(63) Za end

183 6 0
                                        

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(63) End

Wattpad @divaadoveysdiaries03
Okadabooks
@divaadoveysdiaries03

08165992806 . WhatsApp only, ladies only (mata zallah)
______________

💕✨💕✨

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Wani irin hawayen dadi ya zubo wa Soffy me hade da kukan farin ciki...

Tayi zaton zata gan shi da mata da Yaya ko biyu ko uku haka,amman Allah ya amsa mata,ta ganshi be yi aure ban ba ma..

Wannan farin cikin har Ina?

Hawaye take sake Yi kafin tace "when is it taking place?"

Dariya yayi me cike da nishadi sannan yace "Saurin me kike yi ne? Se mu fara sanin juna mu fahimci juna,muso junan mu sannan ai ko?"

Katse shi tayi da fadin "Fahimtar juna?,fahimtar juna fa kace khairu,ba wannan zancen, maganar mu so junan mu ma,ni tunda na sanka ban taba dai na sonka ba,for over how many years,ko son da eNike Maka kadai ya ishe mu rayuwa har jikokin mu"

Zaro Ido yayi Yana dariya Yana mamakin halin saffiyyan..

"Oya laugh" tace,baka san me nake ciki bane ba,at this age banyi Aure ba Ina jiran ka,se da na ganka sannan se a fara wani fahimtar juna? Ni na fahimce ka tuntuni,Shima ya ishe mu rayuwa"

Murmushi yayi yana kallon wayar da ta shigo masa domin ba shida abun cewa ma ..

"Baban su Sufyanu ne ya kira sa"

Da sallama ya daga Yana cewa "Baba barka da yanma"

Se ya amsa wasu maganganu suka kashe wayar su.

Ya masa magana ne akan zuwan su gun president Bala..

Shine yace wa "Safiyya,rigima da kanta ,ni zan wuce an kira ni zanje nayi sharar ofishin mu"

Murmushi tayi sannan tace "ka gaya musu in ka aure ni ka bar musu sharar,se a nemo wani ba Kai ba"

Smiling yayi sannan ya juya ze tafi,se tace "Khairu,in ka tafi ya zanyi na sake ganin ka?"

Juyo wa yayi a hankali ya Ciro wata yar baby waya ya Mika mata yace "sorry please"

Saka masa tayi sannan ta kira kan ta ta tabbatar ya shiga sannan fa ta kyale shi ya tafi dan ta lura daga wayar da ya daga hankalin shi duk ya tafi chan sauri yake yi..

Se da ya fita daga gun sannan ita kuma ta biya kudin abincin da yaci sannan ta fito ta koma office Mai makon ta tafi gidan da tayi niyya....

Ta kasa rufe bakin ta,bakin yayi kamar gonar auduga,ta kasa ma yin komai a office din, sannan a lokacin ma cike take da mararin son sake Jin saukar amon muryar sa a cikin kunnuwan ta..

Maganganun shi suna zuwa mata ne a matsayin busar sarewa a kunnuwan ta..

Daga wayar ta tayi kamar ta kira shi,se ta fasa ...

Shi Kuma a hanya motar da yake ciki ita take nuna masa inda zashi bayan ya daddana inda ze je a map din motar ,don be San Abuja ba kunga ..

Sannu a hankali yake tafiya se gashi a gate din da yake son tsayawa..

Alhaji Baba na gaban shi ,ba dade wa aka bude kofa suka shige ciki har inda zasu ga president...

Abun nata bawa Abul mamaki,Yana ta kallon yadda aka ci uban kudi a wannan gida wai shi Villa kamar baza'a mutu ba ..

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 19, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SAUYIN RAYUWA ✅Stories to obsess over. Discover now