacin tunda thirteen bata fito ba sannan Shima 12 din ce a hannun sa Kuma ba yanda za'ai su ruke waya iri daya..

Dole ya ajje se da 13 ta fito shi Kuma ya siyo 13 din sannan  ya basu nasu.

Da zasu tafi makaranta ya danka musu ko domin su kwantar da hankalin su, su iya tafiya makaranta da murna tunda ma ba me musu rakiya saboda issue din visa din nan..

Ba Wani dogon bayani zan tsaya yi ba akab su mimi..

zamu dai sake waiwayo su bayan Wani lokaci insha Allah.

Fatan mu dai suyi karatu yadda ya kamata zuwa gaba muga me gaban zata haifar ..

✨💕

A gidan Alhaji Hashim kuwa ..ga abunda yake faruwa

Hm hm hm wasa kake dani Alhaji, billahillazi  idan kaga na sake ka ka fita,toh wallahi ka biyani bashi na da ka karba,sanda kazo kana neman ai ban maka musu ba na dauka na baka,se yanzu da nace ka bani ne zaka fara wasu kananun bayanan ka wofi,nifa yanzu ba Wani Wala Waka da zaka mun,malam ka irgo kudi na kawai ka bani bana son wasa,naga ai ba naka nace Ina so ba ballantama muzo ana yar wallahi tallahi,naga dai nawa ne,hakki na ne nace ina so ba wani Abu ba .

A zaton ka idan da bana sana'ar da nake yi yanzu kake neman durkusar dani zan Kai haka a nan gidan ne,me ma ake da zaman gidan ka,gidan yunwa da Babu?

Da jiki na ka Aure ni fa, amman dubi yadda na koma kamar irin tunkiyar nan da ta gama haihuwa saboda tsabar azabar ka da masifa.

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now